CHAPTER TWENTY EIGHT

0 0 0
                                    


Kura ma ceiling din dakin tayi bayan ta bude idanunta da kyar hawaye kawai ke kwarara daga idanunta, a hankali ta kai hannunta goshinta taji wani abu mai kauri nannade a wurin, dayan hannun ta kalla taga drip jone yana dripping kadan kadan, tabbas ba asibiti take ba a dakinta take, kofar dakin aka bude nan taga Haidar da wani mutum biye a bayanshi ko ba’a fada mata ba tasan likita ne. “Wow she’s awake welcome back Mrs Haidar” mutumin ya fada bayan ya zauna gefenta yana bude briefcase din da ya shigo dashi, murmushi ya sakar mata “How are you feeling? You finally woke up after 2days, Alhamdulillah you’re finally awake, your beloved husband is worried about you, gaskiya mijin nan naki yana sonki da yawa Mrs Haidar”  Ya fada yana examining dinta Haidar ne yayi murmushi ya zauna gefen Samha yana shafa gashin kanta, wani mugun kallo take watsa masa tana kokarin matsawa daga jikinsa. “Sannu baby na ya jikinki?” Ya fada yana riko mata free hannunta marar drip din, hawayenta ne suka cigaba da zuba ba kakkautawa. Share mata yakeyi da yatsansa yana kallon cikin idonta.   “Haidar garin yaya hakan ta faru da ita? Is like she’s suffering from domestic violence alamu sun nuna haka, sai dai wake mata haka tunda kaidai mijinta ne kuma ga dukkan alamu kana ji da ita...”  “N...o! Doctor Sufyan she’s not suffering from domestic violence no way! Fadowa tayi taji wannan ciwon”  “Ok I see, her face ta kumbura da yawa... well toh Allah bata lfy dai” ya fada yana yi mata Iv injections, bayan ya gama ya cire drip din daya kare ya jona wani, sannan yayi mata pain killers  “Sannu ko? Am... Haidar zan turo da nurse da zata na dinga duba ta da chanza drip da sauran medication din, yanzu ni Kaduna zan wuce amma if there’s any problem just call me for some advice, and by the way meyasa baka kaita asibiti ba? U prefer zamanta a gida?”  Ya sosa kai “Bana so tayi nisa dani ne Doctor, I want to take care of my wife da kyau”  Dariya Doctor din yayi “Da kyau, Sister Jane zata zo later kafin drip dinta ya kare”  “Ok doctor amma ba kwana zata nayi ba ko?”  “A’a kwana ya zama dole Mr Haidar, sai tazo” daga haka ya tattara kayansa ya kalli Samha  “Allah ya kara sauki Mrs Haidar take care”  Kai kawai ta iya gyadawa tana mamakin Haidar.   Jikinta takeson motsawa amma ta kasa sakamon tsami da jikin yayi, wani irin ciwo marar misaltuwa kanta ke mata, Haidar ne ya dawo da cup a hannunsa. “Tashi kisha magani”  As if you care...  “Tashi nace!”  “Ban iya tashi”  Dagata yayi da karfi tasa ihu. “Wayyo Allah mommy na!”  Ya kyalkyale da dariya. “Masu mommy manya” mika mata maganin yayi, itafa batason magani amai takeyi in tasha.  Tura mata maganin yayi da karfi cikin baki ya bata ruwan, ganin tana kokarin masa amai ya daka mata tsawa “Wallahi kika kuskura kikayi man amai a nan sai jikinki ya fada masu!”  Hadiye aman tayi da karfi tana maida numfashi, kokari takeyi tana maidawa amma ina hakan ya gagara nan ta dinga kwarara amai kamar zata amayar da yan cikinta.  “Shit! What the hell have you done? Are you crazy? Bana ce kar kiyi mun amai ba?”  “Am sorry I couldn’t help it, kayi hakuri”  “Thank God you’re sick wallahi dana koya maki lesson this minute!”  Fuu ya tashi ya shiga toilet ya wanke jikinsa, shiryawa yayi ya fita ya bar mata gidan gaba daya.   Kamar Saudat na jira ya fita ta shigo dakin da sauri, zama tayi gefenta ta riko ta. “Sannu Samha, wallahi bani na fada masa komai ba, Please believe me”  Murmushin karfin hali Samha tayi  “Don’t worry Saudat I know bazaki fada masa ba, kar ki damu”  “Amai kikayi?” Ta fada tana kallon aman  Gyada kai tayi a wahalce “Sannu bari na gyara wurin”   Taimaka mata tayi ta tashi tsaye ta jawo mata drip din ta kwantar da ita kan wata kujera sannan ta cire bedsheet din gaba daya ta sake wani, bayan ta kimtsa wurin ta maido ta kan gadon sannan ta fita da bedsheet din da niyyar wankewa. Har ta kai kofa Samha ta kira ta “Saudat...” Ta juyo  “Na’am” “Thank you” Taya murmushi sannan ta fita, ba’a juma sosai ba ta dawo da wani cup a hannunta, taimaka mata tayi ta tashi zaune  “Daure kisha custard dinnan Samha, bakomai cikinki” Da kyar ta tura rabi tace ta koshi, rufe mata tayi ta aje mata gefen bed dinta kan bed side drawer.  “Ki kwanta kiyi bacci, Allah ya sauwaka”  Hannunta ta kamo  “Noo don’t leave me Saudat am scared”  “A’a Samha kiyi hakuri kinsan ya gammu tare wani bala’in ne ki bari zan rika zuwa idan baya nan dai kinji?” Ta gyada kai alamun eh da sauri Saudat ta fita.   Da yamma nurse din tazo nan ta cigaba da bata kyakkawar kulawa, kullum da safe sai ta mata dressing, Haidar kuwa yana nan tunda nurse din tazo don ma kar Samha ta fada mata wata magana. Kullum Saudat ke bata abinci idan Haidar ya fita. Bayan kwana 2 Samha taji sauki Nurse din ta bar zuwa.   I swear Haidar you are going to pay for all the wrongdoings you inflicted on me, mark my words!

******1 week later....

Kwance take har yanzu bata ida warwarewa ba, dadinta tunda Haidar yaji mata ciwonnan bai kara neman yi mata fyada ba, amma yace da zarar ta warke babu fashi.   Kallonshi take yana saka agogonsa a hannu then ya dauki kayansa dake kan gado wanda yayi forcing Samha ta goge su tas, dukunkune take cikin bargo tace  “Please ka bari na gansu koda sau daya ne, ance Amal tazo rannan akace mata munyi tafiya while ba gaskiya bane, and nasan mom zata fara tunanin munyi tafiya ko bankwana ban masu ba, and nasan sunata trying wayana basa samu na”  Tace almost crying, rabonta da ganin yan gidansu har ta manta gashi aurensu har yana neman wata biyu, abin yayi yawa ay, gashi bata iya wuce gate saboda masu tsaron dake zagaye gidan, ko kofar shiga gida bata isa ta fita ba, da sunganta zasu nuna mata bindiga.   “Don’t dare me Samha! I already said no that’s it!” Ya dauki hularsa ya saka ta bisa kansa yana mata wani mugun kallo.   “I beg you... just for a little while koda minti daya ne...”  “Who do you want to go to first is it Fawzan.... or?”  “Kar ka kuskura kasa sunan Fawzan a ciki ya rasu let him Rest In Peace please” ta fada tana kallonsa a wulakance  “Good! So better stop asking about your family, bakida kowa sama dani yanzu, I am your damn family and this room is your home” wayarsa ya dauka saman mirror yayi gaba abinsa.  Tayi alkawarin bazata kara masa kuka ba enough is enough, she have to be strong and fight for herself and for her freedom!  She carefully made up her mind and smile weakly.  Tashi tayi, tayi wanka ta wanke gashinta da yayi mugun datti, bayan ta fito ta tsane shi tayi drying sannan ta gyara shi, kallon kanta take gaban mirror duk ta bi ta rame tayi qashin kashin wuya. Fuskanta duk tabon ciwo ne kala kala.  Shafa mai tayi ta fesa body spray, akwatinta ta shiga bincikawa neman kayan da zata sa, wata doguwar riga ta gani mai stripes din black and pink, tunawa tayi mahaifiyar Fawzan ce ta bata ita ranar wani birthday dinta as a gift, she was one of the nicest person Samha has a ever met, ta nuna mata so sosai.   Rigan ta saka amma abin mamaki wuyan rigan zamewa yakeyi, and shape din ya mata yawa, lokacin da take sa rigan cip take fitting dinta and now this? Veil ta saka pink color ta feshe turare a jikinta, dakinsa ta nufa nan ta shiga dube dube biro ta gani da pen, ta shiga rubutu kamar haka. “John ask the driver to take my wife to her father’s house now”  Dauka tayi tana murmushi ta fito waje bata damu da yadda suka sa mata bindiga ba direct wajen John ta nufa ta mika masa takardan. Kalla yayi yace “Meye wannan?”  “Karanta kaji mana”  Budewa yayi ya karanta, bayan ya gama ya kwala ma Bala kira.   “Bala zaka fita da madam! Make sure ka dawo da ita after 30 minutes”  “Ok sir! Muje”   Dadi ya cikata nan suka dauki hanyar gidansu she can’t wait to ser them.  Suna isa ta fito tayi ciki da gudu, a bakin kofa taci karo da mom hugging nata tayi cike da jin dadi. “Mom am so happy to see you! I missed you so much!”  Shirun da mom tayi yasa ta  janye jikinta daga jikin mom,   “What’s wrong mom? Are you alright?”  “Samha, I hope you’re alright meyasa zakiyi tafiya baki sanar damu ba?”  “Mom I...”  Amal ce ta fito a guje  “Mom it’s dad...!”  Da gudu mom ta hau sama, a gigice Samha tabi bayanta “Meyasamu dad?” Tace tana shigowa dakin  Ganin dad kwance kan gado da bandage nade a kirjinsa yasa Samha ta kalli mom idanunta cike da hawaye “What happened?”  Amal tayi hugging nata tana kuka tace “Ya Samha, dad was attack on his way back home from kano few weeks ago, Samha har gidanki naje akace baki nan zan fada maki me ake ciki, muna ta kiran wayarki kashe”  “Innalillahi wa inna ilahir rajiun! Attack by who?” Ta fada tana karasawa kusa dashi ta zube kasa   “Dad..!”  Bude idonsa yayi da kyar ya kalleta yana dariyar karfin hali  “My daughter... how are you?”  Kuka ta fashe dashi tace  “How are you feeling dad?”  Ya gyada kai yana murmushi  “Much better now”  Mikewa tayi tana kallon mom “Bazaku kaisa asibiti ba?”  “An sallame shi ay, ya dawo daga comma few weeks back, dressing kawai ake kaishi”  “Ya Rabbi bansani ba mom, who attacked him mom?”  “Yan fashi ne, suna demanding kudi a hannunsa, da yace babu suka harbe shi”  Hawaye kawai ke kawarara daga kumatunta sannan ta fice daga gidan da gudu tana kuka. Tana jin suna kwala mata kira amma ina har takai mota “Take me home now!”  Kuka kawai take a motan, suna shiga tayi sa’a motarsa na nan da alama ya dawo. Tana shiga ya daka mata tsawa “You go against my orders again Samha! How dare you!?”  Cikin kuka tace “You have no right to stop me from seeing my family...!”  “And who gave you the audacity to talk back at me?”  Tsanar da take ma Haidar bazata misaltu ba, take ta daga hannunta ta wanke shi da wani irin wawan mari, ta shiga nuna sa da yatsa cike da tsana!  “Never in your life think about hurting my family! Kasani nasan abinda kayi ma mahafina but wallahi wallahi! Pray that nothing else happens to my dad or I’ll make sure you pay for it and make myself your worst enemy ever!”  Gadan gadan ya taho zai rama marinsa tasa hannu ta rike hannunsa sannan ta wulla hannun nasa a iska tana kallonsa cikin ido!   “Idan ka haihu a cikin uwarka ka sakeni Sir Aliyu Haidar!”  Kallonta yakeyi cike da mamaki kafin ya tako daf da ita yana kare mata kallo kamar yana kallon abin kyama....”

FAWZAN KO ADEEL.Where stories live. Discover now