*ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 9.
INA MATAN DASUKA AMSA SUNANSU KUZO GA INGANTACCEN MAGANIN GYARAN BREAST MAI SUNA BULL - BULL BREAST POWDER MAGANINMU INGANTACCEN MAGANIN GYARAN BREAST NE DA YAKE AIKI ACIKIN 1 WEEK DA YARDAR ALLAH MAGANINMU BADA ZALLAR HATSI MUKA HADASHI MUN HADASHI DA INGANTATTUN SAIWOYI DA MAGUNGUNA DOMIN GYAREN BREAST DA KUMA KARESHI DAGA CUTUTUKA . YAR UWA NONON KI KO YAKAI SILIFAS SABODA YA MUSHEWA IN SHA ALLAH KIKAI AMFANI DA BULL BULL BREAST POWDER ZAKI DACE MAGANINMU BASHI DA SIDE EFFECT KOWA ZAI IYA AMFANI DASHI MUNA DA ZUMAR KIBA DATA HIPS DATA BREAST DUK AFARASHI 👌🏻
INA GARIN KANO MUNA TURA SAKO KOWACE JAHA 08063114606
Madina tunda ta wayi fari ta manta bata yi brush ba, sai ta kama ciye ciyen abubuwa shaf ta manta dan ko data zo wanka sauri sauri tayi saboda ana jiran ta fito ayi mata kwalliya, shiyasa ta manta da yin brush dan dama ba tun yau ba ta saba haka, ita da gari yana wayewa taga abunda take sonci ba wanke baki zata hau cinsa, sai in tazo wanka ne take wanke baki, yau dai kam ta sha'afa ga ango yasha ƙamshin bakinta, har suka rabu bata gano ma yaji ba itama bata ji ba saboda tsabar busy da zumuɗin auren. Amarya ansha hidima dan zuwa yamma ta gayi liƙis kamar anyi mata duka, ganin magrib ya kusa yasa anty Aisha ta haɗa mata ruwan wanka mai zafi sosai danta gasa jiki tace ta shiga tayi ta haɗa da yin brush da alwala, kana ta fito ta shirya dan Habib ya sanar da Kausar ana yin sallar magrib zasu zo ɗaukar amarya, dan dole Madina tayi wanka amma da ta ra'ayinta ne ba zata yi ba dan ita bata ga dattin da jikinta yayi ba, haka ta shiga tayi wanka da ruwa mai ƙamshi dan Aisha ta sanya mata turaren wanka, ta yi wanka da brush sai a lokacin ta tuna ma yau kwata kwata bata yi shi ba, da kuma ta wanke bakin ita kanta taji daɗinsa, sai ta yi alwala ta fito ta shirya cikin wani rigar gown ɗin amare light brown da ratsin cream color a jiki, nan aka yi mata kwalliya sama sama dan cewa tayi bata so, ganin sun matsa tace ayi kaɗan kar a cika mata fuska kamar na ɗazun, bayan ta idar da sallar ne aka yi mata ɗauri, nan amarya ta fito fes daga gani kasan shigar dinner ce, bayan an gama mata shirin sai Anty Aisha ta kama hannunta suka isa ɗakin momy akan za a yi mata faɗa, nan ta zauna akan dadduma ga iyaye nan daga ƙawayen momy sai 'yan uwanta, ko wanne ya shiga faɗar albarkacin bakinsa, faɗa ne dai na yau da kullun da iyaye suka saba yiwa duk ɗiyarsu da za a kaita gidan miji, Hajiya Sa'a ce ta kalli momy tana cewa.
Ƙawata baki ce komai ba kinyi shuru ko har kin fara kewar babyn naki ne.
Hmmm kewa ai ya zama dole gidan zai rage sai ni kaɗai da 'yan aiki, kuma yanzu ma ni me zance bayan kun gama yi mata faɗar, sannan tun biki na saura wata nake yi mata nawa faɗar.
Dik da haka kice wani abu matsayi ki da uwa a gareta.
Cewar wata ƙanwar momy, guntun murmushi momy tayi.
To Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya yasa abokin zamanki ne na har abada, sai dai tunin da zan ƙara yi miki ban yarda ki zauna kishiya ta taka ki ba, sannan kina da gata da ƙima a gidanku muddun Hamid yaso cin zarafinki bance ki saurara masa ba, domin gidan aure ba gidan bautar miji bane gida ne na jin daɗi da farin ciki da ko wani magidanci ya kamata ya bawa matarsa, kinga dai yadda na zauna da mahaifinku har ya bar duniya yana daraja ni domin banyi saken daya raina ni ba, kuma a kishiyoyina babu wacce na ragamawa balle taga damar yi mini iskanci gashi kuma mun rabu lafiya da kowa, dan haka ki tuna ke mai daraja ce babu wani wanda ya isa ya takaki ki kyale shi. Uwarsa kuma in ta ɗauke ki a 'ya to kema ki ɗauke ta a uwa, in kuma ta nuna son kanta ta nima takura miki ki nuna mata ke 'yar zamani ce bance ki ragawa kowa ba wlh.
Nan fa mutanen cikin ɗakin wannan ya kalli wannan, wasu sunyi mamakin maganganun momy amma wasu basu yi ba sanin halinta, dan haka suma suka ɗaura da nasu faɗar, daga bisani aka sanar dasu 'yan biko sun zo, nan aka tasa ƙeyar Madina aka fito da ita falo, sun kawo abinci kala biyu waina da miya da jelof ɗin shinkafa ga kuma kular farfesun kaza daban, abu dai na girma da arziki aka yi shi, su Asma dasu aka zo ɗaukar amarya zai wani kauɗi da iyayi suke yi, ba wani ɓata lokaci aka basu amarya suka rankaya zuwa gidan Hamid.