CHAPTER THIRTEEN

0 0 0
                                    


Friday, 14 June 2019

Sai da ta dauki tsawon awa biyar tana ta bacci, lokacin data tashi da ciwon kai ta farka, hannunta ta dora saman goshinta tana addu’ar samun saukin ciwon kan da takeji, idanunta ta  bude Hilwa da Amal ta gani zaune kusa da ita.

“Sannu ya Samha” cewar Amal

Kallonsu kawai takeyi ba tare data ce komai ba, kamar ta tuna wani abu kuma sai ta mike zaune a zabure, kafadunta Hilwa ta dafa

“Am sorry Samha but he’s gone”

Kallonta Samha take tana son gaskata zancenta.
“Daman ba mafarki nake ba? Ba Gaskiya bane... kuce mun yana raye...”

“Haba don Allah Samha! Sai kace ba musulma ba? Ina iliminki ya tafi? Kin san daidai kinsan tawwakali shi musulmin kwarai da tawwakali aka sanshi, na fada miki ya rasu ya rasu ko ki yarda ko kar ki yarda ya rage naki” Hilwa ta fada a fusace

“Ya Hilwa kiyi mata a hankali...” cewar Amal

Bata tanka ba illa wayar Samha ta dauko ta shiga nemo hotunan Fawzan, wanda suka dauka a randa zai tafi ta shiga nuna mata. 

Bin wayar da kallo Samha tayi tana kallon hotunan a yayinda Hilwa ke ta scrolling tana fada mata cewar Fawzan ya tafi bazai dawo ba.

Bedsheet din dake kan gadon ta shiga damkowa da hannuwanta ta runtse idanunta gam gam.
“How?” Tace muryarta na rawa

Ganin Hilwa ta fara nasara yasa ta cigaba da magana

“Plane crash, ya mutu Samha, Fawzan ya tafi har abada bazai dawo ba, kiyi hakuri haka Allah ya kaddara...”

“Da gaske ya rasu? Ya tafi kenan ya rasu? Bazan sake ganinsa ba?” Ta fada wane yarinyar dake koyon magana

Amal ce ta rungume ta tana kuka
“Ya tafi ya Samha, dole zakiyi hakuri, ya rasu bazai sake dawowa duniya ba, Fawzan ya tafi... ya tafi har abada...” kasa karasawa tayi saboda kukan da yaci karfinta tana matukar tausayin yar uwarta.

Suna kallon sadda idanun Samha ke ciccikowa da hawaye, nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tana nuna kirjinta.

“Zuciyata zata buga ya Hilwa, ku taimaka mun, ina ma mutuwar nayi nima kila dana samu sauki” tace cikin rawar murya

Kafin ta ankara hawaye sun fara zubo mata.
Tashi tayi daga gadon tana kallon Hilwa.

“Fawzan ya tafi kenan? Ya rasu?” Ta fada tana tambayan Hilwa, Amal kasa daurewa tayi ta fice daga dakin tana kuka.

Girgiza kanta Hilwa ta shiga yi alamun eh sannan ta shiga girgiza ta da dan karfi
“Ya rasu, nace maki ya rasu, ya tafi kiyi kuka Samha, Please cry na roke ki kiyi kuka...” ta fada tana gunjin kuka tana cigaba da girgiza ta.

“Innalillahi wa inna ilahir rajiun” tayi ta nanatawa a take ta kurma ihu tare da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi, ganin haka yasa Hilwa yin hamdala gami da fita daga dakin da sauri.

Nan Samha ta zube kasa ta dinga kuka kamar ranta zai fita sai surutai takeyi, su mom ne suka tsaya bakin kofa suna kallonta cike da tausayi ba halin su rarrashe ta don kukan ake bukatar tayi daman.

Tafi minti talatin tana kukan nan, kafin a hankali ya fara ragewa, kwanciya kasa tayi hawayen na zuba tana ajiyar zuciya, mom ce ta isa inda take tana ganin mom tayi saurin rungumo ta, wani kukan ne yaci karfinta, sai da tayi mai isarta sannan dad yace.

“Ce Innalillahi wa inna ilahir rajiun” take tayita fadi, cikin ikon Allah ta rage radadin da takeji ta dan samu nutsuwa.

“Hada mata ruwan wanka kisa ruwan da zafi sosai” cewar mom tana rike da Samha.

FAWZAN KO ADEEL.Where stories live. Discover now