Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Gt2q0QWZkoO0MpK7tbcbwZ
MATAR SOJA
AREWA WRITER'S ASSOCIATION💦
Book oneRashma
Page five
Free page
Wani soja ya ɗauki Lukman ya mayar da shi bakin ƙofar falon Aunty inda take tsaye "kashigo dashi ciki mana bazan iya ɗaukar sa ba."
Ko kallon ta baiyi ba yayi tafiyar sa "shegu masu baƙar zuciya, kai kuma tashi zakayi na kama maka kashiga ciki."
"Mushiga ciki kinga ya sako karen nan nashi wallahi ubankowa bazai bari ba tunda kinji yace kowa."
"Dama haka yake da zuciya amma na tausaya miki Rash sai kin dage sosai."
"Ayra ni kaina ina jin tausayin kaina amma naji Aunty tace ubansa ya gado da kakarsa itama bata ɗaukar raini amma wallahi ina cikin farin ciki yau nice na dakatar da Ya Haidar kuma yana cikin fushi."
"Yanzu ya kamata ki fahimci wanene mijin da zaki aura bawai sai kin shiga ba kita samin matsala kinganni nan inada burin auren soja harma matar soja ake kirana a gida ana tsoratar da ni cewa zan sha duka da masifa to sai na nuna musu cewa mace fa mace ce saina takashi wallahi saina mayarda shi abin kwatance."
"Cab wannan irin buri haka amma kinsan wani soja baya takuwa ko kizo mu auri Ya Haidar to."
"An gaya miki banda nawa inada my Soja yana cen gida."
"Inye ƴar gari kice zamu sha biki har sojan nan yabani tausayi."
Murmushi tayi tana fari da idanu a falo suka sami Hajja tsaye "kai me yake faruwa ne a gidan?"
"Me ya hanaki kifi ta ki gano halan sai gulma."
"Ke kam anyi ƴar iskar yarinya me shegen baki."
Wayar ta taɗauka "me zakiyi naga kin ɗauki waya?"
"Me za'a fasa Abba zan kira na gaya masa gidan sa anyi rasuwa."
"Waya gaya miki ya rasu ne meyasa ke komai a bakin ki akejin shi."
Ko tsayawa sauraren Ayra batayi ba ta danna masa kira bugu biyu ya daga "hello Abba Allah yayiwa Ya Lukman cikawa."
Tana fadin haka ta rushe da kuka sai yanzu take jin zafin abin "ke kinutsu ki gaya min me yake faruwa ne?"
"Kayi sauri kadawo dai."
Wayar ta sauke tana sharar ƙwalla zaune Hajja ta kai tana sharar hawaye da majina "Allah sarki Lukumanu na ka tafi ka barni wayyo mutuwa baki min adalci ba."
Ayra dai tana tsaye sai kallon ikon Allah takeyi wata wayar ta sake kira "to gantalale sarkin yawo wallahi duk inda kake ka dawo dan dan Bature ya dawo yanzu haka yayiwa ya Lukman duka saida ya mutu."
"Ke dan manzo Allah dagaske ko wasa kike mani."
"To katsaya kuma ya zo da wannan karen nasa yanzu haka ya sake shi a compound kuma kasan ba baccin dare yakeyi ba duk wanda ya shigo yana kallon sa."
"Nashiga uku yanzu ya zanyi?"
"Kuma idan baka kwana gida ba jiki magayi.""To shi Ya Lukman me yayi yasha na jaki har ya rasu anya ma ya Mutun dagaske nasan halinki."
"Na maka ƙaraya kar kadawo mafita ɗaya ka kira Abba be dawo ba."
"Ƴar nan waye ya rasu kamar zancen mutuwa nake jin anayi kuma naji kince dan Bature waye haka?"
"Wai Inna dama bakiyi bacci ba "Ya Haidar ne ya daki ya Lukman."
"Waye kuma Haidar a cikin zuri'ar mu muke da mai wannan sunan?"
"Inna Aliyu fa ɗan Dady Ibrahim."
"Waye shi Ibrahim ɗin." "Inna nafa America nake magana."
Mtsww "to me ya kawo shi a cikin zuri'ar mu ana zaune ƙalau wani sharrin ne ya kawo shi dan duk inda yahudu da nasara suke babu zaman lafiya kira min Audu ko Yusufa yanzu nan bazan kwana guri ɗaya da arna ba."
Taɓe baki Rashida tayi sai can kuma ta saki murmushi "yawwa Inna wai me mom tayi ne haka da zafi ina son naji tarihin abinda ya faru a baya."
"Ba labari ne mai daɗin saurara ba bare kiso kiji manta kawai yanzu ki kiramin Yusufa dan shi kaɗai ne yasan zafin da nakeji."
"Zan kirasa amma ki fara bani labari tukunna sai na kirasa."
Nisawa tayi ta fara goge hawayen da suka zubo mata sannan ta fara cewa "Alhaji Abubakar Tilde shine cikakken sunan mahaifin mu muna kiransa da Alhaji mu ƴan asalin Bauchi ne amma muna zaune a Tilde maihaifin mu yanada dukiyar dabbobi da gonaki mu uku kacal ya haifi sai ƙanin sa wanda yake da yara sama da goma muntaso cike da ƙaunar junan mu amma mahaifin mu yafi son Zainaba gata nan Hajja duniya bayada wanda yake so kamar Zainaba komai itace babu mai ikon taɓa ta yana matukar tausayin ta saboda lalurar da take da shi na makanta yayanmu Shafi'u yana matuƙar jin haushin abinda ake mana na banbanci a tsakanin mu wanda nima haka ne wata rana Babanmu yayi baƙo daga Habuja babban soja ne yanada kuɗi sosai wai a gurin aikin hajji suka haɗu a nan yaga Zainaba yace yana sonta Babanmu yayi matukar jin daɗi har farin cikin sa ya kasa ɓoyuwa nan take ya kira mu yana gaya mana nan take nacewa baƙo makauniya ce fa dan ba ƙaramin zafi naji ba amma ga mamakina sai naga yayi murmushi yace ai ya sani daga lokacin ban sake cewa komai ba bayan kamar wata daya akayi bikin su wanda naga nera inda take hmm nida yayanmu Shafi'u bamuyi murna da auren nan ba shekarar su ɗaya da aure lokacin tana da yaro ɗaya Sufiyan aka kawowa masa farmaki a nan ya rasa ransa a lokacin Zainaba tana gani dan ya kaita anyi mata aikin idon ta dawo gida da kamar wata ɗaya mahaifin mu ya kwanta ciwo saida ya kwashe wata biyu a kwance wata rana wacce bazamu taba mantawa ba Baba ƙarami ƙani ga mahaifin mu kenan yazo ya sami Baba da maganar Ishaƙ yana son auren Zainaba wannan kawai mukaji baba ƙarami ya kore mu bamu san me ya faru ba sai kawai mukaji kukan Baba ƙarami wai Baba ya rasu hmmm a ranar munyi kuka barinma Zainaba abin mamaki kwana bakwai da rasuwar Baba a ranar aka ɗaura auren Zainaba da Ishaƙ dangi mahaifin Sufyan suna jin auren ta suka zo suka ɗauke shi kowa yasan Ishaƙ baya jin magana babu wanda ya isa ya gaya masa magana Zainaba ta kasance shiru_shiru ba maison magana bace mu munsan cewa yana cutar ta rana tsaka Zainaba tace a raba gado abata nata yayanmu yaso yaƙi amincewa amma sai Baba ƙarami yace abata haƙƙin ta haka aka raba aka bata nata kuɗin ta ɗauka duka har na gadonta da ta karɓo na mahaifin Sufiyan duka ta haɗa masa wai kasuwanci zaije Lagos yayi wata ɗaya da tafiyar sa ya dawo mana da baturiya soja dan ranar ma tare da yaranta sojoji take tana sanye da kakin ta tunda tasaka ƙafa gidan babu wanda ya sake tari idan kayi wani kuskure zata sa yaranta su zane ka amma duk duniya babu wacce take so kamar Zainaba lokacin tana da ciki sai ta kasance tamkar itace mijin ma wata uku sukayi ta tattara ta koma da ita da mijinta aka bar Zainaba da ciki babu ci babu sha ba sutura sai tayi surfe sannan zata ci ga Yayanmu ya tattara dukan dabbobin mu yatafi kiwo Baba ƙarami kuwa ya handame gonaki gaba ɗaya yace ya saida yayi biyan bashi muna cikin halin rayuwa wata rana da dare Zainaba ta tashi da naƙuda a walce ta haifi ɗan ta namiji Abdulkarim kenan har tayi sati biyu da haihuwa ba labarin Ishaƙ gashi Baba ƙarami yaƙi ya yankawa yaro rago kuma munsan yanada shi babu mai kula damu Innar mu dama ta daɗe da rasuwa mukɗai muke rayuwar mu jinjirin ma sai kayan Sufyan ake saka masa haka zamu zauna muyita kuka nida ƴar uwata tanada sati uku ishaƙ yadawo tare da matar sa a lokacin yanada wata takwas rabon sa da garin matar sa tafi shi murna da ganin jinjirin idan kika ganshi yayi ƙiba yayi ɓul_ɓul dashi yayi jajir dashi ya ƙara wani irin kyau a lokacin ne nasame shi da maganar aure na amma nunawa yayi shi bayada kuɗin da zemin aure naje na sami Baba ƙarami shima cemin yayi bayada kuɗi nadawo na sami ƴar uwata na gaya mata kuka mukaci sosai..........