🎑🎑🎑🎑🎑🎑
*TUN RAN GINI*
*(RAN ZANE)*
🎑🎑🎑🎑✍️🎑
*EPISODE 9️⃣*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*_______________ Kwatanta miki halin dana shiga bayan rasuwar Hajiyar mu Allah ne kad'ai yasani na kusa zarewa, tun daga ranar rasuwar har akayi uku sai na yini ina sambatu da bige bige tamkar nasamu tab'in hankali.
Mutuwar Hajiya ta tab'a ni sosai, especially danake ganin kamar duk nice na jawo hakan. bayan anyi sadakar bakwai mutane sun watse aunty maimoon tace zata tafi dani ni kuwa nace babu inda zanje ina nan gidan ina tuno da Hajiya ta, ba zanje inda zan mance da ita ba.
Babu irin dad'in bakin da ba'ayi mini ba amma nayi fir naki, har abbanmu saida yayi min jan ido, amma a banza tunda ni yanzu ma ba mutuncinsa nake gani ba, ji nayi ma na tsane shi.
Bayan sati biyu na koma zuwa makaranta saboda jarabawar daza muyi, ina komawa kuwa na d'inke da BIBA wacce ke kawo min duk wani nau'in kayan mayen danake so, a wannan lokacin tunani na wannan abubuwan sune kad'ai maganin matsalata, cikin lokaci kad'an nazama wata guruwa a harkan shaye shaye komai na d'abiuna saida ya canza.
Canjin dayayi sanadin rugujewar rayuwata da komai na.
Bana mantawa kamar kullum nida BIBA da ZAFF sai abokan mu Sale da jabir mun tafi yawon shak'atawar mu yanda muka saba duk weekend zamuyi zuga muje party muyu shaye shayenmu yanda muke so, tamkar duniyar ta tsaya ne kawai akanmu.
Yau kam party tamu ta daban ce saboda gayyatar ta manya ce wato d'an gidan general ne yake bikin birthday sa so duk wani d'an mai fad'a aji yana wajen.
Taro yayi taro waje ya cika masu rawa nayi, masu bad'ala nayi, masu ciye ciye nayi da kuma y'an tawagar mu nasu shaye shaye duk mun baje kolin mu babu abinda bama sha, munyi nak'is duk mun bugu
Haka kawai yau naji ina buk'atar yin rawa abinda ban tab'a damuwar yi ba duk shiga na irin wajen, ina shiga kuwa fili ya d'au sowa, nan da nan attention d'in maza da yawa ya dawo kaina, kinsanni d'in sai badai kyau ba.
Kaina ya dad'a kumbura ina jina wata Eh yane, saidai kan na ankare naji an damk'o min kwankwaso ana wani shinshina ni. nayi ta maza na ingiza shi inajin wani irin b'acin rai, saboda duk iskancina da ake gani ban yadda na zubda mutuncina ba.
Tuni na rufeshi da masifa ina layi dama gashi na bugu nayita zagin shi, wanda hakan ya tab'a ego d'insa, ban ankare ba naji saukar mari a gefen kumatu na, nayi baya taga taga kamar zan fad'i na rik'e wajen ina kallon shi da jajayen idanuna.
Nan take nima naji zuciya tajani kawai kan ya ankare na zari k'walban Hennessy da aka sha na saiti daidai k'eyarsa na rotsa masa. ya juyo a wahalce yana kallona kafin na ankare ya kuma shak'o min wuya da mugun k'arfi har saida na fara wani irin tari numfashi na yana katsewa. ganin hakan yasa BIBA da itama take ganin goma a dubu ta kuma rotsa masa gindin takalmin ta mai tsini.
Ay kuwa ya wani k'ara ya sakeni na zube k'asa a galabaice, shi kuwa yana fad'uwa naji wasu suna cewa shikenan sun kashe shi, Ridwan ya mutu.
Duk da halin buguwa da muke ciki saida tsoro ya kamamu sosai, sale da Sadiq dake maza mata ne sunfi mu tsorota duk suka bi ribibi suka gudu, BIBA kam na k'ok'arin d'agani tsaye don k'afana yayi sanyi na kasa tashi.
Kamar daga sama muka ji jiniyar y'an sanda, hakan ya kuma rikitamu sosai, saidai it's too late har security sun gama zagaye wajen tsananin tsoro da tsautsayi yasa zaff ta fara gudu yayinda security ke ta ce mata hands up amma tak'i saurara, sai kawai k'aran harbi mukaji.
Flat a take sukayi wa zaff bullet a k'irji ko motsi bata kuma yi ba, nan take muka fashe da wani irin kuka nida BIBA.
Hannayen mu asama har suka k'araso inda muke suka saka mana handscuff suka tisa k'eyarmu zuwa cell.
YOU ARE READING
TUN RAN GINI!
De TodoKo kunsan abinda ake kirada k'addara wacce hausawa ke cewa tun RAN GINI! TUN RAN ZANE! Zanen k'addara ta zanu a rayuwar ASMY! wanda yayi dogon layi tattare da siffofi da dama, saboda akasi da aka samu daga foundation d'inta. ginin rayuwar ASMY dai a...