Chapter 1

85 5 1
                                    

Jami'an tsaro ne ta ko'ina cikin kayan kaki ma bambanta, duk da cewa yammacin ranar lahadi ne a watan Fabrairu bai hana ta gane fuskarsa ba. Cikin tashin hankali jikinta na rawa da kyarma ta nufe shi tare da ƙoƙarin cakomo wuyan babbar rigarsa tana furta cewa "Shi ne, wallahi shi ne, daman na ce zan gano shi" a gigice mutumin dake ƙoƙarin shiga motarsa da aka buɗe masa ya yi baya yana mai ƙarewa matar kallo sosai sai dai ya kasa gano ko wace ita? Daga ina me kuma take buƙata.

"Wace ita?" Ya furta yana tambayar zuciyarsa tare da kallon gefe. "Wallahi shi ne, mugu azzalumi sai ka yi kuka, ka wulaƙanta " Jin furucinta ya saka ƴan'jarida dawowa kan ta, suka fara tambayar "Kin san shine? Mene haɗinki da shi?" Kafin ta yi magana wani ya ce "Arrest her, ku kamata"

A hankali ya jingina da jikin motar can ya numfasa yana kallon yaronsa ya ce "Wace ce? Na santa ne? To me ya sa take abu kamar ta sanni?"

"Sir da gaske ta sanka bana jin ko mutuwa ta yi ta dawo zata manta fuskarka, kuma zamanta a raye yana nufin abubuwan da yawa dole a yi wa tufkar hanci, kar a bari ƴan'jarida su samu ganawa da ita, even your securites, wannan matsalar kai da kai ce kuma zata shafi kimarka" cike da mamaki ya yi ta kallon yaron nasa na tsayin sacanni da ƙyar ya cije leɓe ya ce "To ina na santa? Me ya sa zata zama damuwata?"

"Sir ita ce wacce ka saka aka kawo maka ita, wacce ka yi wa fyaɗe a lokacin.....,"

"Ya isa!" Ya ce yana jin jiri na neman ɗauke shi, ya dubi tarin jama'ar da suke wajan can ya yi murmushi yana ɗauke fuska sai kuma ya ƙurawa yaron idanu ya juya ya kalli matar ya gyatsine fuska ya ce "kuma ta kasance a raye ya haka? To a yi hanzarin toshe wannan ɓarnar ya zama kamar ba a yi ba"

"Amma me ya kamata a yi mata?"

"A yi mata allurar hauka, wacce ake yi duk shekara da wata wata kana a kaita gidan yari, life in prison har ta mutu. Bayan haukan zata mance komai, su ƴanƴan talakawa wama ya damu da su mutu ko su yi rai bata da wani mai tsaya mata kai mutuwa ma za ta yi" yana faɗin hakan ya shige mota. Tana takure a jikin ƙofar ɗakin da aka ajjiyeta idanunta ƙur a kan photonsa zuciyarta sai zafi take mata wani abu ya tsaya mata. Da sauri ta juya jin an buɗe ƙofa wani mutum ne sanye da farar riga ya rufe fuskarsa hannunsa riƙe da ƙaton sirinji iya ruwan allurar da ya yi ja abin tsoro ne, ta fara ja da baya amma a haka ya fincikota tare da yin cilli da ita,ta faɗi saman carpet bai tsaya jiran komai ba ya caka mata allurar a ƙashin bayanta wajan spinal cord ihu ta fara da birgima idanunta ya shiga ƙaƙƙafewa jikinta na sandarewa ta dinga buga kanta da jikin bango tana buge-buge a hankali jini ya fara fitowa ta cikin hanci da bakinta tabbacin allurar ta amshe ta za kuma ta yi aikin da ake buƙata a jiki da ƙwaƙwalwarta.

******
Cikin sauri suke tafiya a wani ɗan dogon lungu mai duhun gaske tsarin wajan gabaɗaya a ƙuntacce yake kamar zunubin gidan yari. Magana suke ƙasa-ƙasa ɗaya daga cikin su kuma yana duba agogon dake hannunsa tare da duba cikar lokacin fuskarsa a haɗe take sosai. Sai da suka kawo ƙarshen ginin suka tsaya ya ɗaga kai a hankali ya dubi saman da kansa ke taɓowa ya ɗan rusuna sai kuma ya dubi jami'in tsaron dake wajan ya yi masa nuni daya buɗe ƙofar. "Yes sir!"
Bayan ya sara ya ƙame ya buɗe ƙaton kwaɗon yana toshe hanci saboda wari da zarnin wajan. SP Gali  ya kalli team ɗin nasa cikin bada umarni ya ce

"Ku jira nan, idan akwai damuwa zan muku alama na san dai he can't do anything, ba zai iya komai ba" gabaɗaya suka jinjina masa kai tare da zagaye ƙofar fuskar kowannen su manne da baƙin gilas. A hankali Sp Gali ya tura ƙofar ya shiga yana durƙosawa saboda rashin girman wajan. Tunda kafin su ƙarasu wajan ya san da zuwan nasu har aka buɗe ƙofar tare da shigowa, yana durƙushe inda yake ya kifa kansa a ƙasa hannunsa dunƙule ya damƙe abu wanda tun kafin a kawo shi gidan abu yake a hannunsa, yin duniya yaƙi buɗe abun balle a san menene shi.

"Hey you!" Sp Gali ya ce yana saka ƙafa tare da buge ƙafarsa ganin yaƙi motsawa, tamkar gunki haka yaƙi motsi ya kuma ƙi ɗago kansa Sp Gali ya shiga kallon wajan ya rasa wanne irin hali ne da wannan yaron mai baƙar zuciya da taurin kai ya sauke numfashi cikin kwantar da murya ya ce "Ni idan na ce maka ina da tausayi na yi maka ƙarya, amma ka saka zuciyata karaya kana bawa kanka wahala kana bawa jami'anmu wahala. Me zai hana ka sauƙaƙa mana wahalar nan ka faɗa mana gaskiyar abin da ya faru a wannan rana kuma a wannan daren? Me ya sa ka aika abin da ka aikata? Ka kashe matarka, ka kashe ta har lahira kuma kaƙi magana shekara uku kenan kana wajanmu ka rainawa hukuma hankali da kotu, kai baka da zuciya ne dame kake taƙama saboda kana da tsari a jikinka ƙarfe ba zai ratsa naman jikinka ba, muna da kalolin azaba nau'i-nau'i amma gaskiya muke buƙata, ka amsa cewa ka kashe matarka a zaman kotu na yau shikenan sai a yanke maka hukunci daidai da zaluncin da ka aikata"

MUTALLAB Where stories live. Discover now