humood ✨25

77 5 1
                                    

19/06/2023

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Lovesaga 💘

2️⃣5️⃣

Humood ✨

Azabure sumeey da hafsat suka mike, fuskar su ta shiga asalin firgici da mamaki....
buden bakin hafsat tace wannan wani irin jakanta ne da hauka ki wasu irin dakiken mutane be masu dabi'ar dabbobi...Bata Gama karasa abunda take Fadi ba linah ta daga hannu ta shararawa hafsat Mari, cikin Azaba ta dafe kuncita.

Nimrah dake daskare anan zaune gaba dayanta ajike sharkaf.
Wani hawayen bakin ciki ne suka tsiyayo daga idanunta zuwa kuncin ta.
Sumeey da gaba daya ta kidime,kallan Ahlam din Tai murya ta na tawa tace Wai ke meye damuwar ki damune?
Bama shiga harkar ki bansan dalilin dayasa zakina shiga tamu harkar ba.

Shiii!...A Dan zabure Sumeey Tai shuru, saboda yadda ta Fadi shii! Din tana gwale manyan idanuwa kikai dake nesa seka Dan tsorata.

Zaki mun  Shiru ko Sena zubae Miki da hokara,...Dan murmushin mugunta Ahlam Tai tace da baku shiga gona ta ba abunda ze sa inshiga taku,Karan bani da rawar Kai shi ya jaza muku.

Matsiyatan banza.... dariya suka fashe ita da gaiyar ta, sannan Kuma ta tsuke fuska kamar ba ita Tai dariya Yanzun ba,Dan dukufo wa Tai setin fuskar nimrah dake zaune ta kasa motsa Koda Yan yatsan ta ne.

Hannu takai fuskar tare da lakace Mata hanci Girl how market?
Ina fatan kin gane darasina na yau,
Duk da nasan kwakwalwar ki Bata ja Amma nasan tabbas zata dau wannan darasin,saura na gobe Kuma,
Dariya Ahlam ta sake fashewa dashi tare da sake Kai hannu zata lakaci hanci nimrah,se Kuma akai rashin sa,a nimrah Tai saurin damke hannun ta,
Dago idanunta da suka rine sukai jajir saboda bacin Rai ta sauke Kan Alham.

Hadewar idanunsu guri daya seda ya firgita Ahlam,ita kadai tasan me ta gano cikin Idon yarinyar Nan Amma ta dake, saboda ita Ahlam yarinya ce Wanda ko tana cikin firgici,bacin rai, ko farinciki,baka taba gane wa Kan fuskar ta,..firgicin ta na bayya ne kawai intaga mahaifin ta.

Cikin dakewa da zallar iskanci da nuna Kamar taji tsoran  tace...wayyo Ammie na zakanya zata cinye ni,
Bizge hannun ta Tai
Duk da Taki zafin rikon da Tai Mata  ta  hade Rai tare da cewa "Haka kike so kiga nayi ko"sede Ahlam ta wuce yadda kike tunani,.
Nidin damusa ce...daidai da kallan raini bana so bare takai ga antso kale ni,kedin Baki wuce zakanya me suffar  mage ba so stop acting tough,.ballantana awajena ke din Baki wuce magen ba ...
Mikewa nimrah Tai tsaye,ta maida kallanta kansu sumeey tare da furta "kuzo mutafi"
Ratsawa Tai ta gefen Ahlam zata wuce, batai aini ba se jinta Tai akasa ragwafa saura kadan ta buga bakin ta,

Da gangan Ahlam ta sa Mata kafa,Dan Daman hakan ma na cikin Shirin ta na yau,
Da sauri nimrah ta dage durkushe akasa ta waigi Ahlam.
Kanne Mata Ido daya Tai tace Oopps sowey😝, dariya ce ta barke awajan,se asannan nimrah ta gane cewa Basu kadai ne awajan ba harda ma mutanen dake zagaye da su ko ince reporting lives harda masu musu video.
Bakin ciki Kamar ze kashe nimrah,cikin sauri sumeey da hafsat suka yi kokarin dagota dakatar dasu Tai ta mike da kanta cikin jarumta,
Sanyi ne yake ratsa bargon jikin ta sakwamakon ruwan da suka juye Mata ajiki Dan har wani zazzabi da Fara ji..
Cikin Dakiya irin nata ta karasa gaban Ahlam,.
Da mamaki Ahlam take kallanta Dan batai tsammanin inta Mike zata sake waiwayen su ba.
Buden bakin ta se tace,"yau ta kasan ce ranar ki...to Amma fa ki sani akwai ranar da zata kasan ce ta wace,Kuma Ina me tabbatar Miki da a Wannan ranar...se Kuma Tai Shiru ta saki murmushi Wanda Yaba kowa mamaki, dukda Ahlam dince kadai tasan me take fada,Amma wannan murmushin nata yabawa kowa mamaki,
Cikin San sanin abunda zatai Mata Ahlam tace "meze faru wannan ranar"
Wani murmushin ta sake saki,sannan ta juya tare da kallan su sumeey
"Muje"

Humood!!!✨Where stories live. Discover now