3/1/2022
#Wattpad
@fatimalawalbmg✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Lovesaga💘
Humood ✨
1️⃣7️⃣
Hade hannunsa biyu yayi tare da lankwasa murya kamar wani yaro yace please aunty kiyi Hakuri karki dakeshi,sorry on his behalf.
Shuru Tai tana kallanshi yadda yake Abu na Dan lokaci,Dan gyaran murya Tai tace fine na hakura,batare da ta Kuma kallan sa ba.
Murmushi yayi yace tnx u koke fa yanzu kinfi kyau.
Jin abunda yace yasake sata daga idanu ta sake kallan sa,se asannan takarewa kyakyawar fuskar sa kallo,Yana da manyan idanun dauke da lashes sannan Kuma Yana da tsiririn hanci, pink lips dinsa Yan daidai,Yana dauke da saje da lafiyyan Beard,fari ne sosai amma badan hausar dake bakin sa ba zaka iya yace wa ba dan Nan bane imma ko shidin ruwa biyu ne ko Kuma mazaunin Nan ne
,dogo ne Amma ba chan sosai ba Yana da fadin kirji,kyakyawa ne ajin karshe !for the third time kyawun namiji da ya birgeta
Zata iya cewa bayan humood wannan shike binsa a kyau,se sir Ameer da ya shigo class dinsu yau.Hadewar idanunsu guri daya yasata saurin sadda kanta kasa kamar Mara gaskiya,basarwa tai tafara Kiran sunan shaheeed let go.?
Chuchu dake boye abayansa girgiza Kai yayi yace naki din nasan Zaki dake Ni na fito, please Ajussi!karka Bari ta dakeni
Dan lanwkasa Kai Tai cikin daguwa tace please!abeg let's go!....
Jawo hannunsa yazeed yayi yadawo dashi ta gaba,hey boy! trust your sister okey?she promise bazata taba kaba,inhar ta tabaka nida kaina Zan rama maka!kaji?harararsa Tai jin abunda ya fada
Daga Kai yayi alamar gamsuwa!That's my boy!so now fada mun sunan didin naka?
Sanin halin chuchu! Tsab ze iya!ya zazzage Masa har abunda ya fi suna
Bana bawa strangers sunana kaga ne?
Jan hannun chuchu Tai sukai gaba..
Juyar da face dinsa chuchu yayi Yana hangen yazeed,da karfi ya bude muryar sa tare da cewa Ajussi kakirata da Auta.sannan ya fashe da dariya.
Hannu sumeey tasa taringa tallake keyarsaBin bayansu yayi da kallo shima Yana murmushi
har sanda sunka shige motar su dake wajan.Suna shiga ta zuba Masa lafiyayyun rankwashi aka,Wanda har sede ya challara kara!Didi kinyi promising baza ki dake ni ba fa?
Promise when did I?Mara mutunci badan Naja ka ba da wannan shegen bakin naka bansan me zaka fada Masa ba.thank goodness ba lalle mu sake haduwa ba bare ya Tina wani suna auta.Car key dinsa ne ya Fadi yayin da yake giftawa ta kusa da ita batare da yakula da ita ba ko Kuma yasan cewa ya yarda da wani Abu ba.
Sautin faduwan abun da taji yakai idanta wurin,batare da Bata lokaci ba ta dau key din tare da bin bayansa.
Saurin dayake ne yasa be jiyo ta ba Kuma ta kasa cin Masa.
Harsede da yaje jikin motarsa se asannan ya tsaya lalluben key din mota.
Excuse me?
Muryarta yaji Kamar daga sama, voice din dako a mafarki baze taba mantawa, voice din da ko farinciki yake yajita ze iya koma wa bakinci, voice din da yafara haddasa Masa tinani kalakala da azalzala a xuciyar sa.why is she here?tambayar da yayiwa kansa kenan.beyi yunkurin jiyowa ba.Excuse me?
Ajussi Daman ka Yar da car key dinka ne.gashi mikar da hannunta Tai tana Mika Masa.Rintse idanunsa yayi yayain da yake jin wani Kuna a xuciyar sa da kyar yake iya controlling kansa, dogon numfashi yasauke sannan ya sake fuska kamar bashi ba kafinnan ya juyo.
Fadi take azuci to kode kurma ne,immade kurma ne ko Kuma wrong person.mis....... harshenta ne ya harde batare da ta karasa word dake fitowa bakin ta ba.faduwar gaba ce Tai Mata mugun bazata.
Steps yayi yamatso inda take, Yi yayi kamar ma beta sanin ta a rayuwa bah thank you yace sannan yamika hannu ya karfi key dinsa,. security ya Danna tare da shigewa.