Feelings

189 4 0
                                    

7

*...........Sa'eed.........*
Feelings

Shekaru bakwai kenan da zuwa na Maiduguri. Wannan gari mai Albarka ya zame mun tamkar asalina. Ina jin daɗin garin, ina kuma son garin sosai. A shekaru bakwai ɗin nan sau uku na je ƙauyen mu, na farko lokacin da Inna ta ta rasu shekara ɗaya bayan na zo Maiduguri mu ka je ta'aziya tareda Jijiɗo. Na biyu mu ka je da Baffa Manu lokacin da mahaifiyar sa ta rasu, sai na uku wanda ya zamo min wani tarihi mai muhimmanci a rayuwa ta.

Ina shekara shatakwas, lokacin ina aji biyar a sakandare mijin babbar 'yar Jijiɗo ya rasu, lokacin ana hutu sai ya zama na tare mu ka tafi.
Ban sanar da Aaliyah ba saboda sun tafi Lagos bikin wata cousin ɗin su.

Su na dawowa daga tafiyar su, ko cikin gida ba ta shiga ba ta yiwo wajen mu da gudu. Kwana biyar kenan ba sa gida.
Da ta zo ta samu ɓangaren mu a garƙame da kwaɗo. Ta shiga wajen su Mama John ta tambayi ina mu ka je. Mama John ta ce mun tafi ƙauye an ma na rasuwa.

Daga wajen ta fara kuka ta shige gida da kuka. Kai tsaye ta je ta fara haɗa kayanta, da ta gama ta fito da jaka ta samu Amma a ɗaki tana baccin huce gajiya.

Yadda ta ke ƙwala sunan ta ya sa tun kafin ta shigo ɗakin Amma ta farka.

" Aaliyah ki na so na zane ki ko? Yaushe mu ka dawo za ki fara damuna da shirmen ki"

Cikin kuka ta ce "Amma wai Hamma da Jiji sun tafi ƙauye, zan bi su"

Takaici ya sa Amma ta ce " Allah ya kiyaye"

Aaliyah ta fito da jaka ta nufi gate. Ma su gadi sun tafi Sallah, Ɗaya Maigadin da baya sallah kuwa ya kwanta a kan benchi yana hutawa bacci ya tafi da shi.  Ta je ta buɗe ƙaramar ƙofa ta fita.
Taxi ɗin da ta tsare tace da shi ƙauyen Durum zai kai ta. Ganin kayan jikin ta ya san 'yar gidan manya ce. Ƙarancin shekarunta da rashin wayo da ya bayyana a fuskar ta ya sa ya gane ƙila guduwa za ta yi. Ya ce ta shigo.
Su na tafiya ya fara ma ta tambayoyi akan mi za ta je yi a Durum, shi da ko sunan ƙauyen ma bai taɓa ji ba sai lokacin.

"Zan je ganin Hamma da Jiji ne"

"Ayya 'yan mata, Ashe ki na son Hamma da Jijin na kin nan sosai. Amma ban ga kin ɗauka mu su tsaraba ba, na ga kamar jakar kaya ne a hannun ki"

Aaliyah ta dafe kai "oops ai na manta. Mu koma gida sai na ɗauko mu su tsaraban Lagos"

Dama abinda mai taxi ɗin ke so kenan.

Lokacin da ta ce gidan Alhaji Badamasi Bulama zai kai ta sai da yai mamaki.

A ƙofar gate  ɗin gidan ya tsaya ta fita da gudu ta fara buga gate ɗin. Mr Francis ya leƙo ta ɗan ƙaramar ƙofa da akayi ajikin gate ɗin sai ya ga Aaliyah.  Da sauri ya buɗe ma ta ƙaramar ƙofa ta shigo, yana ma ta magana ma ita kan ko ajikin ta tsarabar Hamma da Jiji ne a gaban ta.
Lokacin da ta fita daga taxi yai dai-dai da karyowar kwanar motar Alhaji Badamasi. Tsayawa su ka yi dreban sa ya fita ya je ya kirawo mai taxi ɗin. Mai taxi ya zo jikin window jikin sa na rawa duk da kuwa shi niyyar sa da Aaliyah ta shiga sai ya miƙawa ma su gadi jakarta ya kuma gaya mu su abin da ta ke niyyar yi. Sai dai abinka da ma su kuɗi yanzu sai a fassaraka da wani manufar.

Bayan yai wa Alhaji Badamasi bayani Alhaji ya fito da kuɗi ya bashi sannan ya ce dreban sa ya ɗauko jakar Aaliyah...

Aaliyah tana chan tana haɗa tsaraba ba ta san mi ake ciki ba sai da ta fito falon su ta ga Alhaji zaune ga jakarta a falon.

"Kiramin Amman ki"

"Baba zan je wajen Hamma da.."

"Je ki kiramin ita na ce" ya daka ma ta tsawa.

Ta juya da gudu ta tafi. Lokacin da Amma ta fito faɗa ya fara ma ta akan tana ina Aaliyah ta haɗa kaya har ta fita daga gidan nan wai za ta je ƙauye ba ta sani ba.

Tsohuwar Soyayya (Best Hausa love story)Where stories live. Discover now