Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Gt2q0QWZkoO0MpK7tbcbwZ
MATAR SOJA
AREWA WRITER'S ASSOCIATION💦Rashma
Book onePage One
Free page
..........sosai ta shagala da aikin da takeyi tana juya ƙugu tana juya miya tana waƙa a duniya rana masifar son waƙar gashi bata ma gama haddace yanda take ba wani juyi tayi da ludayi miya a hannun ta "ahayye sama kuɗi ƙasa kuɗi mata irin mu wane yaro mata dan kashe kuɗi akayi mu, mu rausaya mu jijiga ƙugu, mu durƙusa mu kwaso nera inba kuɗi kakoma gefe...."
"Mtsww ƴar matsiyata kwaɗayayyu ahaka za'a ƙare gurin karuwanci."
Murmushi ta saki mai sanyi wanda hakan ɗabi'arta ce ka zageta ta mayar ma da murmushi "Aunty Safna mekuma nayi da zafi haka amma kiyi haƙuri."
"Zanci ubanki me na haɗa dake da nazama Aunty ki bana son kalan dangi kishiga hankalin ki wallahi dan ƙiris nake jira nasa ki bar gidan nan munafuka ni narasa me Abba Abdul ya gani ya kwaso mana ƴar ruga har tazo mana da sadakar yalla gida ai bari Dady ya dawo sai kunbar gidan nan."
Juyawa tayi taci gaba da aikin ta har Safna ta gama ta fice bata tanka mata ba amma tana jin ranta yana mata wani irin zafi a duk lokacin da yaran gidan suke musu irin wannan zagin uwa uba masifar Hajja ta ishesu wani lokaci takanji kamar ta koma ƙauye ta huta da wannan irin musgunawar da suke sha ba ita ba har ƴan ƙannen ta suna karɓar rabon su har ta gama aikinta duk wani farin ciki da take ciki ya gudu fito tayi tana sauke numfashi dan ba ƙaramar wahala taci ba dan duk ranar girkin mamyn ta hana ƴan aiki ake yi suyi girki sai su keyi to yau mamy bata jin daɗi hakan ya saka ita kaɗai tayi aiki tana jin bayanta kamar ya ɓalle sashen mahaifiyar ta, ta nufa dan bata isa ta shiga sashen ƴan matan ba duk da akwai sa'anin ta amma zama sashen mamy yafi mata kwanciyar hankali ruwa ta watsa sannan tayi shirin islamiyya duk da gajiyar da tayi da so samune ta sami guri ta kwanta amma ita tasan bata da wannan damar babban gatan da zatayi wa kanta shine ta sami ilimi domin kuwa shine kawai zai haska mata duniyar ta shigowar ƙanin ta Saif shi ya katse mata tunani "Aunty Aya kijo inji mamy."
"Ai kane Aya nace ka daina cemin Aya bakaji ba Aya ba gyaɗa."
Dariya yahau yi miƙewa tayi daga shafa man da take yi tabi bayan sa a guje "Mamy kinga Aunty Aya zata dukan miki autanki ko."
Bayan Mamy ya ɓuya da take tsaye tana jiran ta "kai haba wai kekam yaushe ne zakiyi hankali ne wai ƙatuwar budurwa amma har yanzu hankali bai zina."
"Mamy Aya fa yake kira na kuma na gaya masa bana so."
"Yooo badole yace Aya ba duk wani iyayi ne abar mutum da sunan sa amma ina wai zamani ina ai ba iya faɗa nayi ba ai Ayan yafi daɗi da sauƙin."
Ƙafa ta fara bugawa tana kuka shagwaɓa Mamy da Saif sai dariya suke mata "wallahi bazan siya maka abinda nace zan siya ba."
Da sauri ya fito yazo gaban ta ya kama kunnen sa "a'a Aunty Ayra wallahi nadaina kiyi haƙuri kinji balan ƙara ba kiji sweetheart."
"Kinga zo kikaiwa Hajja turaren wutar nan idan kindawo kwaci gaba."
"Kai Mamy kibawa Saif mana ya kai mata yanzu ina zuwa zata ce nayi mata wani abun."
"Ke nace kije kikai mata idan kuma bazaki je ba sai naje da kaina."
Juyawa tayi ta koma ɗaki ta sako hijab ta fito kwando da turaren yake ciki ta ɗauka ta fice a hankali take tafiya cike da sanyita da nutsuwa Ayar yarinya ce da batada hayaniya ko kaɗan ga miskilanci idan kaji tana magana to tare take da Mamy ko ƙannan ta, haniyar da taji a sashen na Hajja yasaka ta lumshe idanu ta tsani kallon da matasan gidan ke mata musamman Mus'ab a hankali tayi sallama
"Sai yau nake ganin ki mai fuskar munafukai kina wani noƙewa kamar ta Allah."
Murmushi ta saki tana cewa "haba Hajja kiyi haƙuri kinsan makaranta ke hanani shigowa wani lokaci kuma aiki."
"Duk ma'aikatan gidan nan basa aiki kenan sai kinyi kaji wani salon munafunci."
"Ai idan batayi ba ita ɗin ba jinin Sa'adatu bace."
Cewar Salma da take zaune a ƙasan kafet tana cin soyayyar aya, wani irin bacin raine ya ziyarce "Aunty Salma ina ganin girman ki baki cikin mutanen da nake fatan girman su ya faɗi dan ko wani ya nemi cin zarafin ki wallahi sai inda ƙarfi na ya ƙare kada ki ɗauki halin da ba naki ba zan iya kawar da kai akan komai amma karku taɓa min Mamy na."
Duƙawa tayi ta ajiye turaren "gashi Mamy tace na kawo miki."
Juyawa tayi ta fice taji an fisgota bata gama daidaita tsayuwar ta ba taji wani irin lafiyayyan mari saida falon yayi shiru na wani lokaci buɗe idanun ta, tayi da suka koma jajir tana kallon Aunty Safna da tayi marin murmushi ta sakar mata tajuya har takai bakin ƙofa sai ta juyo tace "Jamcy idan kuka saka na makara keda Saif saina fasa siya muku abinda nayi alƙawari dan naga bakida niyyar zuwa islamiyya."
"Kai Aunty Aya na shirya kaya kawai zan saka sai na riga ki fitowa."
Ƙugu ta riƙe tana hararar yarinyar da take dariya "kuci gaba zanyi maganin ku kiyi sauri ki gayawa A'isha da Bahijja ku fito muje idan na makara aka zane ni sai na rama akan ku."
Daga haka ta fice wasu hawaye ne masu zafi suka sauko mata"ni narasa me yake damunku ne wallahi me yarinyar nan ta tsare muku ne wai ke Safna kishiga hankalin ki duk ranar da Yaya Haidar yasan abinda kikeyi wallahi kashinki ya gama bushewa bare kuma yaje kunnen dady wallahi kin kaɗe har ganye ki."
"Nashiga uku na dan girman Allah ka daina haɗani da waɗan nan mutanen."
"Wallahi ajiye wannan son da suke miki zasuyi a gefe suci ubanki barin ma dady da baya ɗaukar raini kinga dai Rashida BBC bata nan ko hmmm zakisha mamaki idan ta dawo ta sami abinda kikeyi duka_duka yarinyar nan batafi wata biyu da dawo wa nan ba amma kunsaka mata karan tsana."
"Gaya mata dai Lukman tunda ni sun mayardani shaka tafi."
Miƙewa Salma tayi "ai nikam bazan sake shiga shirgin shiriritar nan dan ta fuskance ni ta gaya min gaskiya a matsayina na babba dama ban taɓa kula irin waɗan nan abubuwan."
Ɗaya bayan ɗaya duk suka watse, da dare suna zaune tare da ƙannen ta biyu Saif da Zakiyya ita har ta manta da abinda ya faru tana zaune tana taya Zakiyya home work saiga Mamy ta shigo ranta a ɓace "da na aike ki gurin Hajja shine kika je kika jamin magana to kije ana jiranki babban falo."
"Allah Mamy ba abinda nace mata kuma ai da ta mareni banko ce mata uffan ba ."
"Ban tambaye ki ba dan baki gaya min ba da farko kije."
Hijabin ta, tasaka jikin ta duk yayi sanyi idan akwai abinda ta tsana shine taga bacin ran Mamynta har takai babban falo wanda ya kasance na Abba Abdul saida aka bata izinin shiga sannan har ƙasa ta durƙusa "Abba ina wuni ya aiki andawo lafiya."
"Lafiya lau Mamana ya makaranta malamin ku ya kirani ɗazu yake cemin kinhaɗa hardarki nace ashe babbar malama ce uwata tunda kin hardace mai girma."
Murmushi tayi ta dukarda kanta ƙasa "Mamana me ya haɗaki da Aunty ki?"
Shiru tayi na wani lokaci sannan tace "kayi haƙuri Abba bazan sake ba."
"Ji wani salon munafunci ke a dole ta Allah ana tambayarki kina bada haƙuri sheg..."
"Ya isa Hadiza badake nake magana ba ina a gaban ki ita Safnar tazo ta gama faɗar duk abinda yazo bakinta."
Juyowa yayi kan Ayra "tashi kije Allah ya miki albarka yabaki miji nagari."
Miƙewa tayi tana rufe fuskar ta da hijabinta saida ta fice sannan ya kalli Aunty da take ta cika tana batsewa "kija girman ki a gurin yarinyar nan bana son kina shiga wannan faɗan na yara."
"Aidole zakace haka tunda ba ƴata bace ƴar waccen bararojin ce komai sai ka nuna rashin adalci kaji tsoron Allah Abdulkarim yanzu agola tafi ƴan gida daraja da ƙima........"