🎑🎑🎑🎑🎑🎑
*TUN RAN GINI*
*(RAN ZANE)*
🎑🎑🎑🎑🎑🎑
*EPISODE 🔟*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*____________ Tsaye yake gaban wata corridor wata k'atuwar gini mai hawa kusan goma a inda yake nashi d'akin yana hawa kusan na shida, iskar dake kad'awa a wannan yammacin na d'aya daga cikin abinda yake sashi nishad'i acikin wannan wajen, wacce hakan ke k'ara masa karsashi da cigaba da k'aunar zama a wannan k'asar kamar yanda yake jin wata b'ari daga cikin zuciyarsa na ayyana masa.
Saidai ya rasa meyasa duk da hakan acikin y'an kwanakin nan yake jin wani urge na son komawa gida, yayi duk tunanin da shawaran da zaiyi ya kasa gano abinda zaisa shi komawa yanzu tunda bashi da wani mai jiransa acan, sannan yana hutun aiki, gashi meeting d'in dayazo tun last week ya gama komai.
Ya sipping coffee dake hannunshi yana dad'a k'arewa environment d'in kallo, komai tsaf tsaf kamar babu wani bil'adama dake rayuwa a wannan area. duk kuwa da cewa the place is always busy, mutane ne masu launika, siffofi da al'adu daban-daban ke shige da fice awajen.
Daga shi sai gajeran wando, wanda bata gama isa guiwarsa ba, wacce ta kasance d'aya daga cikin shigar daya fi so idan yana gida less busy, either a Nigeria ko anan Malaysia.
Bluetooth d'in dake kunnensa naga ya tab'a, na wasu dak'iku yana kallo waje d'aya ba tareda ya furta ko kalma d'aya ba, k'arshe naga ya kashe da yatsa.
Cigaba yayi da kurb'an coffee sa ba tareda ya motsa daga inda yake tsaye ba, saidai ga mai tsananin kula zai gano b'oyayyiyar b'acin rai kwance asaman fuskarsa.
Tsawon mintuna biyar yana tsaye awajen kafin daga bisani ya koma d'akin wacce ya baiwa baya, kyakkyawan parlour ne da akayi decorating d'insa da ja da farin kyalle komai ba ciki na nan tsaf - tsaf tamkar babu d'an mutum aciki.
Wannan kofin ya ajiye a gefen wata coffee machine, ta nufi bathroom wacce ke can ta gefe, mintunan da basu wuce goma ba yayi aciki sai gashi ya fito daga shi sai y'ar k'aramar boxers da towel dayake amfani dashi wajen goge ruwa akan sa.
Wayarsa ce ta kuma k'ara wannan karon kana iya jin ringing d'in wayar saboda ya kashe bluetooth d'in.
Kallo d'aya yayi ma wayar naga ya d'auke kai yaci gaba da abinda yake yi, saida ya gama shafe shafensa kamar wani mace. ya shirya cikin shigar k'ananun kaya, wato blue jeans da white shirt, wata fatar hula irinta sanyi data rufe masa har kunne yasaka kafin, ya d'auko wata farin kambas da tayi sloppy yasaka.
Keys d'in sa dake ajiye akan mirror ya d'auka tareda wayarsa ya tura a aljihu, lifter naga ya hau wacce cikin mintuna kad'an ta sauke sa k'asa, fita yayi daga wajen kafin naga ya tari wani kyakkyawan k'aramar mota, ashe cab ne.
Banji me yace wa driver ba, sunyi tafiya na wajen mintuna talatin kafin naga an shigar dashi wani k'atuwar waje d'aya sha k'awa da k'yale-k'yale.
Nan ma saida ya hau lifter ta kai shi can sama, a inda naga ya shiga wani babban shopping mall wanda ya k'awatu iya k'awatuwa, yana shiga wasu k'yawawan mata biyu masu shiga iri d'aya sunyi rolling da farin mayafi suka nufo shi da fara'arsu.
Nan da nan yayi kicin-kicin da fuska kai kace cinye shi zasuyi, saidai kamar hakan da yayi bai damesu ba, don tuni suka cigaba da binshi suna magana cikin harshen turanci wanda daga ji kasan bawai ya wani zauna musu sosai bane a baki.
Wani waje naga yaje direct yayi magana da wata mata kafin ya had'e k'afafu ya zauna yana danne- danne acikin wayarsa. tsawon mintuna goma kafin naga wad'annan matan sun kawo masa wasu jaka guda hud'u kowanne cike yake da kaya.
Ya ciro wani card ya mik'a musu. har mota suka kai masa kayan, wannan karon lumshe idanu yayi kamar mai bacci, a yayinda yake jin kanshi na d'aukan chaji sosai yake jinsa with mixed emotions wanda ya rasa dalilin hakan.
YOU ARE READING
TUN RAN GINI!
RandomKo kunsan abinda ake kirada k'addara wacce hausawa ke cewa tun RAN GINI! TUN RAN ZANE! Zanen k'addara ta zanu a rayuwar ASMY! wanda yayi dogon layi tattare da siffofi da dama, saboda akasi da aka samu daga foundation d'inta. ginin rayuwar ASMY dai a...