Chapter 9

21 1 0
                                    

"Bani da wani zaɓi sai na hakan, haɗa auren Aliyu da Safiyyerh kar ku tambayan dalili kar a tambayan cikin Safiyyerh da Aliyu waye ba ƙwayar halittata bace ta yi sanadin zuwan shi duniya, hankalina zai fi kwanciya kafin Ashraf ya kwana cikin kabari ya zamana Safiyyerh nada igiyar aure a kan ta" ajjiyar zuciya Sharfaɗi ya yi idanunsa a kan Prof Abdu Marafa ya ce "Me kake jin tsoro da kake so dole ka aurar da ita, Allah Ya gani amintar mu ya saka muka yanke hukuncin haɗa yaran nan aure saboda ƙarfafa zumunci, to kana taka Ubangijin talikai na tashi nasa kuma shine gaskiya, Ashraf ya rasu baya duniya ina tunanin ka bar yarinyar nan ta samu nutsuwa ta duba wanda take so yake son ta sai a yi mata aure, kar a ƙuntata rayuwar yarinya"

"Sharfaɗi ba zaka fahimta ba, ka yi mini wannan alfarma ka wakilci Aliyu ni zan wakilci Safiyyerh ga jama'a su shaida Please sai a haɗa a yi addu'a har ta Ashraf"  J zufa har yanko masa take yi na tsananin mamaki mene haɗin Captain da Safiyyerh da za a yi musu aure? Baya son zuciyarsa ta gasgata abin da yake jin tsoro ko wassafo shi cikin kan shi, Safiyyerh fa and Aliyu? Ya Allah! Shi dai Awais kan shi a ƙasa Dr Hash daman baya wajan yana can duba Fiyya tunda ta faɗi wajan ya yi shiru can daddy ya ce

"Kawai alfarma nake nema zan ji daɗin hakan idan ka yi mini"

"To shikenan, waye maɗaurin auren?"

Daddy ya nuna wani abokinsa, Sharfaɗi ya ciro kuɗi mai yawa a cikin aljihu ya dire ya ce "Ni Sharfaɗi ina nemawa ɗana Aliyu Abdu Marafa auren Safiyyerh Abdu Marafa a wajan waliyi na wannan yarinya" daddy ya saka hannu ya ɗauki kuɗin ya ce "Ni Abdu Marafa uba a wajan Safiyyerh Abdu Marafa na bawa Aliyu Abdu Marafa auren yarinyar wajena Allah Ya sanya musu albarka" addu'a aka yi nan take kuma aka ɗaura auren a gaban shaidu ma ɗaurin ya ce

"Aure ya ɗauro a kan sadakin da Sharfaɗi ya bawa dubu ɗari biyu, Allah Ya sanya albarka tsakanin Aliyu da Safiyyerh ya kuma kaɗe fitinar da kan iya wanzuwa a tsakaninsu" duk aka amsa da amin. Daddy ya lumshe idanunsa yana sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya nutsuwar ta saukar masa, bashi da sauran fargaba a yanzu Safiyyerh ta zama matar wani.

Kasancewar rasuwar ɗan babban mutum ce kamar Sharfaɗi ya saka manyan mutane zuwa gaisuwa, ƴan kasuwa da ƴan siyasa da wanda dai suke jin kansu wasu ne a garin. Kallo kallo aka shiga yi tsakanin Hon Maɗatai da Eng Ali wali dukkan su cikin shiga ta alfarma, ga mutane da take musu baya kowanne da tarin ƴan jagaliya da ƴan daba gudun kota kwana. Hon Maɗatai ya yi murmushi yana miƙawa Ali wali hannu ya ce

"Kwana da yawa Ali wali?" Ali wali ya ɗauke hannu sai kuma ya juya ya ce

"Ba yanzu ba ka jira na wani lokaci komai zai haska, za a yi tsawa walƙiya ta bayyana munafukan da suke ɓoye cikin duhun ciyayi" murmushi Hon Maɗatai ya yi kawai yana furta "Allah Ya nuna mana" gaisuwa duk sukai sai dai daddy tsakaninsu kawai addu'a ya miƙewa daga wajan. Bayan yin ta'aziyya Hon Maɗatai ya ce "Allah Ya yi wa Ashraf Rahama, ya taƙaita iya kan shi" Sharfaɗi ya juya ya kalli Hon Maɗatai kana ya kalli Eng Ali wali sai kuma ya ce "Amin, yanzu ba gashi ba gwanin sha'awa a dinga siyasa bada gaba ba sai an fi samun nutsuwar zuciya data ƙwaƙwalwa duk wanda zai samu wannan kujerar Ubangiji ya gama rubutawa kawai dai lalube ake yi cikin duhu ku haɗa kai da hannu kowa ya yi kamfel nasa babban jin daɗin ba jam'iyyarku ɗaya ba"

Cikin jinjina kai Hon Maɗatai ya yi murmushi daman shi bashi da wata matsala da Eng Ali wali shi yake haukan shi hankalinsa na kan wanda ya yi shiru, shirun nasa kuma yana nufin babbar barazana a gare shi "Siyasa ai ba zata haɗa musulmi irina faɗa da wani ba, munga jiya mun ga yau muna da tabbacin za muga gobe mai kyau, ni fatana na samu gurbin saka hannun jari a kamfaninka idan aka bani dama an yi mini komai Sharfaɗi" daddy na jin su can aka kira shi waya da sauri ya miƙe tsaye yana neman uzurin tafiya Eng Ali wali ya bisa da idanu.

Cikin dare Fiyya ta farka da wani irin ciwon kai na ɓari guda, ta kasa buɗe idanunta a hankali ta saka hannu ta dafe kan ta duk da halin cewa bai hanata yin addu'a ya yi tashi a baccin ba domin tabbatarwa da kanta ba a cikin kabari ta farka ba. "Sannu Maama" shine abin da Ummi ta iya cewa tana hamdala a ranta domin shirun ya yi yawa ta damƙe hannunta sosai

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: 5 days ago ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MUTALLAB Where stories live. Discover now