*MATAR UBA...!!!*
*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION* 🦅🪶
*Na Nanah khadii* 💅🏽🛍️
*Sadaukarwa ga Leemart Pinky 💕*
*9&10*
Waleed ne ya shigo ya haye kanta da murnansa abinda ya farkar da ita kenan rungume shi tayi tare da masa peck a kumatu, "Mommy kintafi kin barni inata missing ɗinki kuma Daddy yace zai kawo ni bai kawo muba murmushi tayi masa ya ƙare mgnar yana turo baki, "gashi na dawo yanzu maza kaje ka cire uniform kagani Baby na bacci karka tashe shi, sake ta yayi da sauri ya ƙarasa inda Babyn yake baccinsa kallonsa yayi for like 2mins sai kuma ya ɗago ya kalli mahaifiyarsa, "Mommy inaso na ɗauke sa, "laa baka ga yana bacci ba kabari sai ya tashi ko? Da murnansa ya ansata da, "toh ya sauka agadon da sauri ya fice yana ƙwalama Ahmad daya shigo da sauri ya nufi ɗakinsa ya shiga toilet direct, "kai ina toilet menene? Da cikin farin ciki yace, "guess what? "kai kullun guess ɗinka akan chocolates ne Daddy ya kawo mana ko? "a'a Mummy ta dawo with a new baby, zare ido yayi kamar yana ganinsa kafin yace, "are you sure?, "eh mana kafito muje kagani, da sauri ya wanke jikinshi ya fito ko sauraron Waleed ɗin baiyi ba ya wuce zuwa ɗakin Mommynsu, tura ƙofar yayi yana faɗin, "Mommy wai da gske kin kawo mana Baby? Ya faɗa yana kallon gadon, murmushi tayi kafin tace, "eh amma yana bacci ba kayi missing ɗina ba ko? Sai lokacin ya kalleta yayi dariya, " nayi Daddy ne yace zai kawo mu bai kawo muba, "hug Mommy da sauri ya ƙarasa yayi hugging ɗinta wani sanyi taji aranta sake shi tayi bayan ta tuna halin da take ciki, " kuje ku shirya kusa uniform ɗin madarasa Daddynku zaiyi faɗa, "but Mommy i want to carry the Baby, "Ahmad he is sleeping kasan tym ɗin islamiyan ku is going ko? Wayanta ne ya fara ringing sai time ɗin ta tuna dashi, miƙewa tayi ta ɗakko handa bag ɗinta ta ciro ganin sunan, "Love of my life" tayi akan screen ɗin sanda tayi ajiyan zuciya kafin ta ɗauka da sallama a bakinta, ganin tafara wayane yashi fita a ɗakin, da faɗa Mamah ta rufeta, "wato ke sai ki iya kwana biyu bakiji muryana ba kuma bazaki damu ki kiraba? "kiyi hkri Mamah dama inaso nakiraki yaune kiriƙe kiranki bana so, "a'a Mamah kiyi hakuri, "toh nayi ykke ina masu gidan nawa? fatan duk kuna lfy? "shiru tayi kafin tace, "eh Mamah duk lfynmu ƙalau suma yanzu suka fita zasuje islamiya, "Zainab Mamah ta kira sunanta, ansawa tayi sai kuma tayi shiru, "yau naji muryarki ba kaman na kullun ba lfy kuwa? Ɗan tsorata tayi sai kuma ta dake, "eh Mamah bacci nake su Ahmad suka tasheni, "to Allah yayi muku albarka kina dai kiran yayunki kuna gaisawa ko?, "ameen Mamahna eh muna waya dasu duka, hira suka ɗan taɓa kafin sukayi sallamah, koda ta kashe wayan tajima agun tana kuka jin motsin Babyn ne yasata miƙewa tare da ajiye wayan, ɗakko sa tayi tana kallonsa sai tym ɗin ta tuna da ko huɗuba ba'a yi masa ba, share hawayenta tayi ta masa huɗuba da suna "MUHAMMAD", ta jima tana rungume dashi kafin ta ajiye shi ganin ya koma baccin, jin cikinta na kukan yunwa ne yasa ta miƙe ta zura hijab ta sauka, babu kowa sai ƙaran A/C kitchen ta nufa ta buɗe flask ɗin da suke zuba abinci, jollof rice ne aciki dayaji kifi da su carrot rufewa tayi ta ɗakko plate kaɗan ta ɗiba ta haɗa tea ta koma sama, tun daga stairs take juyo kukansa da sauri ta ƙarasa ta tura ƙofan ta shiga a gefe ta ajiye abincin tasa hannu ta ɗauke shi, jijjigashi ta shigayi amma sam yaƙi yin shiru kawai sai tasa kuka, "anya Yaa Umar akwai zuciya a jikinshi? Ya yakeso nayi wannan yaro idan yana kuka, dagani harshi Allah bazai barmu ba nikam nashiga uku, ganin kukan nashi yayi gaba kuma ta tuna da condition ɗinshi na ɗazu a zabure ta miƙe ta nufi ɗakinsa, tama manta da wani abu waishi Knocking handle ɗin ta murɗa ta shige ɗakin, tsaye yake gaban dressing mirror daga shi sai towel iya west ɗinsa haɗa ido sukayi tayi saurin ɗauke nata jin wani abu ya ziyarci zuciyanta kusa dashi ƙadan ta ƙaraso cikin kuka tace, "dan Allah Yaa Umar kayi hkri dan Allah dan Annabi Muhammadu S.A.W kabarni nabama yaronnan abincinsa na roƙe ka kar wani abu ya sameshi, murmushi yayi mai ɗauke da tarin ma'ana kafin yace, "karki damu zaki shayar da yaronki amma! Da condtions, jin abinda yace sanda zuciyarta ta buga dan tasan condtions ɗin nasa saide Allah ya cireta cikin kuka tana rarrashin yaronta tace, "kamun rai Yaa Umar dan Allah kaga jego nake karka cutar dani, kafaɗa ya ɗaga mata alaman ko oho yace, "ko zaki koma gidan ubansa kiyi jegonsa ne? Da sauri ta girgiza masa kai alama a'a, "then dole kibi dokan da zan sa zaki iya tafiya idan nagama zaki ji su, da sauri ta miƙe ta fice a ɗakin tana koma ta gyarashi duk da kukan da takeyi tasa mishi nono a baki, saide da kyar ya kama zuƙa ɗaya biyu yayi amma duk ya dawo dashi, "innalillahi wa'innah ilaihin raji'un nikam nashiga uku wannan wani irin jarrabawa ce? Ajiyeshi tayi ta miƙe da sauri ta shiga toilet kayan jikinta ta fara cirewa ta ɗaura towel, ruwan wanka ta haɗa ta fito da sauri ta ajiye sanda ta haɗa duk abinda zata buƙata kafin ta ɗago shi duk kukan da yakeyi tasa shi ta fara mishi wanka, cikin green overall ta shirya shi jin ruwan zafi yasa shi yin shiru, feeding ɗinsa tayi yayi bacci tasa shi a kaɗanta yayi gyatsa kafin ta kwantar da shi(dan indai daga shan nono ka kwatar da yaro yakan dawo musu), tsab ta tattara gun kafin ta ɗan samu nutsuwa duk da ciwon kan da take ji ta zauna cin abinci, kuma babu laifi dan taci more than half.
![](https://img.wattpad.com/cover/344472689-288-k52776.jpg)
YOU ARE READING
MATAR UBA...!!!
RomanceHmm babu abinda zance kudai daga sunan kusan akwai abubuwan almara iri iri kawai kubi alƙalamina zan warware muku komai karku manta labarina ba ƙagagge bane lbrin gaskiya ne😍😔