3

122 20 2
                                        

Murya 3
Zahra Tabiu

Ai kawai sai Tafisu za zari mayafi akan igiya ba ta bi ta yaranta ba ta fantsama garin hayin tudu wajen kanwar mijinta margayi, Dije 'yar Babandi. Gida cike yake makil kowa shagalinsa yake domin kuwa a yau din ne aka daura auren Aminatu, ashe angon dai bai wuce dan dijen ba Yusuf da ya je cirani Lagos ya dawo.

A ranar idon Tafisu ya rufe saboda bacin rai ta dubi Dije yar babandi ta fara gaya mata son ranta.

"Haba dije! Yanzu yar tawa da na haifa a cikina za a daurawa aure ban sani ba? Shin an mana adalci ni da ita kenen? Yarinyar nan da babanta na da rai har makarantar primary ta gama, amma mutuwa mai tonon asiri daga dawowarta wajen ki kika fara dora ma ta talla. Ina ji ina gani ban ce komai ba. Har inda nake ake kawo min labarin azabtarwar da kike ma ta ,na toshe kunnuwa na. Wannan bai ishe ki ba sai a daura mata aure yar shekara goma sha biyu! Ba kya bari ta dan tasa! Kina gani a kauyukan namu da na kusa da mu yadda cutar yoyon fitsari ta mamaye mu, so kike irin haka ta faru da ita? "

Ai fa ,wannan maganganu sun fusata dije sai ta ke kallon Tafisu a matsayin butulu ta rike mata diya har ta aurar bata gani ba.Don haka sai cacar baki. Yan biki da makota suka taru dankam! Ana kallo kamar a talabijin, a samu wanda zai raba ma ya zama babban aiki.

Kawai saboda tsabar zafin zuciya sai Dije ta daka tsalle a matsayinta na yar gajeruwar mata ta tsinkawa Tafi mari. Wannan cin mutunci ya batawa Tafi rai, ga mari ga tsinka jaka? Ita aka yiwa laifi kuma sai a bita har da duka. Kawai sai zuciya ta debe ta dama doguwa take mai dirarran jiki. Ta dauki Dije da hannu ta nunawa Allah ta kuma kwandara ta da kasa. Habawa sai kici kici aka fara dambe kamar kananan yara. Da gudu aka je aka kira angon da uban ango su suka raba wanann dambe, Aminatu dai na gefe tana zubar da hawaye.

Duk inda fusata take sai da Dije ta nemo ta ara ta yafa.Domin kuwa bakinta yayi suntumtum idonta yana ta zubar da hawayen azaba. Ta nuna Tafi da dan yatsa ta ce.

"kwarankwatsa dubu in an cigaba da auren nan uwata shegiya ta haife ni! A zo har gida a zagen a ci mutunci na a duken akan auren da nayi don in rufawa yar ki asiri? Yarinyar da ta rasa masoya bakin jini gare ta fa, ku da yake 'ya'yan mage ne sai kika nuna min halinku irin na zuriarku wato butulci. To daga yau ba sai gobe ba an kare aure! "

Ta gyara daurin zaninta da ke neman fadi kasa ya mata tsirara ta nuna dan na ta

"Maza yusufu. In ka haihu cikina, wato ni uwarka. Sau ma ta diyar ta, ta tafi ta bamu wuri"

Da jin wannan kalma sai idon Tafi ya fara kifkiftawa, hanjin cikinta ya fara kadawa, gabanta na dukan uku uku. Ta san abunda zai biyo bayan sakin Aminatu wani alamari ne mai girma da ba zai mata dadi ba. Na farkon iyayenta za suyi fushi da ita sanann yan gari zasu tsangwame ta cewar ta kashewa yar ta aure ranar da aka daura wani abu da bai taba faruwa ba.

Daga Tafi har sauran jamaa aka fara bawa Dije hakuri amma inaaa! Ta yi tsalle ta dire tace ba da ita ba. Da ta ga dan nata yana inda inda zai ta dube shi ta ce

"Idan baka bi abunda nace ba, zan daga maka mama!! Sai ka biya ni wanda na shayar da kai"

A take yusuf yana kuka ya saki Aminatu ya fice daga gidan. Kawai sai dije ta shiga daki dan kayan taron da Aminatu tayi da kudin tallar ta. Kawai ta fara wurgo su waje. Har da mai rose sabin yayi da fanteka kala kala, ji ka ke

"tush! Tush! Kyangyaran! "
Ta ce Tafi ta kwashi tsiyarta da kayansu suyi gaba. Tafi na kuka ta kwashe ta dorawa wani yaro ta kama hannun Aminatu suka yi hanyar kauyensu.

Ashe tun ana wannan harkallar aka samu wani yaro dan hau ya falfala ya je ya fada a gidansu. Don haka ko lokacin da ta isa labari ya riga ya iske iyayenta. Kowa yayi carko carko ne a tsakar gida lokacin da ta iso, sai tayi turus.

MURYA -Gajeren LabariWhere stories live. Discover now