27

1K 36 7
                                    

*ƘAZAMAR AMARYA*

Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 27.

Hamid tunda ya tafi company ya kasa dawowa gida dan ba zai iya zama shi kaɗai babu motsin kowa ba, sai yaji sam gidan bazai yi masa daɗi ba ba yara ba kuma Sakina, wanda yasan ko abincinta zai sa ya zauna a gida tunda zai samu mai daɗi, sai yamma ya koma gida a zatonsa sai samu Madina ta dawo sai dai bata dawo ba har ya ƙaraci zamansa aka kira sallar magrib yayi alwala ya tafi. Madina sai a lokacin ta dawo bayan ta biya ta gidansu ta faɗawa momy duk abinda ke faruwa, momy nan ta kira mai maganin da suka je jiya tace su ƙara haƙuri aikin a hankali ne zai kama jikin Hamid, sannan ai sunga nasara akan tafiyar Sakina kuma daga haka rabuwarsu kenan, tunda Madina taji haka sai hankakinta ya kwanta sannan momy ta bata shawarar ta lallaɓa Hamid har buƙatarsu ya biya, da haka ta dawo gidan da tunanin sauke kai su koma kamar farko da suka fara. Hamid bai shigo ba sai misalin ƙarfe takwas da rabi bayan sallar Isha'i ɗakinsa ya wuce ya aje snack da yayi oder daga Rahma Snacks and more, sai yayi wanka ya shirya ya fito falo ya zauna ya kunna tv ya soma kallo, a lokcin ne Madina ta fito cikin shigar ƙananun kaya ta zauna a gefensa tana ɗaura kai a gefen kafaɗarsa.

Beb ka shigo shine ba zaka nimeni ba, dan Allah kayi haƙuri komai ya wuce bana jin daɗin zamanmu a haka.

Me kuma ya faru ina ce komai ya wuce.

To in ya wuce mai zai sa kaki shigowa ɗakina?

Hmmm meyasa kika yi dare baki dawo daga aiki ba, tun safe fa kika fita.

Aikin ne yayi yawa a office ɗina saboda hutun dana yi amma gobe In Sha Allah bazan kai yamma ba.

Yayi.

Yace a takaice, Madina ta sauke ajiyar zuciya.

Beb dan Allah ka nimo mana abinda zamu ci yunwa nake ji kuma na gaji bazan iya girki ba.

Madina bazan cigaba da kashe kuɗi ba alhalin na wadata gidana da kayan abinci, ki miƙe kije ki dafa duk abinda kike son ci, ni zan kwanta sai da safe.

Ya ƙare maganar yana janye jikinsa a nata ya miƙe, da sauri ta kamo hannunsa.

Hamid Wlh ban iya girki ba shiyasa tun farko nace ka nima miki mai aiki, a gidanmu sai dai a dafa a bani.

Ashe shiyasa kika haɗa girkin daya kusa kasheni ni da Hajiyata, dan haka kisan yadda za kiyi amma tsarin gidana ba bu 'yar aiki ko ba kiga Sakina kewa kanta komai bane, to kema ki koya ki yiwa kanki komai, gobe In Allah ya kaimu kafin ki fita ki tabbatar da kin gyara shi dan ya fara aje ƙura, kuma na duba kitchen akwai wanke wanke duk kiyi su kafin kije aiki kinji na faɗa miki.

Ya ƙare magana yana nunata da tsaya daga bisani ya juya ya mufi ɗakinsa ya shiga, Madina kasa magana tayi jikinta har rawa yake yi akan sauyawar da yayi mata, kamar ta fasa kuka haka ta koma ta zauna tana tunanin abin yi, sai da ta ɗauki kusan minti talatin a zaune ta rasa me takewa tunani, ga dai gida daga ita sai Hamid ba Sakina ba yaranta babu wanda zai kawo musu cikas wajen cin amarci ko a falo suka so suyi komai ba mai damunsu, amma kuma ya juya mata baya ya sauya mata yadda ko dariyarsa bata gani, ga lissafin aikin gidan da yake yi mata wanda ko kusa ba zata iya yinsu ba, sauke ajiyar zuciya tayi ta miƙe ta mufi kitchen ta haɗa comflex ta zabga madara ta fito da kofin zuwa ɗakinta ta zauna tana sha cike da damuwa, bawai dan yana mata daɗi bane kawai ta kawar da yunwar da take ji ne. Misalin ƙarfe sha ɗaya taji motsin Hamid ya fito ya ɗauki ruwa da drink ya koma ɗakinsa, koda ta fito da nufin shiga sai ta jishi a rufe ta soma kiran sunansa yana jinta amma yayi banza da ita, haka ta koma ɗaki ta soma kukan baƙin ciki wanda a haka barci ya ɗauketa.

Da safe da wuri Hamid ya shirya ya fito falo ya aje mata dubu ɗaya ya fita, ƙugin motarsa data ji ya sata fitowa da sauri ta fito, sai dai ta hango bayan motar ya fice ga kuma sabon mota da take da yaƙinin nata ne driver ya bi bayansa da ita, da sauri ta koma ciki dama shirin fita aiki take yi, ta ɗauki wayarta ta kira Hamid har kiran farko ya tsinke a nabiyu data kuma kira ya ɗaga ba tare daya ce komai ba.

KAZAMAR AMARYA Completed Where stories live. Discover now