TUN RAN GINI! 7

1 0 0
                                    

🎑🎑🎑🎑🎑🎑
   *TUN RAN GINI*
  *(RAN ZANE!)*
  🎑🎑🎑🎑🎑🎑
*EPISODE 7️⃣*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

___________ Misalin k'arfe goma da mintuna na safe kenan, kamar ko yaushe sai takai shad'aya ko fiye da hakan ma take barin gado, abinka da y'an gayu akwai mai yi musu komai.

Wayar ta dake gefenta na hagu a saman drawer ne yake ta vibrating, tun tana kashewa har ta gaji ta tashi tana yamutsa fuska tareda tsaki tana kallon agogon dake kallon saitin inda take kwance.

Ta sanya hannu akan wayar tana fad'in wani d'an bakin cikin ne zai kirani this early hour! y'ar hutawar ma baza a barka kayi ba, ta rufe baki saboda hammar dayazo mata, daidai lokacin wani kiran ya kuma shigowa, ba tareda ta kalla ba ta manna a kunne tana fad'in dama nasan kai kad'ai ne fitinanne mai hanani rawan gaban hantsi, kai fa DODO ka cika fitina.

Da serious tone d'insa yace matsala to dake Hajjaju rashin fahimta da gajen hak'uri, ay kinsan idan kika ji kira to tasamu ne ko an shiga wata sabgar mai wuyan warwarowa.

Ta tab'e baki  naji meye kuma ya samu ko zai samu banson jin mummunar labari.

Yayi k'asa da murya wanda hakan yasa banji abinda ya fad'a mata ba, sai ganinta nayi tana dariya, kafin tace aikin ka na kyau DODO! yanzu abinda nake so da kai banason asamu wani akasi daga baya, ka tabbatar ka cikita aikinka ni kuma zan cika maka aljihu, bana failure, sannan asa ido sosai akan cctv da muka ajiye kar ayi sakaci ya karkace a samu matsala.

An gama Hajiya kawai naji ya fad'i sannan ya kashe wayar, itama ta ajiye wayan tana murmushi, daidai lokacin SANATA ya turo k'ofar d'akin a hankali.

I thought har yanzu kina bacci, seems that wani kyakkyawan labarin kika samu, ta d'ago kai ta kalleshi tana dad'a yalwata fara'ar fuskarta don ganin kyan dayayi cikin shigar suit tamkar matashi mai 35.

Ta kamo hannun shi ta taya zama kusa da ita tana fad'in SANATA na yau wannan wankar amma tawa ce koh?

Yayi murmushi yana kallonta sai kuma ya kalli agogon hannunsa yace muna da meeting k'arfe shad'aya kinga har na kusa nayi latti, bari na tafi kafin ba baiwa media wata damar soki burutsun su na yau da kullum.

Yayi mata peck ya nufi k'ofa, ba tace komai ba har ya fita, kamar ranta bai so fitar tashi ba, ta gyara zama tana kallon hotonsu su biyu dake ajiye jikin bedside, ta rintse ido na kusan mintuna kafin ta bud'e, har yanzu     kinada sauran aiki, GWARAM bai shiga hannu yanda kikeso ba, acikin idonsa har yanzu tana hango wani abu dayake b'oye mata, yazama dole ta tashi tsaye, idan ba haka ba, wankin hula zai kaita dare.

*************
Wai ni kam kwana biyu Mummy banjin d'uriyar YAYA SA'AD gashi idan na kira number sa bata tafiya, Mummy please ko kinsan wani abu ki fad'a min, zuciyata ta kasa samun nutsuwa.

Hajiya HANSATU dake k'irga wasu kud'ad'e ta tab'e baki ba tareda ta juyo ba tace ina kuwa zan sani, kema kinsan dadynki bayason ayi maganar auren ku keda SA'AD ballantana naji wata magana daga bakin shi.

Shamsiyyah tayi tsaki tana turo baki gaba cikin y'ar fushi, dama nasani ay daddy ba k'aunata yake ba, i don't know why yake kin jinin had'ina da yaya SA'AD, and he would be claiming he loves him more than anything, love him my foot! ta k'arashe tana mai wurgi da comb d'in dake hannunta wanda take taje kai.

Hajiya HANSATU ta janye k'afa saboda yanda comb d'in ya kusa samunta, kefa SIYA na lura wani lokacin bakida hankali, SIYA ta mik'e tsaye tana cewa eh say it am crazy na yarda idan akan yaya SA'AD ne call me a psycho i don't give a damn.

Ta Juya ta nufi k'ofa tana fad'in bari naje na matsi tsohuwar nan, nasan ita tanada masaniya ay!

Ke talatu! wai bazaki zo ki cire min wannan k'unzugun bane sai ya jeme ni na kasa tafiya. taci gaba da magana ita kad'ai, nidai a gidan nan babu mai daraja ni, daga yayan har jikokin kamar sun lashi takashi duk idonsu a bushe an deb'e albarkan cikin ta.

TUN RAN GINI! Where stories live. Discover now