Da sallama ya shiga parlon dad dinsa, tsaye ya iske sa yana gyara hulan kansa da alama fita zaiyi. Zama yayi kasa inda dad dinsa ya zauna saman kujera sannan ya some gaishe sa.
“Ina kwana Abba”
“Alhamdulillah, daman kuwa ina son ganinka”
Ya fada yana saka agogonsa, sannan ya dago yana murmushi
Fawzan yace
“Toh Abba gani”
Abba yace daman maganar kwanaki ce zan maka, gaskiya it’s high time ka fara tunanin settling, kullum girma kakeyi ba yaro kake komawa ba”
Mami ce ta shigo da sallama tana murmushi, gefen Abba ta zauna inda Fawzan ya shiga gaishe ta bayan ya amsa tace
“Ai Alhaji kasan yana da wacce yake so, abinda ya tsaida sa yarinya zata fara zana jarabawarta ta fita secondary, yana jira ta gama sai ya tura gidansu yarinyar ko gaisuwa ne ayi”
Abba yace
“Tabbas hakane nasani, toh Allah ya tabbatar da alkhairi, ya sa ayi damu”
“Amin amin”
Abba ya mike inda Mami tabi bayansa suka fice a tare, Fawzan ma yabi bayansu don zai fita tare da abokinsa Ahmad.
A mota ne yayi dialing number din sahibarsa Samha.
“Hello” tace cikin yar siririyar muryarta.
“Hey babe, ya kike?”
“Lafiya lau, you?”
“Same, anjima zanzo insha Allah”
“Yeey! Da gaske?”
“Eh mana, da anyi isha’i zan shigo”
“To shikenan me zan aje maka?”
“Ai kinsan abinda nafi so, ke kadai kin ishe ni bana son komai”
Cike da shagwaba tace
“Ya Fawzan!”
Yayi dariya.
YOU ARE READING
FAWZAN KO ADEEL.
General FictionA story about a girl that thought she lost the Love of her life forever and ever, little did she know what faith has installed for her, let's go!