Murya 4
Zahra TabiuCikin ikon Allah kafin kace kwabo Tafi da yaranta sun mike. Sanaa ba kama hannun yaro. Kuma sai komawarsu unguwar ya zo musu da tulin alheri. Mutane sukai ta aiko da daka da surfe. Tun da suka fara alewar yara sai ya zamana gidan ba a raba shi da sallamar yara.
"Akwai mandula? "
"Akwai tsami gaye ko carbin malam"
Muryoyin da za kai ta ji kenen. Ba a rufa wata daya ba yaran suka koma makaranta don ita Aminatu ma sai aka saka ta a wata makarantar sakandare ta je ka ka dawo. Da ibrahim da usman su ke zuwa makarantar primary. Shi kuwa Manu ta kan zauna da shi ne a gida tana sauran aikace aikace tunda bai isa makaranta ba.
Tana son ta koma makaranta amma ta san a halin da ake ciki a lokacin abun ba zai yiwu ba. Kudaden hannunta ba wasu masu yawa ba ne, hakannan shi kan sa manu ba ta da wanda za ta barwa shi. Da a ce ma ba a kore ta daga gidansu ba ne sai ta dunga barwa mahaifiyarta. Anan dai ta maida hankali ga yaranta wanda ganin su kadai yake faranta mata rai.
Me zai faru?
Sai gari ya dauka ai ga Tafi can tana zaman kanta, ta kama gida ta kuma kwace yara. Ta giga ta zama abunda ta zama. Sai su ka ce da wa Allah ya hada su in ba da ita ba?Wannan lamari ya kara kular da iyayenta da sauran dangi. Mahaifinta kan ce ya gane tabbas ya haifi yar kanta mai kunnen kashi da bata jin magana.Matar da wai zata zabi siyar da kayan kwalam da makulashe don ta rike yara ta kuma ki zaman aure….wata irin mace ce?
Musamman mahaifiyarta ta yafo mayafi ta zo inda take ta kuma gaya mata sakon karshe. Babanta yace in dai tana so su shirya sai ta maida yara dangin ubansu ta koma gidan tsohon mijinta ta zauna.
A ranar ne Tafi ta san tayi kuka me yawa, irin kukan nan da yake makale maka a makoshi. Sai ya sa ka ji zuciyarka na bugun tara tara. Wani abu ya zame maka kulli a zuci numfashi na neman gagararka. Daga karshe ta samu ta fashe da wani kuka. Har yaran suka dawo a hakan suka tadda ita. Hankalinsu ya tashi,nan dai suka yi ta lallashinta.
Tayi shiru tana tunani ta kuma yanke hukunci da cewar ba zata koma ba. Ta kan je ta gaishe su akai akai, wataran su amsa wataran ko kallo ba ta ishe su ba.
Za a yi kamar shekara daya da rabi Manu ya dan tasa sai Tafi tayi tunanin ta koma makaranta ko da ta yaki da jahilci ce. An cire ta ne a aji uku na karamar sakandare, tana so ta karasa ko da satifiket na sakandare din ne ta samu. Saura kuma sai abunda Allah yayi. A halin yanzu kudi sun dan zauna a hannunta ta ma daina surfe da daka.
Mutane daga kauyuka mabanbanta suna zuwa sarin alawowi daban daban ana kaiwa kasuwanni irin na su Maigatari da ke ci ranar Alhamis. kasuwar wudil ,ta Bichi da kasuwar lahadin makoli. A halin yanzu ba Tafi da yaranta kadai ke aiki ba akwai matan unguwa da ta dauka suke taimaka mata ake ba su lada. A wannan lokaci ba ma ta samun zawarawan da suke kawo mata caffa, a cewar yan gari tafi karfin duk namiji. Don haka duk wanda ya kai gidansa ma ya daukowa kansa kara da kiyashi. Don haka sai ta aje batun aure a gefe ta doshi abunda take ganin zai fisshe ta.
Ta jefa Manu a makarantar yara ita ma kuma ta koma makaranta.
Bayan shekara Ashirin
Kwas kwas kwas
Wata mata ce kakkaura da akalla za tayi shekara Arbain da biyar sanya da fararen kaya irin na aikin jinya take takawa a hankali zuwa motar ta.
Fuskarta ta kadaran kadahan ta latsa security din mota yayi kara alamun budewa ta fara ajiye file file da takardunta a ciki. Ta ji an kwala mata kira
"Sister Tafi, Sister Tafi"
Ta waiwayo a hankali ganin matar yasa ta washe baki .Bayan sun gaisa tana cewa"Sister Kulu ashe kin shigo. Allah ya so ba za muyi sabani ba"
YOU ARE READING
MURYA -Gajeren Labari
Short StoryLabarin zawarcin Tafisu, gwagwarmayarta akan 'ya'yanta