MATAR SOJA
Book one
Rashma
AREWA WRITER'S ASSOCIATION💦
Page Three
Free page
"Amma dai za'a bari naci abinci na huta sannan ko?"
"Karkije ki zauna ki gani yau idan ba sai an haɗa mana taron kanmu ba."
Tafiya ta fara tana cewa Allah na gani bana son tashin hankali amma da kaje sai anyi kuma wai har kwana biyu."
Mamy najin ta amma uffan ba tace mata ba sai ma kicin da ta shiga wanka tayi duguwar riga ta saka ta atamfa kum da mai ta ɗauko ta fito falo bata sami Mamy ba sai ta haura sama nan ma bata falon saman ɗakin ta tashi a zaune ta same ta waya a hannun ta fuskar ta da ɗan damuwa "Mamy lafiya me yake faruwa ne?"
"Bakomai ya akayi ne?" Zama tayi kusa da ita ta dafa ta "Mamy ki gaya min me yake faruwa ne nasan bazai wuce matsalar gidan mu ba ko?"
Numfashi ta sauke "Ayra baffanki ne ya kira ni wai akawo ki aure za'ayi miki da ɗan uwanki Bello maja."
Da sauri ta miƙe tsaye Allah ya sawwaƙe wallahi dawa za'ayimin auren da wannan ɗan iskan bayan inada wanda nake so kema kinsan shi wallahi bazan aure shi ba sojana zan aura."
"Ke auren nema a gaban ki ba karatu ba nida nake da burin kiyi karatu kizama wani abu amma ke har yanzu kina tare da wannan sojan."
"Mamy abinda kika sani ne kowa ya sani yarinya bata wuce shekara sha hudu anmata aure ni yanzu gani da shekara ashirin ai gani suke na gama tsofewa a gida kice masu akwai bikin da ake yi idan angama zaki kawo ni amma maganar gaskiya bazan auri Maja ba saidai su saka min fetur taje mun kaina naje gurin Hajja."
Numfashi ta sauke ta karɓi kum ɗin ta fara taje mata dogon gashin ta da yake a cike "ke ni wannan gashin naki ya ishe ni gobe sai muje saloon a wanke shi ko yana rage kauri."
"Wash Mamy zafi kiyi a hankali."
Bata bi ta kanta ba saida ta taje shi da kyau sannan ta ɗaure mata fuskar tayi jajir ga hawaye sun wanke mata fuska "tashi ki bani guri raguwa sai girma da shekaru amma ba jarumta naso ganin yanda zaki haihu ki ɗauki abinci yana nan kice abawa baƙuwa."
Fita tayi tana share hawaye bawai na taje kanbane harda na maganar wai aure za'ayi mata tasan cewa Khalid ɗin ta bai tashi aure ba kuma tasan wannan karon babu yanda za'ayi ta kuɓuta dayaya ta samu tazo nan domin ta ƙarasa makarantar ta hawaye ta sake sharewa hijabin ta tasaka sannan ta ɗauki kayan abincin ta fice a nutse take tafiya hankalin ta gaba ɗaya baya jikin ta mafita kawai take nema ta kusa shiga get ɗin da zai sada ta da part ɗin Hajja taji an dafa ta a firgice ta waigo "haba Rash wallahi jarkin tsorata ni."
"Ke kuma sarkin tsoro inata ƙwalla miki kira amma baki jiba me kike tunani ne haka naga duk kinyi wani iri."
"Ba komai ƙawata kawai dai Mamy ta taje min kai ne kuma ta ɗaure sosai shine yake min zafi."
"Ayya sorry besty, ke Ya Haidar ya dawo ɗazu ba wanda yasan yau zai dawo yau akwai casu kinganni tunɗazu nake zaune waje domin naga wanda za'a fara cin ubansa kizo mu zauna."
"To muje mukaiwa Hajja sannan mudawo."
A tare suka shiga suna ta shewa "Ayar Ina matuƙar son Ya Haidar amma shi ko kallo ban ishe shiba ƙanwar sa kawai ce a gaban sa."
"Ai tunda ba ita zai aura ba kawai ki kwantar da hankalin ki sai ya soki da yardar mai sama insha Allah."
"Banga alama ba wallahi dan ko yana sona uwarsa bazata bari ya auri ƴar Nigeria ba ai zasuzo tare da dady da Ya Alim zaki gansu kinsan mahaifiyar dady baturiya ce to shima baturiya yake aure."
"Ta yaya hakan ta kasance kuma gaku fulani amma ƙanin Abba bature."
"Kai ɗan fari wawa ce miki nayi mahaifiyarsa ce baturiya."
"Meye kuma ake kira mana annasara rana tsaka "Hajja labarin wani fim da na kalla ne nake bata ko Ayra?"
"Eh haka ne ." "Kudai kuka sani da muna funci ."
"Hajja ina wuni gashi Mamy tace nakawo abawa baƙuwa."
Washe baki tayi tana dariya "kai masha Allah Abulele kice angode, ai takusan ma isowa kuzo kuje kasuwa ku siyo mata zogale."
"Ke kiji wani rikici dan Allah a nan garin Lagos a ina za'a sami wata zogala kinma taɓa ganin munje kasuwa bare ki aike mu akan tsamurarriyar tsohuwar nan ai yanzu shikenan tunda zatazo duk wani tsuguri tsoma za'a fara shi da tashin hankali duk wani ƙulli zakaji daga gare ta yake."
Baki sake Hajja take kallon Rashida ga hawaye sun wanke mata fuska ni kike ciwa mutunci mu kike kira matsafa yau sai ubanki ya zaɓa koni ko ke yau bazan kwana a gidan nan ba ke Abulele kirawo mini Audu."
"A'a Hajja kiyi haƙuri dan Allah basai ankira Abba ba dan Allah."
A sheƙe take kallon ta "ni zaki gayawa magana tun kafin a haifi uwarki nasan haƙuri yau idan Aliyu be sauke ƙurar Amurika da ya kwaso ba hegiya nike."
A zafafe ta lalibo wayar ta tafara neman number da zata kira sai hijiga takeyi ta riƙe ƙugu kamar yarinya "hello Audu kana ina duk inda kake kazo gida ina son ganinka."
"Ba Audu bane ɗan sa ne kije ki nemesa."
"Ai Lukumanu ne to ka kira min shi."
"Bazan kira ba ai kinada number ɗinsa."
Daga haka ya yanke kiran da kallo tabi wayar "yara duk basa tsoron Rabbu duk sun lalace sun zama ƴan tasha."
Kuka ta kuma saki tuno abinda aka faɗa akan ƙanwarta "wallahi sai Allah ya saka miki Bintu."
Mayafinta ta ɗauka ta fito tana ta sharar ƙwalla "Hajja dan Allah kiyi haƙuri kawo wayar na kirasa dan Allah karki fita."
"Ki barta ta fita mana idan aka sace ta ko aka yanke kanta ubanwa zai damu nidai ko kuka bazanyi ba da ba wanda ya akeki fita."
Takalman ƙafarta ta cire "wallahi anyi asararriya idan aka yanke kan nawa sai abiki idanun kici mayya shegiya mai siffar arna."
"Inci idanun ki ince naci me ido duk kwantsa da ruwa masu ɗoyi."
Hannu ta ɗora aka tashi ga rusa kuka "Hajja dan Allah ki daina kuka Rash Please mana kidaina mana idan Abba yazo bazakiji da daɗi ba dan Allah ki daina mana."
"Ke rabu da wannan mai siffar tsofaffin Aljannu batajin lallashi sai Audu yazo."
Ganin Abba a gaban ta ya sakata zaro idanun ta "Ab......"
"Idan na ɗauke ki da mari sai kinga mala'ikan daukar rai uwar yawa ce ta zama abokiyar wasanki."
"Abba kasuw fa tace zata aike mu."
"Ko birnin sin tace zata aike ku bazakije ba kenan."
"Rabu da ita Audu yau gidan zan bari gara na koma Tilde da na zauna yaranka duk sunraina ni basa ganina da ƙima."
"Hajja dan Allah kiyi haƙuri duk bai kai can ba bari na kira Haidar kisa ya hukunta su yanda ranki yake so."
"Ashe Audu bakada imani jikokin nawa zaka sa wanccen gardin ya hukunta su yanda nace bana son ganin sa daga shi har ubansa haka ban yafe ya taɓa min jikokiba indai ina raye fice ka bani guri lalatace marar zuciya."
Kansa ya dukar ƙasa yana mayar da hawayen sa da suka cika masa idanu miƙewa yayi "Allah ya baki haƙuri Hajja zan koma office muna meeting ne Lukman ya kirani."
Shiru tayi bata tanka masa ba hakan ya saka shi ficewa jikin sa a mace duk duniya rashin hadin kan danginsa yana ci masa rai kuma duk laifin Hajja ne da taƙi sakin abu a ranta shekara da shekaru amma taki ta manta tana kallon al'amarin kamar yanzu akayi shi har ya kai nashi ɓangaren yana wannan tunani kaya ya cire dan ya watsa ruwa ko zuciyar sa zata sake masa shigowar Mamy ne ya tsaya yana kallon ta har ta ƙara so Sweetheart lafiya ka dawo yanzu ko mantuwa kayi?