TUN RAN GINI! 8

1 0 0
                                    

🎑🎑🎑🎑🎑🎑
    *TUN RAN GINI*
  *(RAN ZANE)*
🎑🎑🎑🎑🎑🎑
*EPISODE 8️⃣*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

_________ A yau ne take cika sati guda acikin gidan kuje prison, wanda a wad'annan kwanakin datayi acikinsu yazame mata mafi munin ranakun data gani a tsawon rayuwarta.

Duk da cewa a baya tasha samun k'alubale da suka d'orewa wanda a yanzu take gani, amma na yanzu yasha bambam dana da, wanda a yanzu take jin tamkar wani sashe na rayuwar ta ake figa saboda tsananin zafi da ciwon datake ciki, wanda ya faru a sanadiyyar tunanin d'an d'anta ASLAM wanda ta kasa kwantar da hankalinta saboda tunanin halin da yake ciki na rashinta kusa dashi wanda tun tasowarshi ita yasani da ita yasaba, ita kad'ai ne dangin shi na kusa da nesa, to gashi yanzu k'addara na neman rabasu, ko wani hali zai shiga idan ta kasance sai tayi wannan shekarun acikin wannan gidan? waye zai rik'e mata shi tsakani da Allah?

Wannan tunanin yasa ta kwana tana kuka, RAMLAT na kallonta ta shareta don ta lallab'ata har ta gaji.

Kwananta biyu tana kwance Raf, don zazzab'i ne mai zafi ya rufeta, har saida aka nemo medical care na wajen aka dubata.

Sati guda kenan yanzu ta warsak'e amma kuma tayi wani wawan rama, dama can ba k'iba gareta ba, sai tazama wata one zero kamar ka hureta ta fad'i, ta kuma zama silent maganar kirki batayi daga uhmm sai uhmm, RAMLAT dake ta iya k'ok'arinta wajen cheering d'inta har k'awaye ta samo mata acikin inmates d'in don su dinga tayata hira a fad'ar ta wai ita bata iya hiran y'an jarida ba sai na y'an tab'are 😀

Saidai all efforts in vain, ASMY dai kullum sake zama introvert take.

Yau suna zaune a wajen cin abincinsu itada RAMLAT na facing juna, yayinda sauran k'awayen RAMLAT d'in ke zagaye a gefensu, kowacce roban abincinta na gabanta, wasu naci wasu kuma hiransu suke shiyasa ko tab'a abincin basuyi ba. ita kam bata d'aya daga ciki hankalin ta ya tafi ne ga wani rubutu da akayi da farin chalk a jikin bangon wajen

"NEVER GIVE UP" 

Tabbas wannan kalma ya rinjayi tunanin ta, rather fannoni da dama wanda a yanzu ta fara tunanin mafuta ne agareta, wanda acikin kwanakin da suka wuce ta riga da ta soma fidda rai daga duk wani jin dad'in duniya.

Tayi wani murmushi kana ta soma cin abincin da tuntuni ta tisa shi gaba tana juyawa, RAMLAT da tuntuni ke naxarinta ta kad'a kai kawai itama ta cigaba da cin nata batareda tace uffan ba.
ASMY ce ta fara tashi awajen, kowa yabita da kallo saboda yanda ta kasa barin fara'ar dake kan fuskarta ya gushe.

Wajen da wasu mata ke motsa jiki ta nufa, tana tafe tana dad'a baiwa kanta assurance d'in zata iya, she would surely survive, cos only the weak are being bullied, don haka dole tazama strong yanda zata iya defending any situation dazai zo mata.

Saidai kallo d'aya sukayi mata taji cikinta ya d'uri ruwa, su d'in matane masu wani manyan k'ira, ko ta ina acike yake ajikinsu, duk da cewa ba suyi kama da masu yawan shekaru ba, amma jikinsu ya b'oye yarintarsu, hatta asalin k'iransu na y'ay'a mata ya fara fading saboda yanda suke ko ina a murde.

Idanunsu kuwa a kallo d'aya zai baka amsar irin k'wayar da suke kwasa wanda ke k'ara b'oye musu sirrika da yawa a matsayinsu na y'ay'a mata.

Almost 30 seconds tana k'are musu kallo, while k'irjinta na bugun 360° a second guda.

Har saida taji ta fara tunanin juyawa ta koma inda rai fito, sai ta kuma tuno da kalmar dake motivating d'inta a yanzu "NEVER GIVE UP"

Exhaling wani nannauyan numfashi, kafin ta k'ara taku biyu kusa dasu trying so hard to control her self.

May i join? tayi maganar cikin wani irin k'arfin hali da batasan daga ina yazo ba. d'aya daga cikin su ta ajiye wani k'aramin weight lift dake hannunta na dama, ta karkad'e jiki ta tashi tsaye tana dad'a k'arewa ASMY kallo tamkar mai son ganin wani abu a jikinta.

TUN RAN GINI! Where stories live. Discover now