MATAR UBA...!!!

11 2 0
                                    

*MATAR UBA...!!!*

*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION* 🦅🪶

*Na Nanah khadii* 💅🏽🛍️

Ƙorafi ya karɓu naƙara wannan page ɗin last free knan😁kiyi ƙoƙari kiyi payments 🤍💕

  *page 11&12*

Bauchi Unguwar Jaki....

Duk da baya ganinta bai hanata zare ido ba jin ya nakira sunan Mamah, ƙoƙarin zare jikinta takeyi tanaso ta miƙe saide sam yaƙi saketa, fashe mishi tayi da kuka da muryarta da baya fita tace,  "dan Allah ka sakeni na tashi kar tazo ta ganmu a hka nikam, cikin kasalalliyar muryansa da daƙyar ya iya controlling kansa bai shigeta ba yace, "shikenan zan sakeki tunda ba kyaso naji ɗumin jikinki yana faɗan hka ya saketa da sauri ta miƙe ta bar katifan ta koma gefe ta zauna, ya kusa 10mins kafin yayi ƙarfin halin miƙewa ya kunna torchlight ɗin wayansa ajiyewa yayi a gefe yana kallonta, ganin irin kallon da yake mata ne yasata sunkuyar da kanta ajiyan zuciya yayi kafin ya miƙe a hankali ya taka inda take takure, hannu yasa ya miƙar da ita saide sam taƙi yarda su haɗa ido cikin wahalarlilyar muryasa yace, na dameki ko? Kanta a ƙasa ta kaɗa masa alaman a'a yajima yana kallonta tare da jin sonta na ratsa duk wani ilahirin jikinsa, gunda kayanta yake ya nufa yafara tattarawa a hankali ta tako tazo tasa hannu suka tattara cikin bakonta ya zuge zip, taso ta canza kaya amma tasan zai irina cewa ta canza a gabansa yasa ta hkra sabon Hijab ɗinta har ƙasa ta ɗauka tasa, duk tarasa meyasa jikinta yayi mata sanyi ɗaukar bakon yayi yasa a bakin ƙofa kafin yace tazo suje, jin abinda yace sanda hanjin cikinta suka kaɗa jikinta a sanyaye tazo tabi gefensa zata wuce, janyo ta yayi tare da matseta a jikinsa ƙoƙarin kwace kanta take saide sam ta kasa sun kai minti 5 a hka kafin ya saketa tare da riƙe hannunta suka nufi ɗakin Mamanta, a ƙofar ta ɗan ja ta tsaya tana tunanin mai zai faru juyowa yayi ya sake jan hannunta zuwa dap da ƙofar ya saketa suka shiga da sallama a bakinsu.  Cikin sa'a suna shiga ana kawo wuta, zaune take gefenta Khaleesat ɗan gefen Aminah sai Sadeeq da Ishaq dasuke gefe suna wasa, ɗago kan da zatayi ta gansu tare sanda ta haɗiye wani abu mai ɗaci daya tsaya mata a wuya, wani kallon banza ta musu ta ɗibesu ta watsar tare da sunkuyar da kanta ɗan gefenta ya zauna, kafin yayi mata nuni da ido alaman ta zauna, gefensa can ta zauna tare da takura dan harga Allah duk hankalinta baya jikinta jiran me zai faru kawai takeyi, gyaran murya yayi kafin yace ma yaran su shiga uwar ɗaki zaiyi mgna da Mamansu, sai lokacin ta ɗago tare da watso masa harara, "wani darene jemage bai gani ba duk abunda yake faruwa ba a idonsu akeyi ba? Ko sai yanzu kasan da yara agidan dan Allah ku ficemin a ɗaki ta faɗa ranta a mugun ɓace, bai ce mata komai ba harta kai aya kafin yace, "ya kalli Aminah yace kama hannun ƙannanki ku shiga ciki, turo baki tayi tare da kama hannun Khaleesat kamar zata karya tace su zo su shiga ɗaki, bbu musu suka miƙe tare da bin bayanta, ganin yaranta sun bargun itama ta miƙe zata bi bayansu, "Sa'adatu mgna zamuyi ki dawo ki zauna,  "mtsss me zaka cemin nifa kaga banda lokacinka kaje ka ɗakko wannan zuriar mayun ka shigo min da ita ɗaki taya kake so na saurareka? Tunda take mgna ta sake sunkuyar da kai ji take kamar ta fice a ɗakin jin abinda yace ne ya katse mata tunanin ta gaba ɗaya,  "tunda ba kyaso ayi mgna ta nutsuwa da fahimtar juna komai naki cikin fitina yake nazo na sanar dake yau an ɗaura Aure na da Zakkiya, jin abinda yace sanda cikinta ya kaɗa cak ta tsaya tanajin wani jiri na ɗibarta juyowa tayi a zafafe tana kallonsa lafin tace,  "anya Auwalu baka fara shaye shaye ba kasan kuwa me kake cewa Aure fa kace a ina aka taɓa ɗaura Aure da daddare? Ko duk cikin matsuwan kaga ka kwanta da ita? Auwalu kana da hankali kuwa? Jin abinda tace sosai ransa ya ɓaci kallonta yayi kafin yace, "niko nake cikin hankalina Aure kam an ɗaura kuma yanzu zan kaita gidan mai unguwa kafin na gyara inda na kama mata haya zuwa wani sati ta tare, tunda suke mgna zuciyarta ta sake tsannanta bugawa hawayen idonta ta share jikinta sai rawa takeyi "da kuka ta fashe tana faɗin, "lalle namiji butulune namiji hankaka gabanka fari cikinka baƙi, wato saida ka Auri wannan yar matsiyatan hmm! Naji babu komai amma wlh bbu hayan da zaka kaita, a haɗe mata wancan ɗakuna biyun sai yaran su koma wancan ƙaramin store ɗin, Auwalu bazaka raba mana gurin zama ba wlh banyarda ba,  "ai bayardar ki nake nema ba ra'ayina zanyi ba naki ba, "lalle kace ka shirya cin amanata tun yanzu wlh muddin kace zaka raba mana gida zakaga abinda zai faru tana faɗin haka ta shige ɗaki tana kuka, miƙewa yayi yafice yayinda itama jiki a sanyaye tabi bayansa ɗakinta ya shige itakuma ta tsaya a ƙofa taƙi shiga, ganin bayida niyan fitowa ga dare ya farayi ne yasata ɗaga labulen jiki a sanyaye tana rarraba ido gefen katifanta ta hango shi tsaye ya zubo mata ido, saurin ɗauke kanta tayi cikin tashin hankalin me yakai shi ɗakinta ta ɗaga ƙafarta da ƙyar tasa a ɗakin tare da cire slippers ɗinta da ya ɗan ji jiki a sanyaye ta shiga saide kanta a ƙasa taƙi ɗagawa su haɗa ido sam, ta ƙarasa gunda yake tsaye duk da a jikinta tanajin alaman ya kafeta da ido ko da tashigo sam taƙi zuwa kusa dashi ɗannesa ta tsaya kafin da kyar ta iya cewa,  "dan Allah kazo mu tafi dare yayi ta ƙare mgnar cikin kuka, hannunsa yasa ya janyota ta faɗa jikinsa ƙoƙarin tashi take amma yaƙi bata dama, kawai saita kwanta lub tana jiyo bugun zuciyarsa yayinda shikuma yake jin wani abu na taso masa, sun jima a hka kafin ta ɗago ido wutan lantarkin daya haska gun ne ya bata daman kallon idonsa da suke lunshe, yana da haske da hanci saide idonsa ne ƙanana har akance masa ɗan China kuma baida tsayi can, kallonsa takeyi wanda ita kanta bata san dalili ba buɗe idon da yayi sukayi ido huɗune yasata jin kunya tare da saurin rufe nata murmushi yayi kafin yace,  "meye kika rufe idon bayan nasan tun ɗazu ni kike kallo, duk tana jinsa saide sam taƙi buɗe idon jin bakinsa kan nata datayi ne ya tsorata zaro ido tayi tana kallonsa, saide shikuma ya lunshe nasa lokacin ƙwace bakinta tayi cikin sa'a ta turo su kafin tace,  "dan Allah mutafi wlh darw yayi, still idonsa na lunshe ya bata ansa. "nifa gsky a duk sanda na kasance tare dake rasa nutsuwata nakeyi da zakimin alfarma da kin..." a'a dan Allah kayi hkri ni kakaini gidan mai unguwar, kuma tunda Anty tace mu zauna anan ka gyara mun sai mu zauna, jin abinda tace sanda ya buɗe idonsa da suka sauya kala cikin wata dashasshiyar murya yace, "kinsan me kike cewa kuwa kina ganin hka kinma kanki dani adalci? Da sauri ta ɗaga kai alaman "eh ",  wani ajiyan zuciya ya sauke yana kallonta yayinda itama shi take kallo yace,  "shikenan tunda hka kika zaɓa Allah ya haɗa kanku yasa hakan yazama alkhairi da sanadin shirinku, "Ameen tace tare da saurin fita a jikinsa ta fice a ɗakin, ajiyan zuciya yayi tare da bin bayanta koda ya fito bai ko kalleta ba ta ɗauki bakon kayanta suka fice a gidan.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 08, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MATAR UBA...!!! Where stories live. Discover now