Gajeran Labari
Zahra TabiuMURYA
(Shin mace na da murya? Idan ta yi magana za a ji?)Kwanaki arbain kenen da rasuwar Malam Idi mijin Tafisu kuma a ranar ne aka ce kowa ya hallara. Yayansa Malam Mudi shi ya tsaya ƙerere yana nuna mata ɗan yatsansa cikin karin harshensa ya ce
"Saurara Tahisu, wadanga ɗiya hwa babu mai bar maki su wurinki. Yaushe na aka barin ɗiya hannun macce su tanbaɗe a zanka kiransu ɗiyan mace?" Ya ɗaga hannu ya daki wani murfin taga na langa-langa ya ɗora da faɗin
"Wanga gidan dukiyat marayu na, kuma kassuwa zai shiga, haka su ma gonakin. Ɗiya da dukiyat su duk alhakin su na bisa wuyana. Ni nissha mama ni saki ubansu marigayi ya kama. Kin san dukiyat marayu bata son wargi, shi na nika so in tattala musu abunsu in zanka juya masu har su kawo karhi. Abun da babba ya hango da zaune yaro ko rimi ya hau ba shi gani nai"
Wani irin numfashi Tafisu ke fitarwa na tsananin baƙin ciki amma bakinta ya mata nauyi ta kasa cewa wani abu. Ta san wannan wani salon danniya ne da zalunci. Tun da kuwa kowa ya san margayin ko cikin 'yanuwansa ya dan fi su samu, za a iya cewa ya dan bar wani abun tunda har gida gareshi na kashin kan sa. Ga yara hudu ya bari ita ba wata madogara ba sai kuma a ce ba za a raba gadonsu ba?
Hankalinta bai kara tashi ba sai da Malam Ali wani babban aminin margayin ya nuna yaran ya fara yi musu kashin dankali. Ya ce
"Ai da yake mun gama shawara da Malam mudi yanzu za kiji yanda mu ka zartar. Wadannan yaran biyu Usman da Ibrahim almajiranci za a tura su, badi ya war haka sai ki ga sun kawo goma a kan su cif! Ita kuma Aminatu dama akwai kanwarsu Dije ta Hayin-Tudu har yau Allah bai ba ta haihuwa ba sai ta rike ta. Shi kuwa wannan na goye Manu ai ya kusa yaye, kina yaye shi Malam Mudi ya ce zai gama shi da dan wajensa Murtala na amaryarsa Tasalla sai su taso abunsu tare. A haka a haka ana kular musu da dukiyarsu har su girma su amshi abun su"
Bai ko dire zancen ba ta gane bakinsu daya, so ake a yashe 'yar dukiyar a raba ta da yaranta. Kawai sai ta fashe da kuka saboda rauninta. To a haka duk ragowar dangi suka saka baki ana kara godewa halacci irin na Malam Mudi da ya rungume dukiya da kuma marayun Allah.
Haka Tafisu ta cigaba da sauraren hukunci akan 'ya'yan cikinta hawaye wani na bin wani cikin tsananin kunci da rashin 'yancin kai. Ta dauka za a bar musu gidan gadonsu ne su zauna ita da 'ya'yanta. Ta dauka za a taimaka musu ne a yayin da take tare da 'ya'yanta ta tallafe su. Ashe abun duk ba haka ba ne? Ashe bata da wani 'yanci akan hakan? Tana kare takabarta ta yaye Manu,suka karbe. Aka ce ta kwashe na- ta -ya -na -ta ta koma gidansu. Babu wanda ya yi bi ta kan maganar tumunin takabarta ma. A tsawon lokuta Tafisu kan nutse cikin tunanin rayuwar yaranta. Ta na ji tana gani an raba su ba tare da ta na da ikon canja hakan ba. Shin wani hali suke ciki? Shi ne abun tambaya. Ba ta yi cikakken wata shida a gida ba, ba ta ajiye ba ba ta kuma bawa wani ajiya ba mahaifiyar ta ta dube ta ta ce
" Tafi, mahaifinki ya yi min maganar ki. Yace a fadi maki shi gidansa ba a zawarci. Girma ya taso masa ba zai iya daukan dawainiyarki ba ya dauki ta kannenki. Ya ce cikin manemanki kiyi kokari ki fidda guda daya ki yi aure. Mace idan ta wuce zaman gida to fa ta wuce"
Wani irin abu ne marar dadi ya gifta a ranta. Aure kuma? To yaushe ma ta gama alhinin mijinta? To yaushe ma ta gama farfadowa daga jimamin rashin yaranta. Me yasa duk ba a damu ba? Me yasa ake kallonta a matsayin wani nauyi? Wani nauyi da kowa ke gudu? Ta tuna irin yadda ta kan je gidan Malam Mudi ta tarar da dan yaronta Manu diki -diki kana kallonsa ka san yana bukatar kulawa. To amma ta san yanzu idan ta matsa cewa za ayi bata da kara.
A lokacin da ta gama karamar makarantar sakandare babu mai hazakarta a ajinsu. Saboda hakan ne ma ya sa karamar hukumarsu ta ce zata dauki nauyin karatunta har zuwa babbar sakandare. A rayuwar Tafisu tana da burirrika, burin wataran a ce tana da zurfaffen ilmi tana da abun dogaro da kai. Ta so ta zama malamar jinya saboda a gaba ta taimaki mutanen kauyensu da ke fama da lalurori musamman wacce ta shafi haihuwa. To amma me? Burinta bai cika ba, mahaifinta bai yarda da wannan buri ba. Haka aka cire ta a makaranta aka aura ma ta Malam Idi.
Ta kalli rayuwarta a yau, ta dauka a wannan karin za a bar ta ta nemi madogara. Rashin madogarar ne ma ya sa aka raba ta da yaranta. Wata kila da ace tana da karfin iko to sai inda karfin ta ya kare wajen tallafarsu.To amma ita yanzu ba ta da murya, saboda bata da wata madogara ta cin gashin kai na rayuwa don haka ko tayi magana ba za a ji ba. Ko da ta kawo wa mahaifinta uzurinta na son neman ilimi wannan karin ma bai karbu ba. Shekara dai bata rufa ba ta tsinci kan ta a matsayin matar Malam Tanko.
Mijin nata wani irin tsattsauran mutum ne mai takunkumi. Dubo 'ya'yanta ya zame ma ta wani abu mai wahala. Hankalin Tafisu bai kara tashi ba sai da tafiya ta kama su dubiya wani kauye. Zaune take a kujera ana jiran cikar mota sai taji wata murya da ba za ta taba mantawa ba ta ce
" Hajiya za ku sayi gyada marau marau? Hajiya a siya a yi tsaraba"
Wata irin juyowa ta yi idonta yayi caraf akan na ɗiyarta Amina ɗauke da katon faranti na talla a kan ta. Ta dafe kirji ta ce
" Amina dama talla ake dora miki?"
Cikin tsananin murnar ganin uwar ta ce,"Baba Dije ke dora min tun safe tace kuma kar na koma sai na siyar. Mamanmu zan bi ki. Yaushe za ki zo ki tafi da ni?"
Hawaye ke zubo ma ta. A rayuwarta bata taba hango diyarta za ta yi talla ba saboda lalacewar tarbiyya to amma yaya za tayi? Wancan karin ma da tayi yunkurin yin magana akan dan ta Manu iyayenta suka hana wai za ta nuna rashin kara. Har ta koma gida ta rasa mafita. Ta roki maigidan nata ko zata karbo rikon Amina tunda diya mace take mai rauni. Ya nuna mata sam sam shi baya rikon agola. Haka ta hakura. Sau dayawa ta kan yi tunani menene ya sa rikon dan wani kan yi wa mutane wuya? Shin me mace zata taka a rayuwa ta samu ta rayu ta tarbiyyantar da yaranta? Bata samu wannan amsar ba har sai da wani abu ya faru.
Talgen tuwo take a wani yammaci sai ga yaro dan gidan Malam Mudi ya shigo a guje da gare garensa babu ko sallama ya ce,
"Tafisu wai babanmu yace a gaya miki ga Ibrahim can an dawo da shi daga makaranta babur ya kade shi ya karye"
Ai kafin ta tambayi wani ba'asi ya ruga a guje. Jikinta na rawa ta shiga daki ta yafo zani ta bar wa abokiyar zamanta sallahun idan maigidan ya dawo ta gaya masa halin da ake ciki. Irin halin da ta ga Ibrahim a ciki ya sa ta kuka. Ashe yaron yayi tsawon kwana uku ana masa dorin gida babu wanda ya kai shi asibiti. To a nan ne Malam Mudi ya yanke hukunci cewa ta tafi da Ibrahim wajenta ta yi jinyarsa a can sabida wai babu mai kula da shi anan. To hawo dan babur rungume da Ibrahim ta kawo gidanta yana kukan ciwo tana kukan tausayawa rayuwarsu.
A nan tsakar dakinta ta goge masa jiki tsaf ta ma sa shinfida. Daga dawowar maigidan na ta ya daga kodadden labulenta ya gan ta tare da danta ya sauke. Daga nan bai kara shigowa ba. A kwana na 3 ne Malam Tanko ya dube ta yace ta je gida tayi jiyyar yaronta domin ba ya ajiye agola a gidansa. Jiki a sanyaye ta amince.
To a can gidan nasu ma bata sauya zani ba domin iyayenta fushi suka yi da ita. Akan lallai ta mayar da yaro ta koma tayi zaman aure. Batun da bata aminta da shi ba. Idan ta bar yaron wa zai kula da shi? Su ma yara ai suna da hakki mmai yawa akan iyyayensu, musamman yaro kankani irin wannan. Tana so ta kai shi asibiti to amma bata da kudi ba ta da abun dogaro da kai tunda babu wata sanaa ko wani ilimi da za a iya neman aiki da shi. Tana ji tana gani haka kafar sa ta soma warkewa a karkace. Wata biyu ta dauka a gida ta mayar da Ibrahim ba dan ta so ba sai kuma ta shirya ta doshi gidan Malam Tanko. Ko da ta je dakinta an buga masa sabon kwado. Maigidan yana nan kuma bai yi wata wata ba ya shiga daki ya dauko takarda ya mika ma ta yace
" Na ga alama 'ya'yanki sun fi rayuwar aurenki. Don haka ki je na sallame ki"
Ta juya ta tafi ba tare da takamaimai ta san inda za ta je ba. Ta zurfafa cikin tunani.
Kamar mace na bukatar murya kalar muryar da idan ta yi magana za a ji. kamar tana bukatar madogara ta rayuwa da gina kai ko don ta tallafi kan ta da 'ya'yanta. Kamar lokaci yayi da za ta nemo murya. Cikin dayan biyu. Ko ta nemi ilmi zurfaffe wanda za tayi alfahari da kan ta 'ya'yanta da alumma gabadaya su yi alfahari da ita, ko ta nemi sana'a don yaki da talauci da kuma dogaro da kai.
Taku take gabanta wata mararraba ce. Idan ta yi dama zata kai ta tashar garin inda ake hawa mota zuwa garuruwa daban daban idan kuma ta yi hagu zata kai ta kasuwar garin da ke ci a duk ranar alhamis. Har Tafisu ta zo mararrabar bata tantance hanyar da za ta bi ba.
YOU ARE READING
MURYA -Gajeren Labari
Short StoryLabarin zawarcin Tafisu, gwagwarmayarta akan 'ya'yanta