Bayan 2 days sai ga kayan sallah Haidar ya kawo mata atamfa guda 2, lace, takalmi, jaka, kayan kwalliya, turare and 3 matching veils, ba karamin mamaki tayi ba, da farko batasan waya aiko ba sai dai akace gashi akace a bata.
Daki ta koma tana budewa taci karo da note ta bude_How’s my princess doing today? Hope good? I love you with all my heart Barka da sallah in advance_
Batasan lokacin da murmushi ya su6uce mata ba, wayarta ta dauka ta kirashi a karo na farko a rayuwarta.
“Baby na” yace cikin shaukin so
“Your message arrived just now”
“Yea, do you like it?”
“I do but I can’t accept them”
“Why? Saboda baki sona or ban isa ba?”
Nan take ta gane ranshi ya baci
“Ba haka bane wallahi”
“Then explain...”
Shiru tayi ba tare data ce komai ba.
“Yanzu har rashin son da kike mun ya kai kiyi denying kyautar dana baki?”
“Wallahi a’a, nagode sosai Allah kara budi na alkhairi”
Tanaji yana dariya
“Haba har naji dadi, toh ranar sallah dai I will be expecting pictures ko?”“Okay, but on one condition”
“What?”
“You send me yours too”
“Really princess? That means you want to see your handsome boyfriend’s kwalliyan sallah”
Murya kasa kasa tace
“Done”
“And su Ayman”
“Yes ma”
Yaji tayi dariya, a beautiful laugh
*****EID DAY
Samha batasa kayanta masu tsada ba wanda Dad dinta ya mata ba, na Haidar ta saka tashiga daukan pictures tana sending masa.
Ba 6ata lokaci taga call dinsa na shigowa
“You look stunning my love”
“Thank you, you all looked beautiful too”
Ya turo mata family pictures din da suka dauka gaba daya. Ba karya sunyi kyau sosai.“So ya sallah din?”
“Alhamdulillah”
“Masha Allah, ya kamata nazo na biya kudin kwalliyan nan ay ko?”
“Uhm”
“My princess kenan, ko kar nazo?”
Tayi murmushi
“Toh sai nazo take care of yourself for me, I love you”
“Thank you” tace kafin tayi disconnecting call din.
****After magrib
Bayan sallah yazo for the first time gidansu Samha, yasamu kyakkawan tarba daga iyayenta, nan ya shaida ma mahafinta yana so a bashi dama ya turo da iyayensa suzo, dad yace an bashi amma ya tabbatar ya samu kyakkwan fahimta daga yarinya ma’ana su daidaita kansu.
Sun sha hira da Samha inda ya bata kudi 20k yasha gwagwarmaya kafin ta kar6a, bankwana sukayi ya tafi ita kuma ta koma gida.
***
Ba 6ata lokaci Haidar ya turo gidansu Samha da niyyar formal introduction amma sai dad ya bukaci saka rana da duk abinda ya kamata, an sa 2 weeks immediately after their second semester exams.
Washe gari aka turo kayan sa rana, tadai sha zolaya wurin Yasmin kamar me.
YOU ARE READING
FAWZAN KO ADEEL.
General FictionA story about a girl that thought she lost the Love of her life forever and ever, little did she know what faith has installed for her, let's go!