MATAR UBA...!!!

5 0 0
                                    

*MATAR UBA...!!!*

*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION* 🦅🪶

*Na Nanah khadii* 💅🏽🛍️

*Sadaukarwa ga Leemart Pinky 💕*

Not edited 🌚🌝

*7&8*

Jin abinda yace sanda ya tarwatsa duk wani tunanin ta jajayen idonta ta ɗago suka kalli juna, ganin kallon tsanan da yake matane yasata sauri saukar da nata cikin kuka ta miƙe jiki a sanyaye, tana rungeme da ɗanta ta tako har inda yake tsaye yana kallonta tsugunawa tayi tare da riƙe ƙafarsa hawayene suka zubo a idonta kafin tace, "Dan Allah Yaa Uwar kamin rai kayi hakuri kabarni na shayar da mala'ikan Allah, wlh shima baida laifi ƙaddarar sa ne shima yasa yazo a hkan na roƙe ka da kamin wannan alfarman jan ƙafarsa yayi tare da faɗin, "lalle Zainab kina da ƙoƙari har kinsan da Allah kike bin maza a titi? Sannan kike neman izinina ki shayar da yaron da ba jinina ba, naji zan barki ki shayar da shi jin abinda yace da sauri ta ɗago tana kallonsa da mamaki, shima ita yake kallo kafin taji yana faɗin, "amma idan nasan waye uban ɗan, "nikam na shiga uku Yaa Umar bazan iya faɗa maka wlh bazan iya ba, ɗaga kafaɗa yayi alaman i don't care yace "nikuma banyarda ki shayar da shiba, kasa motsi tayi ga kanta daya tsannanta sarawa riƙe kan tayi tama kasa mgna, jin yasa hannu ya figi jararirinne yasata miƙewa tare da riƙe saitin zuciyanta da ƙyar ta iya cewa, "dan Allah karka sake kaishi shara Yaa Umar badanni ba dan Allah kayi hkri! Katuna shima mutum ne ni ya kamata ka tsana hka bashi ba still tana riƙe da zuciyanta, cikin zafin zuciya dayake ji kamar zatayo waje yace, "wlh saina kasheshi ni zanzama ajalin wannan ɗan shegen inyaso ubansa yazo mu shiga kotu ya ƙare mgnar yana pointing ɗin jaririn da yake kuka kamar ransa zai fita kinga jin an kashe masa ɗansa sai ya bayyana ,abinda yace ne yasa zuciyanta wani harbawan da tuni ta zube agun, ganin yadda ta faɗine ya shi jan wani tsaki tare da dafe kansa, kusa da ita yazo ya ajiye jaririn dake faman kuka yabi gefenta ya haura sama, ɗakinsa ya nufa tare da bugo ƙofan da sanda giɗan ya ansa, sun kusa 5 mins agun banda kukan jariri bbu abinda yake tashi, Ladine da tashigo tattara wanke wanke ta ƙaraso da sauri jin kukan jariri kamar ana mintsininsa, abinda idonta yayi arba dashine yasata gigice da sauri ta ƙaraso gun tana jijjiga Antyn nata saide shiru, kuka ta fashe dashi tana faɗin "shikenan ta mutu da sauri ta miƙe ta nufa kitchen ruwa ta ɗibo da tazo ta zuba mata, still shiru babu motsi a gaba ta sata tana kuka ko takan jaririn bata ma bi ba, takai 2mins kafin a hankali tayi ajiyan zuciya jin kukan yaronta tayi agefenta ne yasata ta fara tuna duk abinda ya faru, duk son da take ta miƙe ta dauke shi ta kasa abinda ya farune ya shiga dawo mata a ƙwaƙwalluwanta, kawai sai hawaye ne kebin gafen idonta hannu tasa ta taɓa Ladi dake sharɓan kuka a gefenta, sai time ɗin ta ɗago cikin kuka,  "sannu Anty ya jikin bata ce komai ba da ido ta nuna mata jaririn sai time ɗin ta yunƙura ta ɗakko shi ta riƙe shi, dan kuka har muryansa tayi ciki ciki, kujeran dake gefe ta dafa ta miƙe tare da jingina a hankali ta zauna, miƙama Ladi hannu tayi alaman ta bata shi  da sauri ta miƙa mata rungume shi tayi tana sake zubar da hawaye, a kafaɗa tasa shi tana rarrashin sa amma kamar ana sake cewa yayi kukan duk yazama jajawurr, cikin kuka Ladi tace Anty kibashi nono mana, sakko dashi tayi daga kaɗarta tasa shi acinyanta ta gyarashi ɗaga rigar ta tayi ta ciro kyakkyawan breast ɗinta, sai kuma ta tuna da dokan Yaa Umar cikin kuka tace,  "Yaa Umar zai kasheni! ɗaga jaririn tayi tare da mayar da breast ɗinta ta miƙe sashi tayi a kaɗarta ta fara sintiri a parlorn yana kuka tana kuka, saide taji kukan ya tsaya  cak sakko dashi tayi tana jin yayi tsit tashi ɗaya idonsa sun kafe ga wani irin vibration da yakeyi, ganin abunda yakeyi ya mugun tsoratar da ita cikin tashin hankali tace,  "Ladi zai mutu na shiga uku me zan masa? Ladi ganin abinda yakeyi itama duk saita tsorata ta dafe ƙirji tana kallonsu tama kasa mgna, a gadarance ya sakko a stairs cikin ƙananan kaya shirt blue yasa da jeans baƙi, ko kallonsu baiyi ba yazo ya kama hanyan fita, ɗaukan jaririn tayi ta bi bayansa a firgice ta tasha gabansa cikin razata tace,  "Yaa Umar jaririn zai mutu ka temakeni nashiga uku, wani ƙasƙantaccen kallo yayi mata da rinannun idonsa, hakanne yasa ta tuna menene a tsakanin su cikin tsananin firgici da tashin hankali ta sake shi tare da kama hanyan fita saide kamar daga sama ta tsinto muryarsa a iska yana faɗin,  "banyarda ki fita ba in kuma kika fita a bakin aurenki sai zaɓa  Aurenki ko Ran jaririn da bazai taɓa miki rana ba a rayuwarki, jin abinda yace cak ta tsaya agun sai kuma ta juyo da gudu ta wuce ta koma parlorn, ajiyeshi tayi a kujera ta shiga toilet ruwan ɗumi ta tara ta fito a gigice, jakan ta buɗe taciro handkerchief ta dawo inda ta kwantar dashi tsomawa tayi ta matse ta ciro, a goshi ta sa masa still bai daina ba tayi kusan sau uku kafin cikin ikon Allah ya dawo normal, ɗagashi tayi ta rungume tare da fashewa da wani kuka, shikam tuni ya fice abinsa a gidan Ladima ta tana kuka ta koma ɗakinsu na masu aiki ganin abin yafi ƙarfinta.

Tajima agun tana kuka ganin zuciyarta na neman tsayawa irin na ɗazune yasata, tsagaita wa tana kallon jaririn da bacci yayi gaba dashi, jiki babu ƙwari ta miƙe a daddafe ta kama hanyan sama wannan karon tayi sa'a bai rufe ba wani ajiyan zuciya tayi tare da buɗe ɗakinta ta shiga, ƙarema ɗakin kallo takeyi yanda ta ganshi tsab ga ga ƙamshi turaren wutan daya kama ɗakin, lunshe idonta tayi tare da zubar da hawaye kawai tana tuna yadda lokaci ɗaya rayuwa ta sauya mata, tajima agun kafin kamar mai tsoron tafiya ta taka zuwa bakin gadon kwantar da shi tayi itama ta hau ɗan kishin giɗa tayi agun bacci ɓarawo yayi gaba da ita.

Unguwa Jaki...

Dukan da aka ɗaka mata ne ya sata miƙewa a firgice tana riƙe da kanta, ganin Mamanta tayi tsaye a kanta ta riƙe ƙugu, "dan uwarki ubanwa zaiyi wanke wanken kin nemi guri kin kwanta, ai bai Aure kinba bare mu fara raba aiki a gidan ga uniform ɗin yara na sch kuma kinsan gobe akwai makaranta baki wanke ba, kinzo kin kwanta kina bacci asara shegiya zuria'ar tsiya dangin butulu, tunda take zaginta banda kuka babu abinda ya kwace mata, "dan Allah Mamah kiyi hakuri,  " ubanki nace da haƙrin ta mutu sadakan nawa kika bayar? Miƙewa tayi ta nufi ƙofar fita da sauri ta pinciko ta tare da hankaɗa jin azaba tuni tasa ihu... "wayyo ciwo na! Wani mari ta zuba mata tana huci, "ke harkin kai ina mgna ki barni agun ki tafi daga yau idan nafara mgna saina dasa aya zaki bargun, kinji ko baki ji? Riƙe ƙuncinta tayi banda hawaye babu abinda yake sintiri a kumatunta cikin kuka tace, "toh" tsaki taja tafita ta barta agun tana kuka itama tabi bayanta inda wanke wanke da wanki suke gibge ta nufa.

Kusan tare suka shigo da mai Machine bayan la'asar, zaune take kan sallaya ta idar da sallah tagumi ta buga tare da faɗawa duniyar tunani, sallaman shine ya tadawo da ita daga inda ta shiga a ɗan tsorace ta ansa shi tace ya shigo, da sallama a bakinsa ya shigo ya tsuguna can gefe yana mata ya jiki, "da sauƙi abinda tace knan kuma sai ɗakin yayi tsit, "ga guri ka zauna kanata tsugunawa sai kuma tayi shiru kamar ba ita tayi mgnar ba, murmushi yayi mata duk da bashi take kallo ba yace, "a'a tafiya ma zanyi ga wannan babu yawa Allah yabaki lfy,. kallonsa tayi kafin tayi mgna, "harda ɗawainiya hka nagode Allah yasaka da alkhairi, "babu komai nikam zan koma Allah ya sauƙe,  " ameen nagode abinda tace knan shikuma ya fice, ko kallon ledan batayi bata kwanta akan sallayan datake kai. Sallaman Babanta ne yasata buɗe idonta data lumshe, murmushi yayi mata yana mata ya jiki da fara'arta ta ansa tana kallonsa yayinda shima ita yake kallo sun kasa ɗauke idonsu, yarasa meyasa a duk sanda ya kalleta yake jin sonta na ratsa duk wani ilahirin jikinsa ga wani kwanciyan hankali da yake ziyartar shi, "kinci abinci? Sunkuyar da kai tayi ta girgiza masa alaman a'a,  "meyasa ko babu ne? Da sauri tace, "akwai kawai na ƙoshine, "kin tabbata ta baki,  'eh Baba anbani ɗazu nafita dashi, "kinsan ina sani idan kimin ƙarya, rau rau tayi da ido kamar zatayi kuka tace, "naƙoshine mai Machine ya kawo wannan ta nuna ledan daya ajiye, hannu yasa ya ɗakko ya buɗe Multina, madara bread guda biyu da lemo da ayaba ya kawo mata, "kinga yanzu saiki sha Multina da madara zai temakeki sossi, shiru tayi batace komai ba dan gsky tana jin yunwa, cup ɗin dake gefenta ya ɗakko ya buɗe ya zuba half ya miƙa mata karɓa tayi ta ajiye a gefenta, ɓata rai yayi yace ɗauka ta sha babu musu ta ɗauka takai bakinta,  banko labulen ɗakin akayi daya sasu kallon waye,  "yauwa munafiki dama yaran sun jima da faɗa min kana kawo leda ban yarda ba sai yau, gun da ledan ke ajiye ta nufa tasa hannu ta wawuro,   "ai muma muna da hakkinka muda ƴaƴana wlh Allah bazai barka ba banza algungumi, miƙewa yayi tare da karɓan bread ɗin ya ajiye, bai ce mata komai ba shiya bi gefenta ya fice bayanshi tabi tana zaginsa har yafice a gidan, dawowa tayi ta ɗauki bread ɗin da madara ta ɗauke guntun Multinnan ta harareta ta fice, Zakkiya gaba ɗaya taji Mult ɗin ya ya fita ranta agun ta ajiye ta kifa kanta a ƙasa ta shiga rera kukanta.

Wannan book ɗin na kuɗine kibiya 500 ta wannan asusun *0562606466* Gt karkk manta 500 nace only sai kutura da sheda wannan num din *08039171989*

MATAR UBA...!!! Where stories live. Discover now