humood✨5.angry bird

202 15 2
                                    

#wattpad
8/5/2021

Lovesaga💘

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨❤️

Humood ✨

5️⃣

Haka yana kukkunbura baki ba asan ranshi ba sukaje kofar gidan,door bell din dake manne abangon gidan Ameer ya danna...

Daga toilet tafito sanye da pink din towel din da ko cinyar ta be gama rufe wa ba hakama kanta dauke da karami wanda ta nannade gashinta aciki.tana waka.kwalla Kiran Sarah naji anyi muryar wata Mata.sarah,Sarah,.
Numfashi tasauke batare da ta ansaba Alhalin kuma taji,seda ta tabbatar tagama tsantsame kanta sannan tayi hanyar dakin dataji ana kiranta,ko sallama batai ba tace mom gani.

Sarah yanzu tsabar bakida mutunci kina ji Ina kiranki Amma baza ki iya bude bakinki kice naam ba ko.

Sorry Mom Allah banjiki bane,kikalle Ni fa daga bath nafito.

Kallanta mom Tai sama da kasa ta kare Mata kallo,dis gal ke har yanzu bakya kunyar yawo da Dan karaminka towel,.
Aww mom a gida fa nake kuma fa daga ke seni,wani ringing na door bell suka sake ji,
Ooh kinga ma Nina manta kije kiduba kofar Nan kiga wane.
Ok mom.
Fita Tai gantsan gantsan har kofa, CCTV din wajan ta Danna Sega fuskokin su Ameer sun bayyana,idanunta ne suka fara arba da fuskar humood,Dan zare ido Tai oh my! yau habibina ne dakansa.
Murmushin farinciki tasaka, watsa gashin kanta Tai yakoma baya sannan tasake gantsarewa kirjinta yafito sosai.

Bakin kofar takoma tare da sauke numfashi sannan tabude,
idanun Ameer da imran ne suka fara arba da ita, saurin kawar dakansa Ameer yayi tare da fadin ya Salam.
Tsaki imran yayi tare da galla Mata harara,yakula yarinyar Yar iskace duk sanda yazo kusan tsirara yake ganinta.

Wani tsakin yakuma jaa kinga malama kiwuce ki Sanya hijabi kin tsaremu da kallo.
Hankalin ta nakan humood dako kallo Bata isheshiba bema San abun suke tauyawa ba earphone ne akunnen sa.
Juyawa imran yayi tare da kallan humood ganin shi take kallo.

Dawowa kanta yayi madam zaki bude Mana kofa mushigo ne ko sekin gama talla da jikin tukun,Dan Naga kamar Wanda kikewa tallan abun be Ma sani ba.

Harar imran Tai imran bana San haka Naga alama bakasan zaman Lafiya tsakanina dakai.
Too😮Ina yayan yaje yau.lalle Sarah wuyanki ya Isa yanka.
Karasawa yayi kamar ze mangareta dalla gafara kibawa mutane hanya.saurin kaucewa Tai sanin halinsa basa jituwa ko kadan.
Ameer tinda yay Mata kallo Daya besake ba se Bata Rai dayayi kamar Hadari kallan humood yayi muje ko ratsawa yayi shima yashiga.

Dakamar baze bisu ba sekuma yashiga ,ganin ko kallanta beyiba harma ya wuce,Tai saurin riki hannunsa.
Riko hannunsa datai jiyayi kamar ta daura Masa gaurashi,wani wawan kallo ya aikamata idanunsa suka rine zuwa jaa,da sauri ta cika sa tsabar tsoron abunda tagani.
Beyi Magana ba se hannunsa Daya zura cikin pocket dinsa yazaro Hankey,goge inda ta taba yayi,sannan ya wulleta da shi a fuska tare da sakin dogon tsaki.

Yana juyawa kuwa harya fara tafiya beyi auni ba sejinta yayi abayansa ta rungumo shi hannun ta yazago har cikinsa.
Ransa inyayi dubu Saba,in to yabaci wani irin funcika yamata tare da hada kanta da bango ya daddalla Mata mari,har sau uku.
Ihuu tasaka na azama.
Mom najin ihunta Bata gama kimtsawa ba ta yafo Dan kwali tayo hanyar pallow..

Shako wuyanta yayi tafara mutsu mustun kwacewa har towel dinta Yana barazanar faduwa.
Kula da hakan da Ameer yayi yasa yayi sauri rike hannun humood, please stop it ba girman ka bane...she is just small girl hankali begama isarta ba.in ita Bata da hankali Kai Ina naka hankalin.

Sake ta yayi Yana huci ya karkade rigar sa.
Daidai mom tafito hangan Sarah Tai tana maida numfashi,kamar wacce Tai tsere.

Ran mom ne ya baci,tana ganinta haka ma base ta tambaya,tasan ita da humood,itakan ta tsani yaran Nan ji take kamar takashe shi,Amma wannan yarinya da shegen naci Wai shi take so,wani bazan kallo ta aika Masa

Humood!!!✨Donde viven las historias. Descúbrelo ahora