*MATAR UBA...!!!*
*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION 🪶* 🦅
*Na Nanah khadii💅🏽* 🛍️
*Sadaukarwa ga Leemart Pinky 💕*
*5&6*
Ƙarasowa yayi ransa a mugun ɓace yana faɗin, "Sa'adatu!wlh da murfinnan ya sameni ranki sai yayi mugun ɓaci,kina gani ina barinki albarkacin ƴaƴanki kikeci da igiya ɗayan da yarage miki, aurene wlh babu fashi wani lallamine ban miki ba kin rufe idonki kin kasa gane ƙaddarane ta gifta, tunda suke faɗan kuka takeyi sam bataso taga suna samin saɓani akanta, "koba ƙaddaraba wannan son zuciyane babu wata ƙaddara duk matan da suke yawo a titi baka gansu ba,sai yarinyar da muka raina kuma bakaji kunyar kallona Ka faɗa min kabada sadakin taba, jin yadda suke musayan yawu a gigice tafice a gidàn da gudu ba tare da ta san inda zata ba, bin bayanta yayi yana kiran sunnanta saide sam tak'i waiwayo wa da ƙarfi yake faɗin, "kalli gabanki machine saide ina kafin ya rufe baki har ya kaita ƙasa,da gudu ya ƙarasa yana kiran sunnanta, kafin kace wani abu duk an zagayeta ciki harda mai machine ɗin.
Duk ta kukkuje kwance take bata ko motsi, "innalillahi wa'innah ilaihin raji'un Zakkiya!! Muje chemist Dan Allah yana faɗin hka yafara ƙoƙarin ɗagata da temakon mutanen gun suka kikkiɓeta duk da bata da jiki amma yadda yake jin kansa sam ya kasa ɗagata, bawani tafiya mai tsawo sukayi ba zuwa gun a take babu ɓata lokaci mai chemist ɗin ya fara aikinsa,ta kukkuje akanta da hannunta wanke ciwon yayi yasa mata magani,banda hawaye babu abinda yake zuba a idonta har aka gama kuka takeyi,mai machine ɗine ya biya kuɗin kuma ya rakasu har gida,zaune take tana cin cigam cakal cakal suka shigo da sallama wani kallo ta watso musu tare da sheƙewa da dariya , "shegiya dangin mayu dangin butulu aidama mutuwa kikayi dayafi miki, Dan wlh kin kunno wutan gasa kanki daga ke harshi sai kun ɗanɗana kuɗarku muje zuwa, kuda kwanciyan hankali a gidannan ya ƙare mai machine dai mamaki ya hanashi ƙarasawa ciki, Allah ya ƙara sauƙi yayi mata tare da sallama yafice dayin Allah wadaran da irin wannan mata,kome mutum yayi maka ai bazaka masa fatan mutuwa ba. Harɗaki ya kaita yasata a ƴar katifar dake wurge can gefe ledan ɗakin duk ya ciccinye sai ƙullin kayanta shima a gefe ɗaya, tunda suka shigo yake mata sannu a hankali da temakonsa ta kwanta saide still hawaye bai daina tsiyaya a idonta ba harya miƙe zaifita ta yunƙura duk da ciwon da kanta ke mata cikin tashin hankali da ya bayyana a face ɗinta ,dan duk mgna da sannun dayake mata sam taƙi kulasa, "Babah Dan Allah ka haƙura da aurennan nima na haƙura kabarni na auri Salihu kawai,banaso naga kuna faɗa da Mamah akaina kayi haƙuri ta ƙare maganar tana share hawayen daya ƙi tsayuwa a idonta, tunda take maganar kallonta kawai yakeyi ransa bai ɓaci ba sanda yaji takira sunnan Salihu cikin ƙunnan rai yace, "Zakkiya in tambaye ki? Kai kawai ta kaɗa masa alaman "eh", "kina sona? Ko kuma albarkacin rainonki danayine yasa kikamin alkunya kika karɓi soyayyata? Shiru tayi bata da niyan mgna dan tambayan dayayi mata jinshi tayi kamar ya watso mata garwashi a zuciyanta ne,sake nanata mata tambayayi still batace komai ba ganin haka yasa shi faɗin, "shikenan na haƙura karna takura miki ashe ba sona kike ba kinfi son Salihu insha Allah a darannan zanje na karɓa kuɗina agun mai anguwa kuma na sanar masa da ace Salihu ya aiko mgabatan sa, tunda yake mgna kallonsa take yi gaba ɗaya tunani ya kulle kanta yayi murfi bata san ya zatayi da wannan jarrabawar ba, bai jira ansanta ba ya miƙe riƙo hannunsa tayi ta kasa mgna kanta kawai take girgizawa tana kallonsa banda hawaye babu abinda ke zuba a idonta, shima ita yake kallo cike da tausayawa komawa yayi ya zauna still yana riƙe da hannunta,da ƙyar ta tsagaita kukan cikin muryarta da baya fita sosai, "a'a Babah ina....sai kuma ta sake fashewa da kuka har ransa yakejin kukanta, "ina sonka amma banaso naci gaba da rayuwa a haka kullun saina zubar da hawaye banida kowa bansan kowa ba haka na taso cikin ƙuncin rayuwa,banaso yaran da zan haifa suyi irin rayuwar danayi da naji daɗin rayuwa amma tunda wannan ƙaddarar ya gifta namanta meye farin ciki rayuwata ta sauya daga haske zuwa duhu bana jin daɗi idan naga kuna faɗa da Mamah akaina, shiru tayi tana rera kukanta da ƙyar ta tsagaita taci gaba da mgna, "shiyasa na haƙura nafiso naga tana farin ciki mukoma zaman mu kamar nada tana kaiwa nan wani kuka ya sake suɓuce mata, shikansa yasan tana cikin damuwa amma harga Allah tun ranar da ƙaddara ya faɗa mata zuciyarsa ta aminta da ita,baya jin zai iya sadaukar da son da yake mata gawani, ajiyan zuciya yayi mai nauyi kafin ,muryansa a raunane yayi ƙoƙarin kiran sunnanta idonta da sukayi jajawur kamar jini zai zubo ta ɗago ta kallesa,saurin kauda kansa yayi dan baya jin zai iya kallon yadda kyawawan idonta suka sauya daga farare tass zuwa launin ja, "Zakkiya nasan kina cikin damuwa kuma nasan kina sona ko nace muna son junnan mu,kina ganin dankin ce kin fasa aurena zaisa Maman taki soki?to kinyi kuskure ai aikin gama ya gama garama muyi aurenmu ,ki haifa min yara kamarki murene su kuma insha Allah ba zasuyi rayuwar ƙunci ba kema bazaki tabbata a hka ba,tashi ɗaya Allahn daya jarrabeki shi zai yaye miki, kina ganin a kishinku na Mata zata sake sonki? Kai ya kaɗama alaman a'a dan bazata soki ba, kiyi haƙuri da duk inda kika tsinci kanki kowa da tasa ke hka naki kaɗarrar tazo miki kuma bazaki iya guje mata ba, tunda yake mgnan shi take saurare still kukan takeyi,saide sosai mganarsa tayi tasiri a zuciyarta nan yarrarasheta da kalamai masu taushi ta kwantar da hankali ta haƙura kwantar da ita yayi ya fice a gidan, yana fita ta daddafe bango ta miƙe riƙe da kanta da yake sara mata kamar zai faɗo ƙasa hannunta ta ɗaga sama tana faɗin, "ya Allah kamin mafita a wannan rayuwa Allah kasa naci wannan jarrabawar banida kowa sai kai , wannan wani irin rayuwa ce kallon kanta tayi daga zanin da take ɗaure dashi zuwa rigarta, "Allah kasa watarana nima naga dangin iyayena ko zanyi murmushi a rayuwata mai ɗaurewa, tajima a agun tana kuka kafin ta koma ta kwanta nan bacci yayi awon gaba da ita.
YOU ARE READING
MATAR UBA...!!!
RomanceHmm babu abinda zance kudai daga sunan kusan akwai abubuwan almara iri iri kawai kubi alƙalamina zan warware muku komai karku manta labarina ba ƙagagge bane lbrin gaskiya ne😍😔