Suwaye ‘Yan Gidan Gwaiba?Gidan Gwaiba babban gida ne a Tudun Jukun dake garin Zaria. Ya k’unsa sashe da dama kuma akwai itatuwan gwaiba wanda gidan ya samu sunarshi, gashi duka ‘yan uwa ke zaune a ciki.
A cikin gidan akwai wani sashe ta ɓangaren hagu, Sashen Marigayi Alhaji Dhalhat wanda akafi sani da Alhaji Ango ya zauna kafin rasuwar sa.
Mutumin arziki da kamalansa kowa yana yabawa da halayyarsa, yanada da dattako gashi yasan darajan ɗan Adam kuma yana kare hakkin addini. Daya tashi aure sai aka bashi Yar Uwarsa Hajia Hadiza(Gwaggo Dija) which itama yar Gidan Gwaiba ce.
Kwanci tashi ba wuya wajen Allah, sunada albarkan yara guda 8, Bello, Safiya, Abubakar, Kabiru, Yusuf, Fatima, Rabi da Zainab
Babban ɗansu yana zaune a Cotonou inda ya shahara a saida gwanjuna, lak’abinsa shine Mallam Bello Gwaiba Mai Gwanjo. Sunar Matarsa Sakina kuma sunada yara Shida.
Akwai Abdullahi kuma shine ya gajeshi wajen saida gwanjuna. Sai kuma AHMAD shi kuma Boutique yake dashi. Abubakar, Adamu, Aisha, Hadiza da kuma auta ASMA’UL HUSNA.
Sai babban ‘yar Alhaji itace Hajia Safiya kuma tana auren wani ɗan kasuwa Alhaji Abdulaziz a cikin sabon gari dake Zaria. Yaranta guda takwas, Hadiza (Mami), Dhalhat (Baffa), Zainab, Sadiya, Ibrahim, Ummul khair, Salima da Abdulrahman.
Daga nan kuma sai Alhaji Abubakar Dhalhat Gwaiba, House of Representatives ne under Zaria LGA kuma yana auren Hajia Nana Fatima wanda malamar islamiya ce. Yaransu hudu, Bello, Sulaiman, SHEHU USMAN, Lukman.
Mai bin masa shine Alhaji Kabiru Dhalhat Gwaiba, yana koyarwa a Barewa college inda yake ɗaukan Biology. Matarsa itama malamar makaranta ne amma LEA Tudun Jukun take koyarwa. Saidai suna lallaba rayuwarsu ne saboda basuda wadata na kudi.
Yaransu bakwai saboda samsam basu tsarin iyali, akwai Mudassir, Bashir, Hanifa, Fadeela, Mufeeda, Samira da auta Aishat.
Alhaji Yusuf Dhalhat Gwaiba ke bin masa, a cikin Nigeria da kuma kasashe na k’etare kowa yasan da zaman shi. Shine 98th richest man a cikin Forbes kuma 10th richest African Man.
Watau shine mai Shahararren kamfanin nan mai lakabi da GWAIBA INVESTMENT, sun shahara wajen sarrafa auduga su mayar kaya. Sune manyan Dealers ɗinsu Vilisco, Hollandis dasu Da viva.
Kuma suma suna printing atamphophi masu suna Gwaiba Wax, kuma suna sarrafa materials kamar su Chiffon, cotton, valvet, leather da sauran su. Sunada kayan sai wance da wane ke iya daurawa a jikinta da kuma na saukin rahusa.
Kuma sunada hannun jari da dama a kananan kamfanoni masu neman tallafi kamarsu MTN, Julius Berger, Gidan Mai etc.
Matarsa Hajia Hussaina tana cikin Board Members ɗin Gwaiba Investment, ita tana under judicial department ɗinsu. Saidai ita yar Bama ce a jihar Borno watau ita asalin Kanuri ce amma batada haske payau. Cikin ikon Allah yaranta sune masu hasken.
Yaranta Shida kuma harda ‘yan biyu kuma sune haihuwarta na fari. NUWAIRAH da NAWWARAH kuma shekarunsu 21, Nabeelah 17,Naziru 15, Nafisa 13, Nusaiba 9 yrs.
Daga nan sai Hajia Fatima Dhalhat Gwaiba wanda ke auren Dr mannir kuma basuda yara saidai suna rike yaran Mallam Kabiru watau Bashir da Mufeeda tunda Kabiru bashida wadata sosai.
Hajia Rabi ke bin mata, itama tana zama a Lagos da Mijinta Alhaji Aminu Bakin kogi, yaransu Bahijjah, Rahma, Khalid, Maimuna da Ummu hani.
Barrister Zainab Dhalhat Gwaiba ke biye kuma itace auta. Tana auren Major Musa Muhammad, yaransu HUNAISA, Safina, Suhaila, Yusuf.
Wannan shine chronology ɗin yara da jikokin Alhaji Ango. Shi dai ya kasance manomi ne inda yake noma auduga, albarkacin gonarsa yana bunk’asa kuma dashi ya saka yaransa a makaranta tunda shi baije ba.
Kuma yayi kokarin duk sunyi na zamani dana muhammadiya, kowa yayi FCE dake Zaria daga nan wasu suka kara wasu kuma suka soma aiki.
Su asalin ‘yan gidan sun kasance Mallawa ne wadda aka fi sani da mutanen Mali. Gaba daya yaran Ango da sauran Yan Gidan Gwaiba nada zanen biyu biyu a gefen fuskar su.
Mostly bak’ake ne, saidai kuma sunada kyansu daidai gwargwado. Masu hasken ciki shine Yaran Baffa Yusuf yanda duka Family ke kiransa dashi har mamanshi Gwaggo Dija.
Shidai Baffa Yusuf ya kasance mai zafin nema, bashida raina sana’a duk k’ank’antarsa, babu irin k’odagon da baiyi ba har Allah ya albarkace rayuwarsa da arziki mai dunbin yawa.
Bayan ya gama FCE zaria inda ya karanta Agriculture/Chemistry, yayi fafutuka neman aiki amma bai samu ba, shine ya soma noma domin ya taimake kansa, gashi lokacin shekarunsa 21. Ana nan ana nan sai gwamnati ta bada scholarship inda yaje Harvard University ya karance Agricultural Engineering kuma ya haɗa da Masters dinshi.
Toh tunda ya dawo ya fara samun saukin komai, Gashi mutumi ne mai fara’a da mutunci, saidai kuma bayason ragwanci at all. Baya san mutum mai wasa da aikin da aka bashi.
Dayake bashida ɗa namiji babba yasa yaransa mata guda biyu sune kan gaba a Gwaiba Investment. Shi bai damu da bambanci na mace ko na namiji ba, yara baiwa ne kuma duk wanda Allah ya baka idan ya albarkace maka su shikenan.
Nuwairah tana k’ark’ashin production watau inda ake sarrafa auduga ya koma kaya da sauran su. Ita kuma Nawwarah tana ɓangaren Sales watau inda ake siyarda kayan company ɗin.
Sauran Department ɗin company ɗin duk akwai yaran yanuwa a ciki kuma baya nuna masu bambanci, Wannan kenan!#YGG
#Dimples

YOU ARE READING
'Yan Gidan Gwaiba (Completed)
RandomYanka mata wani wawan mari tayi though ba yau suka saba gwabzawa ba, cikin masifa ta nuna mata ɗan yatsa "karki kuskura ki kara faɗin haka, any resemblance to you is what I hate most about myself" saita fashe da kuka.