*MATAR UBA...!!!*
*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION* 🦅🪶
https://chat.whatsapp.com/DzRRptlSGkfEJySfd5kcUi
*Na Nanah khadii* 💅🏽🛍️
*Page 3&4*
*Sadaukarwa ga Leemart Pinky 💕*
Zaune suke a dinning cook ya jere abinci, Waleed tunda sukayi sallah suka sakko yake tambayan Mommynsa, jin zai dame sa da tambaya ne yasa shi fad'a masa, "yaci abinci yayi wanka yasa kayan bacci zai kai shi, koda suke mgna sai tym ɗin Ahmad yarone d'an kimanin shekara 10 yace, "but Dad kace zamu dawo mu sameta a gida am really missing her i can't eat without her, kallonsa Umar yayi yadda yake mgna kamar zaiyi kuka, "kaci abinci kaje kayi wanka kai kasa kayan bacci idan nima na shirya zan kaiku, jin abinda mahaifinsa yace tsab harda murna ya yarda nan yayi serving Ahmad shida Waleed kuma plate d'aya zasu ci.
Kwance take idonta lunshe, banda hawaye babu abinda yake zerya a idonta ga cikinta da yake mata ciwo kamar zata mutu, motsin ƙofar ne yasata ƙoƙarin buɗe lunsassun idonta saide da kyar ta ta iya ɗagosu sbd yadda takejin sun mata nauyi, ido huɗu sukayi da Dr. Abdool murmushin sa mai kyau yayi mata kafin yace, "nasan by now drip ɗin yaƙare and zan tafi gida kuma nasan babu mai kawo miki abinci, ledan da yake hannunsa ya dropping akan table ɗin gefenta, ruwan ya cire mata yana mata sannu kasa mgna tayi kawai sai hawaye da suke patrol a idonta, "kiyi hkri nasan kina cikin pains bansan meyafaru ba and i don't want to interfere in a family issue, but daga yadda na kalla abun dukanku bakuma juna adalci ba kuna musulmai, anyway ba hurumina bane gobe da safe zan sallameki insha Allah, tunda yake mgna ta sunkuyar da kanta ƙasa taƙi ko yadda su haɗa ido wato yasan komai knan, innalillahi wa'innah ilaihin raji'un lalle tashiga jarrabawar rayuwa kamar daga sama taji yana fad'in, "babu wani abu da yake damunki? Shiru tayi bata ce komai ba yakai kusan 2mins, kafin ya sake nanata tambayan still shiru juyawa yayi zaifita dakyar ta iya faɗin, "cikina yana min ciwo still kanta na ƙasa, "alright then zan turo nurse da magani Allah ya ƙara sauƙi, "ameen thank u abinda tace knan ta cigaba da rera kukanta.
Zaune suke sun zagaye shi suna jira yayi wanka yakai su gun Mommyn su, ganin yadda suke damunsa ya sa shi miƙewa ya ɗakko System d'insa, "kunga anbani wani assignment a office ku kwanta idan nagama zan tasheku sai mutafi ko? Yayi mgnar in a serious tone, abinka da yaro duk suka yarda suka kwanta ajikinshi agun sukayi bacci, sanda ya tabbatar sunyi nisa kafin ya gyara musu kwanciya ya fara zageye ɗakin, "wai me yake faruwa ne? Wato knan Zainab amanata take ci? Yana fad'in haka ya kaima wardrobe din dake gefensa wani naushi, da sanda ya lotsa yajima yana kaiwa da komowa a d'akin, ganin baida wani mafitane yashi shiga toilet yayi wanka tare da alola yazo ya shirya cikin kaftan, ya tada ik'aman sallah.
Yanda ya ajiye ledan kobi takai batayi ba, haka ta koma ta kwanta nurse ce tayi knocking tare da turo ƙofar ta shigo, tray ɗin mganin dake hannunta ta ajiye a gefe kafin tafara tambayanta, "Madam kinci abinci? Sai time ɗin ta buɗe kunburarrun idonta, "kai kawai ta kaɗa mata alaman a'a, "ai dole saikin cin abinci zaki sha mgani pls ki dage kici zanzo nabaki mgnani nanda 20mins, kukan da Babyn ya tsala ne yasata saurin zabura har ranta taji kukan nasa, ƙoƙarin miƙewa ta dakkosa takeyi saide jiri na d'iban ta ganin haka nurse d'in tace, "let me help u zauna kawai, babu musu ta koma ta zauna.
Nan taciro Babyn ta mik'a mata, tana karb'ansa ta zubar da hawayen dake mak'ale a idonta, hak'ik'a bahaushe yayi gaskiya kowani tsuntsu kukan gidansu yakeyi, wannan yaro sam bayi da jinin Yaa Umar, tab'ata nurse d'in tayi tana fad'in, "Madam Baby na kuka kin rik'e kina kallo kaman Tv, sai lokacin ta dawo daga tunanin data tafi, da temakon nurse d'in ta samu tabama Babyn zam-zam da dabino bayan ta topa duk wani addua dayazo bakinta(amama asali ga wanda musulunci ya tanadar Fatiha 1, ayatul kurisiyyu 1, izaja'a da alamnashrah, qulhullahu, falaƙi da nasi), kuma bbu laifi yasha nan Nurse ta takemake ta da ruwan zafi ta dama mata tea, ta ajiye gefenta kamar daga sama taji tana tambayanta, "am sorry to ask amma bakida yan uwa a garinnan ko? Kallon nurse ɗin tayi sai kuma ta mayarda kallonta zuwa ga Babyn da take tsananin so da tausayawa, "eh banida kowa a garinnan Aurene ya kawoni, "ayyah amma bakida Sisters ne? Jin tambayar yana nema ya wuce gona da iri yi tayi kamar bata jiba, kawai sai tace ta kwantar mata da Babyn, jiki a sanyaye ta karb'eshi ta kwantar dashi ta fice.
YOU ARE READING
MATAR UBA...!!!
RomanceHmm babu abinda zance kudai daga sunan kusan akwai abubuwan almara iri iri kawai kubi alƙalamina zan warware muku komai karku manta labarina ba ƙagagge bane lbrin gaskiya ne😍😔