2

150 17 12
                                        

Murya 2
Zahra Tabiu

"Tunkwal tunkwal " Tafisu ke daka a tsakar gidansu. Tana mai tuno ranar da ta bi marrarrabar kasuwa tana tunanin mafitar rayuwa. Yau za a yi wata shida da mutuwar aurenta. Babu yadda ba a bawa maigidanta baki ba akan ya maida ta yayi kememe ya ki. Daga karshe ma sai ya bada wani sharadi

"In dai har Tafi tana son tayi zaman aure a gidana to fa sai ta bi dokoki na. Yaranta ba zasu tako su zo gidana ba, ita ma kuma ba za ta taka ta je dangin tsohon mijinta ba. Domin ni babu yadda za a yi ina auren mace tana yin gaban kanta! Ta taka ta je gidan dangin tsohon miji! To ba da ni za a yi wannan sakalcin ba. Sai ta zaba ko ni ko yaranta"

A fusace yake wannan maganar yana kumfar baki.

Tafisu kuwa tayi tsalle ta dire ta ce bata aminta da wannan sharadi ba. Daga nan shi kuwa ya ce ba zai maidata ba. Karshen auren kenen. Iyayenta suka fusata ainun don ganin wai ta bijire masa, abun da ya kawo takun saka tsakaninta da su.

Tunkwal tunkwal ta cigaba da wannan dakan tana tuno yadda rayuwarta ta koma gaba kura baya sayaki. Domin bayan dawowarta sai mahaifiyarta kyallu ta daina mata magana. Hakan bai isa ba sai ta bita da wasu zafafan kalmomi

"Ba kin ki zaman aure ba? To sai ki zauna da ni da ke mu jera kafada a gidan ubanki! Sabulun wanka ma da na wanki ya ishe ki. Taro na ba kya gani ba! Kina diya mace wacce za a kai gidan wani har ki ce kina da ra'ayin kan ki? Wacece ke yaushe kika zo duniya? Yaushe aka haife ki? Sai kulafuncin 'ya'ya!  Yaran ki ne? Da su kika je gidan miji? Sai ki bar su a wajen dangin ubansu domin kuwa su ne dolensu! "

Inna kyallu ta ja numfashi

"Aure dai shi ya haife ki don haka ba ki isa ki guje shi ba. Duk takamar mace dakin mijinta. Kuma dole ki masa biyayya. Idan ba kiyi ba, to ba zaki taba ganin daidai ba. Ba zawarci ba? Shi kika fi so? To ga ki ga shi! "
"Tafi! "

Kiran da ya dawo da ita kenen daga dogon tunani. So take ta koma makaranta. So take ta cika burinta. Amma bata san yadda za ta yi ba.

Sako ne na cewar mahaifinta na kira
Haka ta karasa wajensa tana sun sun da kai, tunda ta dawo gidan take rabe rabe kamar wacce ta aikata wani laifi. To laifin kenen.. zawarci

Ya kura mata ido yana mai kas da tabaraun sa. Ya ce

"Uwaki bata gaya miki ba, ni gidana ba a zawarci? "

Anan ne take gaya masa cewar tana son ta koma makaranta, alabashi daya baya sai tayi auren.Wani kallo yake jefa ma ta irin na wanda ba zai rabauta ba. Ta ce

"Baba ka ga wannan tsilla tsilla da nake yi duk rashin ilimi ne da rashin abun yi. Da zan tsaya da kafafuna ka ga lalurorin yarana ba sai an kai ruwa rana ba. Dukkaninsu suna bukatar kulawa ne da kuma tabbiyya irinta uwa. Idan na samu na koma makarantar nan… "

"Dakata" ya ce da ita "Alhuda huda sarkin karatu. Ke ma kina so ki zama irin matan nan masu tawaye da bijirewa Ubangiji. An ce kiyi aure kike maganar boko? Uwarki ma ba ta yi ba, shin ko kin ga abunda ya same ta? Kin gan ta a halin ha'ula'i? Watakila ha'ula'in da ta shiga bai wuce na haifar bijirarriya irinki ba. "

Ya kama kunnensa

"Ki fito da miji kiyi aure, ki ajiye tunanin yaran nan a gefe. Ba a kan ki aka fara haihuwa ba ba kuma a kan ki za a kare ba. Ni bana aje bazawara a gidana, ba a zawarci. Na baki wata uku. "

Daga haka bai kara cewa tak ba!

Buri ya bi ruwa kenen? Karshen kaddarar kenen?

Zawarawa suka yo mata caaaa, da yake babu laifi tana da mamora dirirrayiyar mace ce mai siffa ta ban shaawa. Ta ki zaban ko daya.Sai ma ta kama kananun sana'o'i irinsu surfe,daka.Sai kuma ta fara irin alawoyin nan na yara su mandula, tsami gaye da su carbin malam. Don takaici har Inna kyallu kan ce

"Lallai!! Tafi an daurawa zawarci zani! An bashi gindin zama! "

A haka ranan yaran makotansu ya shigo ta koya masa home work, aji uku ta yi na makarantar sakandare amma ba karamin kokari ne da ita ba. Da haka da haka sai ta fara tara yara kanana tana koya musu Abcd da su 1234 da kananun lissafin a ranakun karshe sati. Duk wanda zai zo sai taho da N20. Wannan koyar da karatun yana sa ta nishadi. Sa ta ji ta kamar a makaranta take, ta zama malama. Hakan ya kan sa ta cikin nishadi da jin rayuwarta tana da "purpose". Har ma suke kiran wajen da "makarantar aunty".

Dan kudin da take samu sai takan siya su sabulu, omo da yan abubuwan amfani ta kai gidan Malam Mudi na 'ya'yanta saboda ganin su da take yi a kullum suna yawo diki diki! Sun rame sun lalace ba zaka ce sune yaranta ba idan ka san su a da.

Yaranta guda uku ne a gidan usman da Ibrahim da aka dawo dasu daga almajiranta saboda tsautsayin da ya samu Ibrahim din. Sai kuma karamin yaronta wanda ta bada shi bayan ta yaye shi. Ga yara nan zaune kara zube ba Arabi ba boko. Ita ba ta yi ilimi ba yaranta ma ba za suyi ba? Gaskiya ba zata zabu ba bindiga a ruwa!

A hankali a hankali sai ta fara jan hankalinsu, suna zuwa tana musu wanka fes fes, ta shafa musu mai ta ba su abinci su ci su koshi. Tafi-tafi ranann ta je ta musu rijista a wata makarantar gwamnati ta nan garinsu. Ranar da ibrahim da usman suka ga yinifom, habawa! Sai murna da rawa. Ibrahim Ya ce

"Mama Allah zumbuda ki a aljanna!! Muma za mu je makaranta irinsu Hadi. Idan na girma na zama gwamna zan kai ki makkah! "

Wata dariya Tafisu tayi, irin dariyar nan da uwa kan yi lokacin da ta shagalta a soyayyar 'ya'yanta. Irin dariyar nan mai cike da buri, mai fatan gobe ta yi kyau!

Da gudu suka fita sai gidan Baba Mudi sun sanar masa wannan babban alamari amma me? jimawa kadan sai ya iso gidan da baccon kaya hannunsa rike da manu dan karamin yaronta, sauran na bin sa a baya.

Cin mutunci ne ya mata, ya kuma gaya mata ga yaran nan dama ya gaji. Tunda bata ga kokarinsu ba har ta sa yara a makaranta to sai ta je ta rike yayanta.

Ta ce to a basu gidan gadonsu su zauna da yaranta, amma me? A rashin saninta tuni ya cefanar da gida.Babu gida babu kudin gida babu dalilinsa.

Iyayenta suka yi mata caaa! Kan cewar ta zake. Su kan ce

"uwar son 'ya'ya"
A ranar dai Tafi ba ta samu bacci ba.

Wai menene mafita?

Surfe aka kawo mata, yi dai take yayin da hankalinta yana wani waje. Ina za ta je da yara? Ta san babanta ba barinta zai yi ba. Maganar gaskiya ita ce ba zata cire yaranta daga makaranta ba, ko da hakan zai sa a kore ta daga gida. To amma ina za ta?

Ashe tsugunne dai bata kare ba
Da gudu usman ya rugo ya na mai mika mata wani kulli.

Alawa ce da cingam a kulle a leda, ta fara tambayar na menene. Sai cewa yayi

"Cewa aka yi a kawo miki, cingam din daurin aure Aminatu ne a can hayin tudu.Wai biki da tariya sati na sama! "

Kyan gyaran… .!
Tabaryar ta fadi ta gangara ta wani wajen
Ji tayi bata gani
Wani irin duhu ne marar misaltuwa
Ta dafe kirjinta ta ce

"Diyar tawa yar shekara goma sha biyu aka daurawa aure!!? "

"Ban gane ba!! "

MURYA -Gajeren LabariWhere stories live. Discover now