Chapter 5

58 4 1
                                    

"Safiyyerh Abdu Marafa Manager ce a Kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY kuma ƴa a wajan tsohon leccara, muna buƙatar ka yi mana kidnaping ɗin ta" Moh Kallo ɗaya ya yi wa photon da suka bashi ya ɗauke kai
"Ka santa?" Shi dai bai ce komai ba.

Eng Ali wali ya dinga kallon Moh yana tunanin abubuwa da yawa a ransa kafin ya ce "baka gama ganin photon bane, ko da yake yana da kyau da ƙare mata kallo maybe ka zama silar mutuwar ta ko ka kashe ta da hannunka, ka ya zama dole ka gane kamamminta"
Goje ne ya ɗago kai da sauri yana kallon Eng Ali wali kafin "Sai da kai mai gida wannan aikin ai ko ni zan iya yin shi ba sai Mai dawa ba, ka huta ka sarara mai gida"

Eng Ali wali ya yi murmushi yana jingina da kujera ya ɗauki ƙafarsa ya ɗora akan ɗaya ya kalli Mai dawa wanda ko motsi bai yi ba sai jujjuya photon da aka bashi yake. "Ko Mangal ba zai iya aikin nan ba da ya fika wayo a sabgar balle kai da na sani yanzu, shi wannan Mai dawan idanunsa na kalla na san zuciyarsa za ta iya aikata komai"

Ya yi shiru sai kuma ya ce "Ni ɗan siyasa ne babu mamaki ka taɓa ganin poster na  ko bana, shekaruna takwas ina riƙe muƙamin Ɗan majalisa na tarayya a jam'iyyar da nake ta kara, bani da ra'ayin haƙura da kujerata kamar yadda ake yi mini kirarin idan na yi na gama na karya kujerar. Siyasa jinina ce Mai dawa, bana jin akwai wani dalili da zai zo ya saka na haƙura da kujerar na amma wannan karon na yi karo da muruci wanda yake shirin yi mini wahalar dafawa ko ta halin yaya ne dole na sake hawa kujerar nan a karo na huɗu. Hon Maɗatai yana tare da manya wanda suka san kan siyasa ciki da bai dole mu fito da salo na musamman wanda zai kai su ƙasa. Hon Maɗatai shine ɗan takarar jam'iyyar hamayya kuma yana da ƙarfi har yanzu ba'a san mene rauni ko aibun shi ba amma akwai jita-jitar data zo kunne na domin tabbatar da gaskiyar al'amari ya saka na kawowa cikin jama'ata"

Sai a lokacin Mai dawa ya ɗago kansa ya ɗan kalli Eng Ali wali kamar ba zai ce komai ba sai ya cije baki yana karkatar da kai gefe ya haɗa hannayensa biyu suka bada sauti mai ƙara cikin wata murya ta izza ya ce

"Mene haɗin ta da maganar yawar ku?"

Eng Ali wali ya ce "Wa kake magana"

"Ita ɗawar mai ɗan kwalin?"

Cikin rashin fahimta Eng Ali wali ya ce "Meye ɗawa da ɗan kwali kuma?" Mangal ya yi murmushi yana "Ka fice Mai gida, ɗawa da mai ɗan kwali mace kenan ake kwafa maka zancen" Ya ce "Yaran naku sai ku"

Miƙewa Mai dawa ya yi tsaye yana ɗora ƙafarsa a saman farar kujerar dake parlon kallonsa kawai Eng Ali wali ya yi bai ce komai ba. Sai wani ya ce "Mai dawa farar kujera ce fa?" "Ko takaddar jikinka zan ɗora ƙafa akai" wanda ya yi maganar ya yi saurin kallon farar shaddar dake jikinsa fara tas da ita sai ya ja bakinsa ya yi shiru. Moh ya kalli gefe yana furzar da iska daga bakinsa ya ce

"Me ya sa ka neman, bayan kana da gajojinka?"

"Saboda kai ne baƙuwar fuska a cikin wannan sabgar tamu, ba wanda zai gano cewa a tsagina kake za ka yi aiki mai kyau hankalina ya kwanta da kai Mutallab" wani irin kallo Mutallab ya jefa masa idanunsa sun sauya kala ya yi murmushi ya ce

"Oh Mai dawa da jeji, ya batun yarinyar ka santa ne ko ka taɓa ganin fuskarta?"

"Na santa ko ban santa ba ina jin bashi kake buƙata ba. Yaushe kake so a kawo maka ita?" Girgiza kai Eng Ali wali ya yi ya ɗauki ruwa ya kurɓa ya ajjiye kana ya miƙe tsaye yana zagaye parlon hannunsa a baya "Ka jira umarni na, kawai ka zama cikin shiri a koyaushe zaka iya jin kira. Akwai gidan dana samu a bayan gari zan baka makullin ko ka ɗakko ta can zaka ajjiyeta kai ne zaka dinga kula da ita har yanzu lokacin da muka shirya abin da mukai niya, a cikin gidan akwai kayan aiki irin naku wanda za su sama muku nutsuwa"

Goje ya jinjina kai cike da jin daɗi kafin ya ce "Mai gida za a siya mana mota mai iska kamar yadda muke ƴaƴan iska?"

"Za a yi muku komai, ku riƙe amana. Sai dai kawai sharaɗi ko da wasa kar ku nuna kun sanni idan ina buƙatar ganin ku a wannan gidan zamu dinga haɗuwa, ku buɗewa kowa idanu kar ku ji tsoro da shakkar komai ni zan tsaya muku har zuwa ci zaɓe" Moh ya ce "Bayan cin zaɓan fa?"

MUTALLAB Where stories live. Discover now