PAGE 9-10

8 0 0
                                    

🌻🌻 MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
             UWAR MIJI CE SILA

TRUE LIFE STORY

STORY AND WRITTEN BY

UMMUSULTAN
            &
GIMBIYA AYSHU💞💞💞

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚

                     LAST FREE PAGE

PAGE 9-10

____________________Toh Mallam kaji abinda ke tafe da mu,yaron nan duk yabi ya susuce akan mace guda daya,gabaki daya baya Jin Kiran kowa sai nata,ko dai ta malake shi ne Mallam?,ta fada fuskar ta dauke da mamaki zuciyar ta na dukan uku-uku.

Wani irin dariyar shakiyanci boka ya yi ya ce"babu zancen malaka a nan,so ne kawai,sannan tana kyautata masa dai-dai gwargwado,yanzu menene kike so a yi akan ita yarinyar da shi yaron?".

"wallahi ni kawai so nake,itama na malaketa kamar yanda muka yiwa abokiyar zaman ta,ina san ya zamto sai abin da mukace musu shi za su yi,yarona kuma Ina son a saka masa kiyayyarta a zuciyarsa,ya ji babu wacce ya tsana kamar qta kuma ya daina zama a gurin ta".

Kallan mamaki malamin ya bita da shi jin abinda ta ce,ya za'ayi kina uwa ki dinga kishi da matar danki,wannan wani kalan fitina ne.

Hade rai ta yi ta ce"ni kamin aikin da nake so ka daina tanbaya ta".

Kar ki damu za'a yi duk abinda kike so amman ki sani duk abinda ya biyo baya kar ki kuskura ki zo gare ni.

"Mallam ni fa in dai bukata ta zata biya,wallahi komai ma ya faru,wannan  matsalar su ce ba tawa ba ehen".

Girgiza kai kawai boka ya yi sannan ya ce"maganar gaskiya shine daga ke har mijin nata babu wanda ya isa ya mata wani abu sabida jinin ta karfi ne da shi sosai,kuma arzikin ta kuke ci kema kin sa..............

Daga mishi hannu kawai ta yi,ba tare daya furta komi ba ya dauki wani magani ya mika mata yana fadin yanzu idan kuka koma gida kisa masa wannan maganin a tea ya sha,wannan kuma a kofar dakin shi za ki zuba mishi ya sallake,ki tabbatar ya sallake shi,da an yi wannan shikenan mun zare masa yarinyar a zuciyarsa,wannan kuma a  abincin safe za'a zuba masa na tsawon kwana uku,da anyi komai dai-dai za'a sami abinda ake so,ku tashi na salame ku,ya fada yana wani kururuwa mai ban tsoro.

Godiya sosai tayi mai tana murna kamar wacce aka ba kyautar kujerar Makkah.

Zaune suke a cikin mota duk sun yi jugum-jugum suna tunanin ta yanda aikin nan zai yiwu,katse shirun Lauratu ta yi ta dubi Mamansu ta ce"Hajiya Ina ganin fa sai mun hada da Aisha,mai yasa kika ce haka?",itama dukkan su ba tafiyar su daya da Ummu..…..............ni fa wallahi duk ganin su na ke tamkar kishiyoyina wallahi,yanda ban yi RAYUWA da kishiya ba  kafin Alhaji ya bar duniya haka zalika suma bazan bari su zauna lafiya ba,duk matan Alhaji sai da nasa ya sake su wallahi,ni kadai na yi masa takaba wallahi bazan iya jarfa bahhh,sabida haka bazan bari wata bazan chan ba ta mallake min yaro ba ina ji ina gani,ni ba irin sakararrun iyayen mijin nan ba ne wallahi,sam bazai yiwu bahhhh.

Nima ba cewa na yi a fada mata gaskiya ba,za muyi amfani da ita ne gurin cinma burin mu,ita kadai ce kawai zata iya mana wannan aikin,kuma kinga gidan su daya tasan time din da ake ajiye mai abinci,gaya mata kawai za mu yi cewa maganin mallakar yaya aka karbar mata danta mallake shi,zan nuna mata ni ce na karbo kuma kema baki sani ba ko ya kika gani?,rike haba kawai ta yi tana girgiza kai alamun gamsuwa.

Dariya Hajiya ta yi ta ce"shiyasa na ke ji da ke Lauratu,kan ki yana ja sosai,wannan shawarar taki ta yi,hakan ko za'ayi ba tare da jayayyah bahh"........murmushin Jin dadi Lauratu ta yi jin an yabe ta,dai-dai lokacin suka iso gida,a sakar gida suk tarar da Anty Aisha,ba karamin farin ciki ya kama su ba,nan suka baje kolin abubuwan da suka karbo suna harhadawa dan tun daga yau suke so a fara aikin,sabida tsabar murna har kasa kulle bakin ta Aisha ta yi.

Murmushin mugunta Hajiya ta yi ta ce"zaki ci ubanki ne yarinyah".

Sadiya gashi ki zuba a bakin kofar nan kafin na Kira Yayanku ya zo,ta fada tana mika mata laidan maganin,dauke kai ta yi kaman bata ji mai aka ce bah.

"Aunty Sadiya Mama na miki magana fah"...........

Kina tunanin ba ta ji bane,sarai ta ji ni,iskanci ne kawai,kuma wallahi zan yi maganin ki,za ki tashi ki karba ko sai na ci kaniyar ki.

Mikewa ta yi tana kunkuni ta ce"wallahi ni dai ba za'a yi shirka da ni ba,musamman ma  akan Yaya,haba fisabilillahi,Mama mai Yaya ya tare muku ne waiiii.........duk wani nauyin ku daya dace ace ya dauke yana yi,toh fisabilillahi mai kuma kuke so ya yi,bashi kadai ba ne danki balle na ce ai saboda shi kadai ne ya sa kike haka?,mai yasa bakya yiwa sauran mazan sai shi kadai kika sawa idanu,kun hana shi Jin dadi yanda ya kamata,kullum cikin zuga shi kuke a kan matansa,riban meh zaku samu ne dan Allah,idan bai ji dadin matansa na sunnah ba dana waje kuke son ya ji dadi,wallahi ku ji tsoron Allah,hakkinsa dana matansa ma kawai ya isheku,gashi yanzu Kuna son sake kirkiran wata fitina,wallahi ba ruwana kuma babu hannuna a duk wani abinda zai biyo baya,kuma ko da wasa kar a kirani shaid".....................

Saukar marin data ji ne a fuskar ta yasa ta yin shiru ba tare data shirya bah............,saurin dafe kuncinta ta yi tana kallon Hajiya da ta mareta,hawaye takaici ne ya wanke mata fuska,cikin tsanani fushi da kumfar baki Hajiya ta ce"wani kalan maganar banza kike yi Sadiya,i ko mai zai faru sai mun aikata wannan aikin,sannan kuma ko da wasa kika ce za ki sanarwa Yayanku to ki tabbatar daga ranar sai dai ki chanza wata Uwar,babu ni babu keh wallahi muddin kika fada,zan cire hannuna akan lamarin ki gabaki daya".

"Ni bazan hana ku ba kuma bazan fada ba,sai dai bazan taba baku goyon baya ba a komi,sabida haka karma ku sakani cikin duk wani lamari daya shafi wannan",daukar littafinta ta yi ta fice daga dakin tana kuka mai ban tausayi.

Tafa hannu Lauratu ta yi ta ce"lallai ma Anty Sadiya,itama an gama da ita".

Rabu da ita za mu hadu,ta fada tare da daukan wayar ta ta kira number shi,fitowar shi daga wanka kenan ya ji wayan shi na ringing,ba bata lokaci ya daga tare da gaishe ta,ba tare data amsa gaisuwar ba ta ce"ni dai ka yi maza kazo ka same ni a gida,ni in so samu nema ka yi tsuntsuwa".

Da toh Hajiya kawai ya amsa ya kashe wayar,bayan ta kashe ta dubi Lauratu da ke zaune a gefe ta ce"yana zuwa yanzu,ki yi Maza ki hada masa abin sha kafin ya karaso,amman kar ki saka maganin sai za'a bashi,yanzun dai tashi ki hada ki saka a fridge,kuma ki tabbatar kin yi shi da kyau,ina fatan kin jini......................................................


Littafi ya koma normal price,ku biya kudin ku ta wannan account number

Normal price 500 complete 1000.

Account number:2245462427
Account name: Aisha maaruf
Bank name:UBA
Evidence of payment:08076119294.

COMMENT

VOT

SHARE

BY GIMBIYA AYSHU💞💞💞 & UMMUSULTAN.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 07, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(UWAR MIJI CE SILA) BOOK 2Where stories live. Discover now