Daidai parlor suka ja suka tsaya, parlon cike yake da mata ko wace sanye da hijabinta, tsaye Samha tayi tana kare ma parlon din kallo taki cewa komai, Amal ce tayi karfin halin cewa
“Assalamu Alaikum”
Matan suka amsa da “Wa’alaikumus-salam”
“Samha!” Ta fada tana saukowa da gudu daga bene, tana zuwa ta makalkale ta tana kuka har rawa jikinta keyi kamar mazari.
Gaba daya Samha ta kasa koda kwakwaran motsi, duk da batasan meke faruwa ba, amma ko tambaya ta kasa.
“Sai hakuri Yusra” cewar wata mata dake zaune kasan carpet
“Ki daina kuka Yusra, addu’a yake bukata ba kuka ba” cewar wata
“Kiyi hakuri Yusra, Allah sa ya huta yasa iyakar wahalar kenan” cewar wata kuma tana goge hawaye.
“Meke faruwa?” Amal ta fada a razane
A hankali Yusra ta sassauta rikon da take ma Samha, sannan kuma ta janye jikinta daga gareta but still hannuwanta na kan Samha sunata kyarma.
“Ya tafi, Samha ya tafi, shikenan, ya... Innalillahi wa inna ilahir rajiun” ta fada tare da fadawa kan kafadun Samha tana cigaba da kuka.
“Wa?” Cewar Amal
A halin yanzu Yusra bata iya magana, sai da kyar ta samu ta tsaida kukannata, ta dago da rinnanun idanunta tana riko hannuwan Samha tana kallonta cikin ido.
“Ya... Fawzan...” wani irin kuka ta kuma fashewa dashi tare dasa hannu ta toshi bakinta, rintse idonta tayi gam gam tana cigaba da gunjin kuka.
Ware idanu Amal tayi a razane tare da fadin
“Innalillahi wa inna ilahir rajiun”Sarai Samha taji abinda akace, yarda ne kawai ta kasa.
Amal kuka take a hankali cike da tausayin Samha.
Cikin sheshekar kuka Yusra ke girgiza Samha ganin taki motsi tunda suka shigo
“Samha Kinji ni? Fawzan ya rasu ya riga mu gidan gaskiya”
Tuni take girgiza kai tana murmushi, tace
“Bakuda hankali? Wayace maku ya mutu? Fawzan bazai mutu yanzu ba, sai munyi aure mun haifi yara masu kyau, masu kama da babansu” ta fada tana murmushi already dreaming about it.Amal tana kuka ta rike Samha
“No ya Samha, ya mu...”“Bai mutu ba!” Ta fada tana mata wani wani irin mugun kallo
“Idan dai har ya mutu ku nuna mun gawarsa yanzu!” Ta fada cikin daga murya duk wani mahuluki dake gidan yana iya jinta.
“Samha...” cewar Yusra cikin kuka.
Kallonta Samha keyi kamar yau ta fara ganinta.
“Gawarsa bata ganuwa, plane crash fa ne, ya kone, ance ba’a gane shi a cikin gawawwakin kaf ba wanda ya rayu, daga can za’a rufe sa...”
Cikin tsawa tace
“Karya kikeyi ya Yusra, he can’t be dead, munyi magana yace mun zai dawo daya dawo zamuyi aure, lafiyansa kalau ki daina daura masa mutuwa”“Ya Samha...” Cewar Amal tana kuka
Mami ce ke saukowa daga bene idanunta sunyi luhu luhu sun kukkumbura, Samha na ganinta ta ruga inda take da sauri tare da hugging dinta.
“Mami kingansu ko? Ki fada masu Fawzan bai mutu ba zai dawo nan da lokacin kadan”
Wasu hawayen suka kuma sauko ma Mami, tana girgiza kanta cike da tausayin Samha.
Kamo ta Mami tayi ganin yadda kafafuwanta ke kyarma har tsayuwar ma na neman gagarta.
Kan kujera ta zaunar da ita sannan ita ma Mamin ta zauna gefenta tare da kamo hannuwanta duka biyun.
“Khadija nasan kin razana da jin wannan mummunan labarin da ya riske mu lokaci guda, duk da munsan da ciwo amma mutuwa dole ce ko munki ko munso zamu tafi, kowa lokacinsa yake jira ba tsumi ba dabara, wannan ranar itace ranar da Fawzan zai koma ga mahaliccinsa a rubuce yake, muna masa fatan aljanna ce makomarsa, Allah ya jikansa yasa mutuwa hutu ce a gareshi, kiyi masa addu’a shine kadai abinda yafi bukata a wannan lokacin, Fawzan yana sonki, yana kaunar ki, kamar yadda kike sonsa kike kaunarsa, wannan shi zai nuna irin son da kike masa shine kiyi masa addu’a”
Mami ta karasa zancen tana kokarin danne hawayen da ke kokarin sauko mata.Kura mata ido Samha tayi, gabanta yayi wani irin mummunan faduwa, kanta ya sara, jikinta ba abinda yakeyi sai kyarma, kokarin tashi tsaye takeyi amma ina biyu biyu take gani, kanta ya dinga juya mata kafin ta ankara sai ji tayi Mami na kokarin tarbo ta, amma ina Samha ta sume.
___________
YOU ARE READING
FAWZAN KO ADEEL.
General FictionA story about a girl that thought she lost the Love of her life forever and ever, little did she know what faith has installed for her, let's go!