MATAR SOJA
AREWA WRITER'S ASSOCIATION💦Book one
Rashma
Page two
Free page
murmushi ya saki shikam ya rasa wace irin mace ce wannan gaba ɗaya kishi ya rufe mata ido miƙewa yayi ba tare da yace mata uffan ba ya shige ɗakinsa hakan da yayi ba ƙaramin fusata ta yayi ba miƙewa tayi ta fice sashen ta,ta shiga a falo ta sami yaranta gaba ɗaya Kamal ne kawai baya nan sai Rashida da taje gidan ƙanwar Aunty "wallahi duk wanda ya sake gaida waccen matar ban yafe masa ba."
"A'a Aunty me yayi zafi haka wannan ai bai dace ba."
"Ai nasan wanda zai fara bani matsala Umar kaine ko waɗan da ban haifa ba suna min biyayya amma banda kai."
"Aunty ba haka bane kawai gaskiya nake gaya miki ɗafa na kowa ne me tamiki haka da zafi kika tsane ta."
"Ka gwada gaisheta ka ga ikon Allah."
Daga haka ta shige "to Ya Umar me zaka dami kanka ni dama ba gaishe ta nakeyi ba."
"Safna kina manta waye Ya Haidar bare uwa uba Dady kinsa dady yakan manta cewa shi ya haife ki wallahi tsaf zai sa bindiga ya tashi kanki kici gaba mu ƴan kallo muke ko Abba be isa ya yi magana ba akan hukunci da Dady ya yanke ba amma ga fili daga ke har Aunty duk wata matsala daga gurinki take tasowa."
Gaba ɗaya falon shiru sukayi ba wanda yake ƙwaƙwaran motsi miƙewa yayi yafice numfashi Safna ta sauke "ni gobe zan tafi Tilde dan naji Ya Haidar yace zasu zo hutun ƙarshen shekara."
"Shine babban kuskuren da zaki aikata wallahi makaranta fa ki tafi Allah ya baki sa'a."
"Ya Lukman ya zanyi to nasan bazan iya ɓoye ƙiyayyar da nakewa waccen almajirar ba."
"Gobe BBC zata dawo ki kiyaye."
Daga haka ya fice, washe gari Monday tun asuba Ayra ta tashi ta haɗa abin karyawa soyayyar doya tayi da tea a gurguje tayi shirin makaranta ta fito shar da ita sai zuba ƙamshi take yi a falo ta sami Mamy "an fito kenan?"
"Eh Mamy yau zamu fara lesson fa kinsan ƙarshen watan nan zamuyi jarabawar fita."
"Kaga ƴan mata anata murna za'a fita agama saka uniform."
"Allah Mamy duk inata missing ɗin boarding."
"Naji ƙarfe nawa zaku taso?"
"Zamu kai biyarfa."
"Kash gaba ɗaya na manta gashi nayiwa Hajiya Rukayya alƙawarin yau za'a kai mata turaren nan tana ta damuna da kira."
"Ba damuwa zan dawo hudu sai kiyiwa Baba Iliya magana idan na dawo sai ya kaini amma ki gaya mata bazan daɗe kice aiki nakeyi dan na tsani wannan tasa ɗanta ya dawo dani."
"Naji sarkin zance jeki kada ki makara."
"Baki bani kuɗin abun hawa ba."
"Jeki ɗauka."
Ɗakin Mamy ta shiga tazaro dubu ɗaya "Mamy sai nadawo."
"Allah ya kiyaye a dawo lafiya."
A hankali take tafiya tsayawa tayi tan ƙarewa babban compound ɗin kallo mai ɗauke da danƙara_danƙaran motoci na alfarma babban gidan dake gefen daman ta, ta kalla duk tsaruwar gidan Abba Abdul wannan yaci ubansa duk da gaba ɗaya ana kiran sa da *TILDE MANSION* amma a ganin ta waccen dake rufe shine mansion dan tsaruwa da kyan sa sun wuce Misali a hankali taci gaba da takawa dan sosai gidan yake ɗauke mata hankali duk da ƙyale_ƙyale baya ɗaya daga cikin abinda take so saida tasha tafiya sannan ta sami abin hawa koda taje har angama assembly clss ɗin su kawai ta nufa kusa da ƙawarta Hafsah ta zauna "baby waike me yasa kullum sai kin makara."
"Kinsan unguwar tamu ba'a samin abun hawa sai nafito babban titi."
"Nikam kina bani mamaki duk motocin dake gidan ku amma sai kin hau tixe haba."
Murmushi kawai ta sakar mata ta mai hankali akan karatu ƙarfe huɗu ta dawo kamar yanda ta gayawa Mamy wanka tayi taci abinci "Mamy kawo aikan naje nadawo kafin magariba."
"Bazaki bari sai gobe ba ko kawai na bawa Iliyan ya kai mata."
"Shikenan wallahi kin hutar dani Bara kawai naje zuwa karatu."
***
A kwana a tashi a yau Ayra ta gama jarabawar ta cike da farin ciki ta nufo unguwar su tana isowa layin su taga sojojin dake gadin gidan sun ƙara babu ko ɗaya da ta sani a cikin su hanata shiga sukayi tun sha biyu na rana take a tsaye gurin har biyu tayi ko kaɗan bataji ranta ya ɓaci ba dan tsananin ƙaunar da take yiwa soja dawowar Umar ne ya ganta "Aunty Aya me kikeyi a nan."
Gurin sa ta ƙara so "Ya Umar sun hanani shiga ne basu sanni ba."
"To kuma sai ki zauna a nan aida kince sukira ciki su sanar."
"Bakomai ai inason su ne."
"To shigo mushiga waɗan nan sojojin Ya Haidar ne Dady bai ƙara so ba aida layin nan baya shiguwa."
Shiga tayi gaba "inason sojoji sosai dama shima dady soja ne harda Ya Haidar ma."
Murmushi yayi "duk son soja ne haka yau aketa min magana ah lallai kina son kaki."
"Ya Umar a ƙauyen mu Matar Soja ake kirana dan ina son soja nifa bazan auri wanda ba soja ba."
"Kice na janye kenan nida nake tunanin na yi mata ashe ban samu."
"Kai Ya Umar ina zan kaika kafi ƙarfina bayan ma Mamy ta gaya min auren ka za'ayi kaida Aunty Salma."
Murmushi ya saki yana kashe motar buɗe motar tayi "Nagode Ya Umar."
Daga haka ta fice tana ƙarewa sashen kallo yau kam an buɗe shi ga wasu sojoji a bakin get ɗin shiga shagala tayi da kallon su har ta tashi faɗuwa riƙota akayi a mugun firgice ta waigo ta zuba masa manya idanun ta kyakyawar halitta da tagani ya saka ta kasa ɗauke idanun ta a kansa ganin taƙi daina kallon sa yasaka shi sakin ta jikake tim wata ƙara ta saki ko gizau beyi ba sai tafiyar sa da ya cigaba da yi aiko taji haushi tayi ta zunduma ihu Iliya direba ne ya matso kusa da ita yace "ke ƴar gidan Mamyn Zakiyya ki rufa mana asiri idan baso kike yasa a zane ki ba dan mai gida Aliyu ya dawo wallahi zakisha mazga tashi kinma ci sa'a be tsinka miki mari ba ba'a kallon sa."
"Waye shi hakan?"
"Tashi ki wuce ciki idan baso kike kija mana matsala yana iya korata."
Kamata yayi ta miƙe saida ta kaɗe jikin ta bayan ta mugun ciwo yake mata tana taka ƙafa taji hips dinta yana mata ciwo aiko wani sabon kuka ta saki Iliya na ganin haka ya lallaɓa ya gudu tana tafe tana gunji kuka kamar wacce aka yanka abin baƙin ciki ba wanda yake kulata duk da ga masu aiki sunata kai kawo daga maza har mata babu me kulata har ta ƙarasa sashen su kallon ta Mamy ta tsaya yi "ke lafiyar ki kukan me kikeyi?"
"Wani baƙo ne ƙato yanada tsawo kamar fal waya mai ƙirar samudawa ya kayar da ni yayi tafiyar sa kuma yanada kyau amma ba ɗan gidan nan bane ko?"
"Amma tambayar ki nayi kika tsaya zuba ko."
Baki ta turo tana mirza ida mu "ki kama kanki Haidar ya dawo bana son naji wani abu ya fito daga gareki."
"Kinsan bana shiga sabgar kowa a gidan nan sai ta ƙawata."
"Aiko inada tabbacin kune na farko da zakusha duka kije Hajja ɗazu tazo wai kije kimata kwana biyu."
"Yau kuma abin ya motsa kenan kaƙi zuwa ace maka me baƙin hali kaje kuma ace bakaji idan ka kama kanka ace maka munafuka."
"Idan kin gama kije kiyi wanka ki fice bana son ta sake zuwa tace dan ba ita ta haifi ubanki bane na hanaki zuwa......."