Confession

187 5 0
                                    

8

*.............Aaliyah.............*
Confession

Lokacin da Hamma Sa'eed ya tafi Cambridge, sai ya zamo kamar ya tafi da rabin jiki na ne sauran rabin kuma yana Maiduguri. Duk su Jiji sun ɗauka rashin ganin Hamma  zai sa na dena damuwa da shi amma abin bai zamo haka ba. Kullum na dawo daga makaranta ɗakin sa na ke tarewa wani lokaci na yi ta kuka, wani lokaci  na zauna na wuni ina kallon hotunan sa. Abin ta kai har kwana na ke a ɗakin sa duk da kuwa Jiji ta hana ni amma na ƙi ji. Itakam Amma ta yi faɗan har ta gaji ta sallama ni.
Lokacin da Yaya na Bukar ya tafi Oxford karatu mu kan yi waya da shi lokaci zuwa lokaci, amma Hamma tun ina irga kwanaki har na fara irga watanni ƙarshen shekara na baza ido ko zan ga Hamma kamar yadda Ya Bukar kai zuwa duk ƙarshen shekara amma ba Hamma ba dalilin sa.
Safiyar wata Lahdi ina karatu a ɗakin Hamma, Jiji ta shigo da murnan ta. Ta miƙamin wani envelope mai ɗan girma ta ce yanzu Baffa Manu ya kawo, an aiko daga post office wai na karanta mu su daga Sa'eed ne. Ai da sauri na farke envelope ɗin na fiddo da abinda ke ciki. Akwai wani envelope madaidaici wanda  ke ɗauke da sunana a jiki.
Ban san lokacin da na kissing envelope ɗin ba ina shaƙar ƙanshin jiki.  A gurguje na karanta ma ta abinda ya rubuto mu su. Gaisuwa ne da kuma bayanin yadda za su rinƙa amsan kuɗin da zai dinga turowa. Ina gama karanta ma ta na yi waje da gudu. Ban tsaya sauraron wasu tambayoyin ta ba balle na amsa su. Ina zuwa na faɗa kan gado na ina maida numfashi. Finally Hamma Sa'eed ya turomin saƙo. Kenan bai manta da ni ba, kamar yadda ni ma kullum ya ke rai na. Sai da na samu na nitsu sannan na buɗe envelope ɗin na fiddo da takardu goma shabiyu da ke ciki. Na fara karantawa ɗaya bayan ɗaya saboda ya sa number a jiki. Taƙaitattun bayanai ne akan yadda shekara ɗayan nan ta kasance ma sa a Cambridge ba tareda ni ko su Jiji ba. Duk inda ya rubuta *i miss you Aaliyah* sai na bi wajen da kiss. Haka na sa letters ɗin nan a gaba ina karantasu ina sake maimaitawa...

Shekara na biyu ya zo min da sauƙi saboda mun yi musayar letters har sau shida. A wannan shekara na yi jarrabawar Waec ina aji biyar. Babban abinda ya fi sa ni farin ciki da kammala jarrabawar nan bai fi tunanin tafiya Cambridge da zan yi ba. Ina tunanin zan kasance tareda Hamma na.

Sanah Oxford ta zaɓa ni kuma na zaɓi Cambridge duk da ma dai Baba ya so mu tafi waje ɗaya tunda tare mu ka taso amma kowa da ra'ayin sa. Ita Sanah tuntuni Oxford ta ke son zuwa ni kuma tun lokacin da Hamma ya samu scholarship a Cambridge na sa wa raina Cambridge zan je.

Abu ne na 'ya'yan ma su kuɗi. Ko ina za ka je indai ana zuwa to ba matsala ba ce a wajen ma su arziƙi. Baba ya sa aka fara ma na shirye-shiryen tafiya. Ni excitement ɗi na ba na makarantar da zan je bane sai dan ganin Hamma da zan yi after 2yrs da ba ma tare.

Cikin ƙanƙanin lokaci aka  sama mana admission aka arranging ma na komai hatta wajen da zan zauna an shirya komai. Ranan tafiya ta zo, Baba da kan sa ya raka ni airport abunka da shalele, da ke ba tare za mu tafi da Sanah ba ita sai nan da sati uku.

Ban sha wahalar komai ba saboda an riga an shirya wanda zai ɗauke ni tundaga airport ya kaini gidan da zauna. Gidan flat ne ɗaki ɗaya da falo sai kitchen. Ba abinda ke raina illa na ga Hamma, ko ya ya ƙara girma yanzu oho.
Mun riga mun tsara inda za mu haɗu a cikin makaranta idan na zo. Ba tareda hutawa ba na ce da wanda ya kawoni gida akan ya kaini makaranta. Baturen Mr Wallace ya nuna na huta yau gobe sai muje ya nuna min yadda zan ƙarasa registration. Na mai fau-fau akan dole sai mun je makarantar. Ba mu su ya amince, tunda kuɗi aka biya shi ya kula da ni...

Kaman yadda na haddace sunan Hamma Sa'eed haka na haddace sunan address ɗin garden ɗin da za mu haɗu. Ba tareda ɓata lokaci ba Mr Wallace ya kaini wajen. Dai-dai wajen fountain ɗin da ya ce zai zauna ya jira ni dai-dai nan na tsaya amma banga Hamma ba. Na tsaya a wajen ina irga saukar numfashina, wanda ke sauka da sunan Hamma Sa'eed. Ban fi minti goma da zuwa ba amma gani na ke kamar na fi awa ɗaya.  Tun ina sa ran zan ganshi har na fara jin ko dai ya manta ne, ko dai baya son ganina ne ko dai... hawaye su ka fara sauko wa daga ido na. Ina zaune sanyin ruwan da ke ɓulɓula daga fountain ɗin yana ratsa ni amma ni zafi na ke ji.
Daga ta baya na aka sa hannu aka rufe min ido, na sa hannu na taɓa hannun da ya rufe min ido, nan ta ke farin ciki ya mamaye ni. Shekara biyu amma ban manta yadda ɗumin hannunsa ya ke ba.

Tsohuwar Soyayya (Best Hausa love story)Where stories live. Discover now