Thriller

515 37 15
                                    

Breaking news "VOA"
"MOHH Ya kashe matarsa bayan tafiyar ƴan kai amarya"

Labaran kai tsaye na fita ne daga bakin matashin ɗan'jarida mai sanin makamar aikinsa a kodayaushe. "WAHEED J KALLAH" bayan wahalataccen numfashi da yaja yana mai duban camera ƙirjinsa na dokawa ya ɗora da;

"Waye MOHH?
Waye Scorpio?
Jama'a na zargin mutum ɗaya ne, ƙila dai mun yi sara ne akan gaɓa, ba tare da ruwanmu ya kai tsaiko ba, SCORPIO sananne ne MOHH fa? Ya amsa tuhumar da ake masa kai tsaye ba tare da bawa jami'an tsaro wahala ba, wakilin VOA Shateema ya kawo mana rahotan. Tambayar a nan, shin baya son ta ne? Me ya sa ya zaɓi ya kasheta ta hanya mafi muni?..."

****
Dukkan naman jikinsa rawa yake da wani irin ɓari zuciyarsa na tafasa. Tun bayan faɗan da ake yi masa bai ɗago ba, balle ta tofa tasa "Ina jin kamar na haifawa kaina matsala"

Ya ɗago rinannun idanunsa wani irin ruwa ne kwance a cikinsu, jijiyoyin kansa sun yi ɗoɗar tare da jerewa suna harba masa.

"Mutallab" ya ji zuciyarsa ta kirayen shi, kiran da sai daya ja numfashi ya haɗiye abinsa zuwa ciki ba tare daya fesar ba, yana jin hucin zuciyarsa na keto ruɓin fata bakwai da Ubangiji ya halitta a jikinsa, me ya sa suke son yi wa rayuwarsa iyaka da jin daɗi ne? Shahara tare da daular da yake mafarki suke son yi masa farraƙo da ita? Da gaske arziƙi yake so, iko yake buƙata, lalle suna son tauye rayuwarsa.

A hargitse ya furta "Kar ka yi mini baki, Abi da kun sani da ba ku yi cikina ba, da kun sani da baku yarda kun haifan ba, karku ƙuntata rayuwata ba zan ɗauka ba"

Kuka take sosai ya saka ƙafa ya buga jikan ƙyaure nan take ya faɗo, ya dinga dunƙule hannunsa jini na zuba rezar na shigewa ciki hannun.

"Idan na lalace ku na lalacewa domin zama zan yi mu raba hisabin tare" Ya faɗa yana zaro mesa daga cikin aljihunsa ya rataya a wuyansa.

"Me kake so?"

Kai tsaye ya ce "KUƊI, IKO!"

*****
Tunaninsa ya barranta ya dire allon hannun nasa ya dubi Abi tun safe yau bai furta komai ba sai yanzu.

"Duka ne dai ka daka Abi, ba zan iya karatun nan ba, ka dake ni ina da shiga dawa yau, zan kamo ɓauna, bulala ɗari ce ko dubu ɗaya?"

Da idanu Abi ya yi wa gardawa nuni suka kame shi nan take ya ɗaura masa mari.

BAN CE NA FI KOWA BA,
BAN CE ZAI ZAMA DABAN BA,
NA DAI SAN BAKU TAƁA CIN KARO DA HAKAN BA,
LALLAI ZAKU ƘAUNA CE SHI,
ƘAUNA MAI YAWA,
MUSAMMAN GA IYAYE MATA DA MAZA?

INA SON JIN RA'AYINKU A SHARHI. MU FARA NE?

MUTALLAB Where stories live. Discover now