Chapter 3

46 2 1
                                    

Da sauri ya nufe ta kamar zai kai mata cafka, ta yi saurin ja baya idanunta cikin nasa. Yana tangaɗi ya ja ya tsaya a gabanta tare da ƙura mata idanunsa da suke lumshewa, har yanzu jikinsa ɓari yake domin basu daina buga ganga da ƙahon da suke busawa ba kamar masu yin gangi.

Hannunsa ya ɗaga musu cikin sauri suka daina abin da suke, cikin izza da gadara ya basu umarnin tafiya har lokacin idanunsa yana kanta ganin yadda take kallon shi kamar ya ta saba ganin halittarsa. "Ban yi zaton a haka zan ganka ba, autan Ammo me ya sa?" Ya ɗauke kansa yana haɗe fuska sosai ba wargi banda cewa ita ce ba zai taɓa tsayawa ba. Cikin raunin murya kamar za ta yi kuka ta ce "Me za ka yi da wuƙa haka?" Ya buɗe ido sosai sai bai magana ba, a hankali ma ya bi gefen ta zai huce ta yi saurin riƙe masa hannunsa tana faɗin "Ni ɗin ma? Yau za a ji kan mu da kai, kar ka faɗa mini sauyin da ka yi ya zagayo har kai na?"

Ya ɗago kai ya kalle ta ya kalli hannun data riƙe shi da shi, hannunta fari tas saɓanin nasa da yake mai kauri kuma baƙi irin na majiya ƙarfin nan wanda suke tashe akan shekarunsu. "Don Allah ka tsaya mu yi magana, ni ko gidan ba zan shiga ba wajanka na zo" ya cije bakinsa ya mai da kai gefe cikin muryar mai kauri ya ce "Kin ci darajar Ɗan Amina, mene sakin?" Ta girgiza kai kawai tana duban gefe dakalin dake wajan ta gani ta je ta zauna akai, ta yi masa alama ya zauna amma ko motsi bai yi ba, ta san cewa yana jinta amma hankalinsa na kan hanya sai waige-waige "Mutallab ka kalle ni bafa wani zai kawo maka farmaki ba" ta nisa idanunta cike da ƙwalla ta ce "Don Allah kai ne ka kashe ta? Ba zargin ka nake ba Autan Ammo ni me iya rufa maka asiri ce idan ya zama kana da laifi ka faɗa mini gaskiya na maka alƙawarin ko Ammo ba zan faɗawa ba, ka kashe matarka ko ba kai bane?"

Ya juya da wani irin sauri yana kallon fuskarta da take kallon shi cike da damuwa, idanunsa ya yi jajur naman jikinsa na motsawa ya kasa furta komai. Miƙewa Anty Hameeda ta yi tana girgiza kai kuka na cin ƙarfinta "Ko minti ashirin ba mu yi da kai maka matarka ba, sai labarin mutuwar ta muka ji da kisan wulaƙancin da aka yi mata. Mutallab kai ne fa muka gani tsaye akan gawarta, kai ne fa riƙe da wuƙar da aka kashe ta da ita jikinka duk jinin matarka innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na kasa yadda ka kashe ta, daman soyayyar da ka nuna mata na iya fatar baki ne?" Wani irin ihu Anty Hameeda ta yi tana kaiwa jikin bango ganin ya ɗaga hannunsa ya yo kanta sai kuma ya tsaya cak, a hankali da baya da baya ya dinga ja yana ƙare mata kallo sai kuma ya taune bakinsa idanunsa kamar zasu zazzago don girma kallo ɗaya idan ya yi dasu sai an razana da ƙyar ya iya ware laɓɓansa biyu da sukai masa nauyi sosai ƙasan zuciyarsa na ta fasa banda cewa Anty Hameeda ce tabbas da sai ya karya ta gida huɗu.

"Ni na kashe ta, ta cancanci haka ne" ya juya da sauri Tiger da spider da rainbow suka bi bayansa kamar zai tashi sama haka ya sha kwana. Zubewa Anty Hameeda ta yi a wajan tana rushewa da kukan baƙin ciki, su waye suke da saka hannu wajan lalacewar Mutallab? Ba komai ta sani ba ita ba ma'abociyar zaman garin bace ita da mijinta ta dinga kuka da ƙyar ta rarrashi kan ta, ta miƙe tsaye kamar zata shiga gidan nasu sai kuma ta fasa tana ƙoƙarin barin wajan ta ji Malam ya ce "Hameedatu me kike anan ina mijin da yaran naki?" Kanta a ƙasa ta ce "Suna gida, ina yini Malam?" Ya jujjuya yana kallon hannunta ganin babu komai ya ce "Ba za ki shiga bane?" Ta girgiza masa "Zan juya wajan Mutallab na zo" ya jinjina kai domin ba wannan ne a gabansa ba.

"Ba wata mutalla da zan iya samu a wajanki na siyo wainar rogo?" Ta buɗe jakarta ta zaro kuɗi tana irgawa ya yi maza ya fisge ya ce "Mene na lissafi? Maza jeki wajan yaranki kuma na ja kunnenki babu ke babu yaron nan idan ba su kike watarana ya ja miki masifar da za ki ƙare rayuwarki a gidan ɗan kande ba" bata ce komai ba sai data juya zata tafi ta ce "Duk lalacewar Mutallab kai ne ka haife shi, jininka na wanzuwa a nasa" tana kaiwa nan ta yi gaba abinta saboda ɓacin rai da damuwa ko gabanta bata gani sosai.
 
Moh na kwance a saman wani dutse idanunsa a rufe tun bayan barin shi wajan Anty Hameeda ya zo wajan ya kwanta, zuciyarsa a cunkushe take babu gurbin samun sauƙi a cikinta duk yadda ya ke son tuna waye shi me ya sa ya zama haka sai ƙwaƙwalwarsa ta yi hooking, ya ɗauki zafi sosai ta yi ta processing ya ji Ammo ɗinsa kawai yake son kasancewa da ita yanzu. Ya motsa kaɗan zazzaɓi ne sosai a jikinsa saboda saran da aka yi masa bai gama warkewa ba, baya kuma shan magani wacce zata iya kula da shi baya jin zai iya zuwa wajanta. Ya ƙanƙame jikinsa sosai abubuwa da yawa baya son tunawa sai ya cimma muradin zuciyarsa sai ya ɗauki fansa na abin da aka aika, sai ya bayyana abubuwa da dama tunda har suka bari ya shiga cikin gidan yari ya kuma yi shekaru uku a Cid ya rayuwa cikin masu aikata manyan laifuka. A sama ya ji an kira sunansa

MUTALLAB Where stories live. Discover now