MATAR SOJA
AREWA WRITER'S ASSOCIATION💦
Book oneRashma
Page four
Free page
Ya sakar mata murmushi "ina fatan haka Habiba bara na watsa ruwa na koma Company namu yau a rike ce yake rikicin Hajja ne ya dawo dani babu shiri."
Murmushi ta saki "ayita haƙuri da Hajja ai ɗazu zuwa tayi Ayra taje ta mata kwana biyu."
"Al'amarin Hajja kamar yarinya abu gida ɗaya amma take roƙon azo amata kwana kuma akan su ne ta taso ni ina tsakiya da aiki Lukman ya kira ni wai naje uwata aljannun ta sun tashi wallahi abun ya mugun tsorata ni na fito babu shiri dama waccen akun ta kira ni wai Hajja zata aike su kasuwa."
"Aljannu fa ita Hajjan take da wasu aljannu?"
"Iskanci Lukman ne fa, zo kimin wanka na samu na koma na ƙarasa aikina kafin wancan jaririn ya iso ƙasar."
"Dady ɗin ne jariri?"
"Miye banbanci sa da jariri."
A tare suka shiga wanka sun jima a ciki sannan suka fito itama saida ta sake wankan "dama haɗa baki kikayi da Hajja ta koro miki ni kizoƙe min ruwan jiki ko."
"Banda sharri kai zan cewa haka neman hanyar dawo wa gida kake yi ai kayi na sati ɗaya ingaya ma."
"Zancen kike so ki shirya yau bake ba bacci."
"Bama zan kwana nan ba guduwa zanyi."
Kayan da zai saka ta ciro masa taya shi sakawa take yi suna fira wayar sa da ta ɗauki tsuwa yasaka janye jikin sa daga nata wayar ya ɗauka "hello ya ake ciki an sami wani haske kuwa?"
"Eh ranka yadaɗe yanzu haka ma ga takardun a hannuna."
"To Alhamdulillh gani nan yanzu zanzo."
Daga haka ya yanke kiran "me yake faruwa ne?"
"Bara naje nadawo sai muyi magana."
Rungume ta ya ƙara yi turare ta sake fesa masa da sassarfa ya fice ta bisa da kallon mamaki ɗakin ta fara gyarawa, sosai yake jin daɗi dan ba ƙaramin matsala Company zata samu ba suna isa ya ɓalle ƙofar ya fito baima jira a buɗe masa ba da sauri yake tafiya kaida gani kasan ba'a natse yake ba koda ya isa office nashi a bakin ƙofar shiga ya sami Lawal yana jiran sa "shigo mana."
Shiga sukayi takardun ya karɓa saida ya gama dubawa sannan ya ɗago kansa ya kalle sa "a ina aka gansu?"
"Ranka ya daɗe sir Haidar ne yace mu sake shi kuma kada mu gaya ma komai zai magance matsalar bazata sake faruwa ba."
"Ya akayi Haidar yasan cewa takardun su ɓata?"
"Ai duk abinda yake faruwa a cikin Company ɗin nan yasan dashi wani abu nida nake ciki ban sani ba sai ya gaya min."
Murmushi Abba ya saki wanda ya ƙara wa dattihuwar fuskar sa kyau da annuri "shikenan kana iya tafiya."
Yana fita Abba ya janyo wayar sa wata number ya nemo wacce aka rubutawa *Rayuwata* ya jima yana kallon number sannan yayi kira bugu ɗaya aka ɗauka wata murya ta bayyana mai kauri da amo ta furta "Assalamu alaikum *Rayuwata* da fatan kana lafiya."
"Ina lafiya Ibrahim ko Abraham zance."
Ya faɗa yana mai sakin murmushi"yaya ka fara ko kasan Mom kaɗai take kirana da wannan sunan."