TUN RAN GINI! 5

1 0 0
                                    

🎑🎑🎑🎑🎑🎑
   *TUN RAN GINI*
   *(RAN ZANE)*
  🎑🎑🎑🎑🎑🎑
*EPISODE 5️⃣*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

_________ Talatu! talatu! kai jama'a wai gidan nan anya akwai wanda ya fara fitowa taka kuwa? kayi kira! kayi kira tamkar duk sun mace taka.

INNO magana kike yi ne? INNO ta d'ago kai ta kalleta cikeda takaici kafin tace A'a talatuwa ba magana nake ba, kwarmatoto nake ina lissafa sauran kwanakin daya rage miki kibar gidan nan!

Jiki na bari Talatu tace afuwan INNO bana kusa ne, yanzu na dawo daga sashen Hajiyar Siya na kai mata ragowan kayan da kikace a mayar mata.

INNO ta gyara zama tareda sauke k'afafunta duka k'asa tana kallon talatuwa kallon irin na tuhuma, sai kuma ta nuna ta yatsa, ke talatuwa kiji tsoron Allah, da yaushe na baki umarnin maida wani kaya a gidan nan.

Talatuwa ta hau zazzare idanu tace kar dai har kin manta yanda kukayi da SIYA jiya data dawo, har take baki labarin kulawar data samu awajen SA'AD bayan kwana datayi awajen sa, da kuma tarin kayan datazo tayi ya rabawa saboda murnan datakeyi.

INNO ta hau zazzare ido kafin ta hau salati tana tafa hannu, amma dai talatuwa kin cika y'ar b'akin ciki, yanzu daga d'an burarin danayi akan wannan kaya har kin kwasa kin mayar dashi saboda k'ullin ciki gareki, to wallahi sai kin dawo min da abata

Talatuwa ta cigaba sa zare manyan idanuwanta tunowa da irin rashin mutuncin dataje ta shuka yanzu a sashen HAJIYA HANSATU wai ita ala dole INNO ce ta aikota.

Tayi k'asa da murya tana kakkashe ido amma INNO kamar ba girman ki bane canza magana, mu bar musu kayan kawai tunda waya sani ma ko wani wajen SIYA tabi ta samo kayan shine zatazo tana k'aryayyaki akai!

INNO ta d'an yi shiru tana mamula baki kamar dai maganar ta talatuwa taso tayi tasiri a cikin zuciyarta.

Ta yarfa hannu tace kuma fa maganar ki akwai k'amshin gaskiya aciki, ni dama tun da yarinyar ta dawo take rawar k'afa jikina ke bani wani abin taje ta k'ullo, zatazo tayiwa SA'ADU sharri, yaron kirki ta b'ata masa suna ya rasa matar aure!

Yanzun ma ay ya rasa! talatuwa ta fad'i can cikin mak'oshi, INNO ta d'ago ta kalleta tace me kuma kike cewa? nan da nan talatuwa tayi yak'e tace wai nace ko zan koma na karb'o kayan!

INNO tayi k'wafa, kinga zo ki kaini naje da kaina, tun wuri ayita ta k'are tsakani na da HANSATU tun kafin ta had'a baki da wannan bankad'add'iyar y'ar tata su b'atawa SA'ADU suna a idon duniya.

Talatuwa tace Yawwa INNO ashe kema kin gane manufarsu, ta janyo keken INNO tana cigaba da zuge INNOn yanda tasaba a koyaushe.

Wai wannan wani irin baccin lalaci kike yi ne tun jiya da kika dawo gidan nan SIYA banga abin kirki da kika tsinana ba, sai kalan kwanciya kamar mai k'aramin ciki!

Sai kuma ta zaro idanu waje sosai tana mai yarda lip balm dake hannunta, badai cikin kikayi ba?

Siya dake dad'a gyara kwanciya tace haba mum meye kuma da wani ciki sai kace wata local, ay idan kin ganni da ciki to ba na kowa bane sai na yaya SA'AD!

Ahir d'inki mai tsamin baki! aniyar kura tabi shi, dama sharrin da kuke kan k'ullawa SA'ADU kenan!

Hajiya HANSATU dako d'ar ba tayi ba da zuwan na INNO ballantana ta nuna ta damu da maganar INNO ta tashi tsaye da kyakkyawan murmushi a saman fuskarta tace Hajiya INNO ce yau da kanta a y'ar akulkin mu!

INNO ta wani b'ata rai tana jin kanta na k'ato, dama haka takeso ya kasance ana girmamata yanda yakamata, to fa za'ayi zaman lafiya.

Ta kalli SIYA da ko motsawa ba tayi ba ballantana ta tashi tayiwa INNOn gaisuwa, ita kuma wannan data mik'e kamar an shanya faranti a rana fa?

TUN RAN GINI! Where stories live. Discover now