Chapter 2

67 4 2
                                    

Cikin bukkar ya faɗa  jikinsa jina-jina da jini sara ta ko'ina da ƙyar yake iya fidda numfashi, ya zube a gabanta idanuwansa a lumshe har yanzu yana jiyu sautin ihu da kukanta, ya kasa ceton ta, ta sake mutuwa, yaushe zata ci-gaba da rayuwa tana sake macewa akan idanuwansa? Ya cije jajayen laɓɓansa wanda jini ya ɓata sam bai damu da yadda yake shanye jinin yana koma masa ciki ba, a matuƙar fisge ya yi maganar mai sautin gurnani ya ce "Na amince, da gaske na amince Abbasa, zan zama mata maza, ki mayar dani jinsin mace ina tunanin zama macen ya yi daidai da tafiyar ƙaddarata! Zan zama mata maza, bana iya kwanaki ba, bana iya wa'adin sa'a ba, ba kuma iya na tafiyar sakwanni ba, ba kuma iya na gilmawar kwanaki ko shuɗewar watanni da nisan shekaru ba, a'a Abbasa, a'a Abbasa ina son zama mata maza ne na daidai da tafiyar agogo da adadin shekarun da zan yi a duniya"

Yadda furucin ke fitar da kan su, da yadda yake magana idanuwansa na fiddowa waje duka jikinsa rawa yake da ɓari yana wani irin tsuma bakinsa har wani hayaƙi yake yi jijiyoyin kansa tamkar zasu ratsa fata bakwai su keto, ganin halin daya shiga ya saka Abbasa cewa. "Iya zubin tunanin naka kenan? Iya jarumtar kenan? Mayar da suffarka zuwa abi mafi nakasu a rayuwarka? Ka zama mace shin ko ka mace da......"

"Abbasa!"

Ya kira sunanta a karo na farko a tsawa ce, domin baya son tuna abinda take ƙoƙarin cewa "Shikenan shikenan, zaka zama jinsi biyu, mai halitti biyu" ya girgiza mata kai yana jin amo da sautin muryarta cikin wutar da suka babbaka ta ciki "Kawai ki nakasta ni" "Tabbas zaka nakasa, zaka zama kamar jaririn da aka haifa yau, zaka zama riƙaƙƙe zaka gagara, ubanka zai alfaharin haihuwarka duk da tsinuwarsa na tattare da kai, zaka sake yi rashi, rashi irin wanda baka taɓa yin irinsa ba, zaka samu dukkan wata shahara da ɗaukaka da kake buƙata, amma zaka dauwama a matsayin mata maza"

Ihu ya fasa yana ƙoƙarin miƙewa tsaye da ya yunƙura gefen cikinsa yake sake buɗewa saboda shafcecen saran da aka yi masa, jikinsa bashi da wani gurbin da babu sara.Abbasa ta miƙe ta ɗakko wani farin abu a hannunta tana zuwa kan shi ta danne shi da duka ƙarfin daya zo mata, ta ɗauki garin abun ta fara shaƙa masa a hanci yana shaƙa da ƙyar da sauri ya damƙi hannunta ya kifa fuskarsa da hancinsa gabaɗaya, yana ihu da gurnani jikinsa na rawa ya fara sambatu, Abbasa ta ce "A me ka zo waje na?"

"Taya" ya bata amsa a raunace idanunsa na lumshewa. "Wasu sun biyo ka ne?" Ya girgiza kai can ya ce "Cinnaku, Cinnaku na fi ƙarfin su" ya dinga juyya kansa can ya ce "Akwai Kimini a tattare dani, ya faɗawa ƙashi wani abu, sun nemi asawa da Tsohuwa....!" Ya kasa cewa komai idanuwansa har yanzu na hango yadda gangar jikinta take ci a wuta.

Ita dai Abbasa ta kasa cewa komai ta zuba masa idanu, ta dinga kallon yadda jikinsa je rawa a hankali kuma ya fara saki idanunsa ƙur a saman bukkar cikin fitar hayyaci da yanayi irin na maye yake sambatu tare da kiran sunayen da ita kanta mata sani ba. A hankali ta ce "Mutallab" bai amsa ba sai zuciyarsa kawai dake rawa ta hango hakan ne a yanayin yadda ƙirjinsa ke ɗagawa. Ganin ya zama kamar matacce tsoro ya kama Abbasa ta tuna ashe bai taɓa shaƙar abin da ta bashi ba a yanzu, maganin ƙarfe dana tauri kawai yake sha gashi kuma zaman da ya yi na shekara uku a hannun jami'an tsaro ya sa tsarin ya karye.

Ƙwarya ta ɗakko ta jiƙon wani magani tare da ruwa mai zafi ta fara danna goge masa jinin jikinsa sai a lokacin ta lura da gabaɗaya farcen yatsun ƙafafuwansa dana hannu babu ga jikinsa duk alamar an jona masa shokin akan tilasta masa amsa laifin da babu wanda yake da masaniyar komai akai, sun yi masa haka ne da nufin ya amsa laifin kashe matarsa da ya yi. Ta sauke numfashi tare da kallon bakinsa a hankali ta kara kunnenta a tausashe yake cewa.

"Ina son ta, ina son ta zuciyata zata fito ita ce wajan ta uku me ya sa.... Ina jinta a ƙasan zuciyata"  Tunda suke bai taɓa yi mata zance ɗiya mace ba, haka bai taɓa magana mai tsayin da ya yi a yanzu ba, duk abin da ya saka Mutallab magantuwa ba ƙaramin abu bane ba. Miƙewa ta yi ganin kamar ya samu yin bacci ta fita waje zuciyarta cike da saƙe-saƙe.

MUTALLAB Where stories live. Discover now