*MATAR UBA...!!!*
*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION* 🦅🪶
*Na Nanah khadii* 💅🏽🛍️
Sadaukarwa ga Leemart Pinky 💕
Gaisuwan bangirma zuwa ga, H-Umar admin Beneficial writer's, da MK ina muku jinjina godiya ta mussaman.
Littafina true story ne, so pls duk yadda ka ganshi ka karanta, bansan k'orafi abeg😍.
*Page 1&2*
Bauchi garine mai tarin tarihi da albarka, b'angaren sarauta kasuwanci, da tarihin gargajiya, yanayin garin zafine kuma tanada girma, amma ba sosai ba.
Annoor specialist Hospital, asibitine ne na masu hanu da shuni duk wata Mace da zaka gani cikin asibitin, Mace wacce taci ta tada wuya wurin iya tsaruwa asibitin ya tsaru sosai, " *LABOR ROOM* " Abinda ke rubuce a saman k'ofan knan, cikin sauri ya fito da kallo d'aya zaka masa kasan baya cikin hayyacinsa, farin glasses d'in dake manne a idonsa, ya gyara wanda ya sake k'ayata kyansa yana fad'in, "gsky she is in pain in dai har tak'ara 10mins bata haihu ba, bamuda wani alternative dole ayi mata C.S, ya fad'a in a serious tone yana k'ara sauri, nurse d'in dake biye da cikin shiganta na kayan nurse, da ya karb'e ta sosai tace, "kaman ta jima tana labor a gidane, shiyasa duk k'arfinta ya k'are, shiru yayi yana jinta ba tare da yasake bata ansa ba, office d'insa ya bud'e ya su ka shiga, table d'insa ya nufa ya d'auki wayansa k'irar iphone 13, kallonta yayi ya sake gyara tsayuwarsa kafin yace, "kije kufara arranging komai zan kira mijinta, zaizo yasa hannu sai musata ayi mata C. S d'in kawai, dan already tariga tasha wahala, "ok sir" tana fad'in haka ta fice da sauri.
Kunna wayan yayi tare da shiga, ma'adannan numbobi ya fara neman sunan sa, cikin sa'a ko yaci karo da sunan shi kamar yadda yayi saving Umar Ahmad Adam, danna kira yayi cikin sa'a bugu biyu ya d'auka.
Zaune yake cikin office ɗin shi shadda ce light blue a jikin sa,idonsa a lunshe suke yayinda sanyi A/C dake manne a bango, ya gaure shi ga k'amshi turensa designer ya had'u da sanyin gun, juyi kawai yakeyi a kan kujeran saide kallo d'aya zaka masa kasan tunani yakeyi, ringing d'in wayansa ne yadawo dashi daga duniyar da yafad'a, ganin sunan Abokinsa dake rubuce a kan screen ɗin wayan Dr. Abdool Maleek ne ya shi sakin murmushinsa mai kyau tare da ɗaga wayan, ko da ya picking sanda wasu ɗakiƙai suka shud'e kafin yace, "Hello likita bokan turai hala mafarkina kayi yau ka kirani yayi mgnar cikin zolaya, jin yadda yayi mgna ba tare da wata damuwa abun ya bashi mamaki katse shi ta hanyan faɗin "kasan ba neman juna muke ba sai wani abu ya taso, hka zumunci zamanin ya zama sai a hankali, anyway ba wannan ba Madam fa abu yak'i, dole sai an mata C.S kuma bana so ta sake 10mins ba'asan matakin d'auka ba, koda yake mgnar sam Umar bai gane inda ya dosa ba sanda gama mgnsa, kafin yayi dariya cikin zolaya yace, "Mallam ko dai patients sun maka yawane?, ka duba numbern wanda ka kira kuwa, ni Matata tana gida bata da ciki balle ayi mgnar haihuwa, d'an tsaki Dr yayi kafin yace, "joke aside wlh bazata iya haihuwa da kanta ba, in the first place wai meyasa ma baka d'akko wani daga y'an uwan ta sun zauna da ita ba kuma kaima baka nan akanta why?, kaga time is going u have to come and sign, "like serious wlh matata bata da ciki, ka sake duba number d'in wanda ka kira, jin mgnar sa sosai ya sa shi cikin rud'ani da jin haushi da kyar ya sake fad'in, "Umar matarka Zainab ita nake nufi jin abinda yace sosai yayi mmki, "anya kuwa ba dai mata ta ba abinda yace sosai ran Dr ya ɓaaci cikin ɗacin zuciya yace, "kagani duk abinda ya samu matarka kaine ka jawo, ganin fa da gske Dr yake ya sashi fad'in, "am on my way bari nazo naga ikon Allah, bai jira ansansa ba ya kashe waya tare da d'aukan car key d'insa, ya fita a office d'in cike da zullumi aransa kallo d'aya zaka masa kasan yana cikin rud'ani, koda ya shiga mota sake mai maita mganar Dr yayi a ransa, "matar ka Zainab, wani rough driving yake yi kamar zai tashi sama.
YOU ARE READING
MATAR UBA...!!!
RomanceHmm babu abinda zance kudai daga sunan kusan akwai abubuwan almara iri iri kawai kubi alƙalamina zan warware muku komai karku manta labarina ba ƙagagge bane lbrin gaskiya ne😍😔