Twenty-one

4.7K 274 4
                                        

Brooklyn, NY

    Babu wani abun kirki daya canza a tsakanin Hamza da Hunaisa sai kuma dai yanayin zamansu yafi nada.
    Tun wata ukun nan sau daya tayi kokarin guduwa, shima tana murɗa kofa ya soma ruri tareda danja.
    Sabon karatun da Hamza ya koya kenan, idan mutum zai fita ko shiga baka nan ya taɓa kofa ko Window a yanda bai dace ba sai ya sake garkewa fiye da nada.
    Kuma ya haɗa abin ta wayar hannunsa, yana hanyar komawa gida yagani. Kwafa yayi yana tunanin wannan wani irin mutum ne mai shegen naci.
    Cikin mintuna da basu wuce goma ba yakai gidan. Wasu nambobi ya danna sai karar ya daina sannan saiya shiga ciki.
   Ita kuma Hunaisa shiga tayi chan kuryan ɗaki tana kuka sosai, kenan ya tabbata bazata sake ganin wanda suke sata farin ciki ba.
    Hamza ta gani a kanta ya harɗe hannu a kan kirji. Ya tsaya yana kallonta na wajen minti goma sha biyar ba tareda yace mata k’ala ba.
    Ita kuma tana kuka k’asa k’asa tana jan majina. Zuwa yayi dab da ita ya zauna saiya riko mata hannu.
    “Zaki fita ba tareda izini naba, kin mance akwai aurena a kanki ne?” Yace mata, ita kuma saita ɗaga idonta ta kalle shi kana ta mayar kasa.
   “Ba gudu zanyi ba, kawai zani ganin gari ne
     “Dama ai bance guduwa zakiyi ba, cewa nayi zaki fita. Amma tunda kin kawo maganar gudu abinda kike so kiyi kenan koh?”
   “Ni banga amfanin zamana a nanba, bansan komai a kanka ba. Bansan sana’ar da kakeyi ba ko dalilin zaman mu a wannan garin, kuma wai ace mijina kenankuka yaci karfinta yasa ta daina magana
     “Yanzu idan kinason sanin wani abu gameda ni bazaki iya tambaya naba sai kice zaki gudu? Bakya tsoron mugaye su kamaki
    “Toh meye maraban dambe da faɗa
    Dariya wanda ya nuna dimples ɗinsa sai yace, “Toh aini sanki ya jawo min haka, kuma bakiji ance their is no boundaries in love and war”
      “Ni bansan wannan ba, a raba mutum da gidansu wai dan ana sanshi
     “Okay na ɗauki laifi, kiyi min hak’uri mu wuce wajen Please. Yanzu an riga an ɗaura mana sai muyi kokarin yafema juna laifunkan da mukayi
    Dagowa tayi tana dariyar mugunta, “Ka yafe min? Me nayi maka da zan bukaci gafarar ka?”
    “Watau bakisan me kika minba? Kullum ina zulumin fita saboda ina tsoron kada ki gudu
   “Ai
    “Yanzu dai nina yafe maki, kefa?”
   “Ba abu bane mai sauki, banaso na yaudareka. Amma zanyi kokarin tolerating ɗinka for now”
     Toh fah tun daga ranar sun fita sau biyu, ɗaya shopping ɗaya cinema. Batun aikinsa kuma yace mata yazo karatu ne kuma saura wata uku su koma gida Nijeriya.
    Bai faɗa mata batun sata da sukeyi ba saboda yana tsoron kada ya firgitata bayan ta fara sakin jiki dashi.
   Har yanzu kallon farkon datake masa na mugu yana nan a cikin idonta saidai kuma bai dameshi ba. Ya faɗa mata cewa iyayensa sun rasu kuma kashesu akayi.
   Bayan nan kuma akabi sister ɗinshi da mijinta da yaranta akayi ram dasu. Toh anan taji tausayin shi sosai, kuma ya faɗa mata babu wanda yakeso a faɗin duniya daya wuce ta
   Ita yanzu batasan yadda zatayi da soyayyar YaMudassir ba dayake zaune daram babu inda yaje, idan daidai tausayin Hamza ne babu tantama tanayi ainun.
   Amma kawai tausayin sane babu komai a tareda ita, saidai kuma tasan cewa wata sa’in tausayi yakan koma soyayya. Kuma dama ance their is a thin line between love and hate amma Koda wasa bata so k’in datake masa ya koma so.... Wannan kenan!
     
     GRA, Lugard Roundabout....
  
   Babu abinda ke shiga tsakanin Hajja Zee da Husna face girma da mutunta juna, kamar yadda Hajja Zee ta dauki alkawari na rike Husna kamar ɗiyar data haifa da cikinta.
     Itama Husna a matsayin uwa ta ɗauketa, dama batada raina mutum. Koda bata samu juna biyu ba a ‘yan watannin nan bai dameta ba saboda ba haihuwa ya kaita nan take ba da k’uruciyanta.
     Ta fiso gama more amarcinta kafin ta fara jigalan yara. Shikuma Alhaji TK yasha Iyayenta sunyi mata bayani na rashin yara yasa bai taɓa kawo mata zancen ba.
     Dama daga Babanta sai Baffa suka sani kuma sun zuge bakin su basu ce komai ba. Husna tana zaune akan kujerar falo tana kallon ‘No Greater Love’ a Dstv saiga Lubna ta shigo.
   Ihu suka somayi saboda rabon dataga Lubna tun bikinta, anan suka baje kolinsu saboda Hajja Zee ta tafi shago sai la’asar take dawowa.
     Mai aiki Husna ta kira domin ta kawo ma Lubie abinci, aiko anan aka kawo su kayan ciye ciye dasu fruits birjik harda grapes.
     Lubie taya kawarta murna tayi saboda tana damawa da naira saidai kuma wani hanzari ba gudu ba, kowa yasan cewa TK baya haihuwa.
    “Toh yanzu ya zakiyi da rashin haihuwar TK?”
    “Ban gane rashin haihuwa ba?”
   “Baki san baya haihuwa bane koko wani salan wulakanci zaki mun. Kowa dai yasani
    Ras gaban Husna ya faɗi, kwata kwata bata san baya haihuwa ba. Ita kawai tasha ko yaransa suna Kasar waje ne suna karatu ko makamcin haka. Anan idanta ya kawo ruwa saboda idan TK ya faɗi ya mutu daga kannensa sai iyayensa zasu gajeshi.  
     Ita kuma tayi kunnen doki da talauci bazata iya zama cikinsa ba.
     “Wallahi Lubie bansan baya haihuwa ba, shine aka boye min
   “Nima a gari naji, kuma nayi mamakin da baki faɗa min da bakinki ba”
   “toh ta ina zan faɗa maki bayan nima ban sani ba”
   “Yanzu dai kawai yadda zamuyi kiyi haihu dole, koma yaya ne saifa kin haifa koda kwara ɗaya ne
      “Lubie ta ina kike ganin haka zai faru? Jibi fah matarsa bata taɓa haihuwa ba saini
     “Karki damu da wannan, ki barmin wuka da nama. Inace ninace zaki haihu? Ki bari kiga aiki da cikawa. Halan bani na taimaka maki ba da TK bai gane abinda Ashafa yayi maki ba gashi yanzu kina zaune lafiya a ɗakin ki
     “Haka ne, kece. Toh yanzu me zamuyi?”
    “Zamuje asibiti ne a dubaku, zaki lallabesa akan ya yarda kuje. Ko artificial insemation ne ko surrogate... Nifa i don’t care sai munga TK da yaro
    “Anya zai yarda ya bini kuwa, na tabbata babu inda basuje da Hajja Zee ba”
    “Wannan kuma dab da ita, ita ta sani. Kisisina da shagwaba zaki rinka narka masa harya yarda dake. Haba sai kace ba mace ba, ai ba gatsal ake neman abu wajen miji ba. Sai kin nuna masa so da kauna tukun saiki kawo bukatar ki a hankali
      “Toh shikenan Lubna zan gwada... Nagode kawar arziki
     “Yauwa dama ai amfanin kawancen kenan, kuma dama akwai wani asibiti a chan Barnawa wanda private ne haka kuma mutane suna dacewa idan suka je
    Daga nan suka bar zancen suka koma batun Lubie a inda take faɗa ma Husna cewa Minister yace ta aureshi amma taki yarda.
    Ita tace masa bazata iya zama da kishiya ba, dama matansa guda biyu da yara tara. Yanzu haka ya sake matarsa na farko wanda keda manyan yara har shekara ashirin da takwas.
     Yace mata zai sake na biyu tsakanin gobe ko Jibi, ita dai tace kada ya sake kiranta saiya saketa.
      “Wow lubie kina sha’aninki! Kina wuta wallahi
   “Atoh yaushe zan iya wani zama da kishiya da kuruciya na, bari kiji Koke idan kinaso na tayaki fitar da Hajja tsab zan maki
    “Ah ah kyaleta, tanada kirki dan Allah”
     “Tsiyata dake kenan, rashin hankali. Kin taɓa ganin wanda ya aminta da kishiya. Ai babu kirki tsakanin ku”
    “Nidai ki kyale min ita, babu ruwanki da ita
     “Ke kika sani, nidai Kinsan nambar wayana idan kin canza ra’ayinki”
      Daga nan suka canza hirar, ita dai Husna tana tunanin yadda TK zai yadda ya bita asibiti kamar yadda Lubie ta bukata. Wannan abunda kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa..... Wannan kenan!

     Geneva Avenue, Gwaiba Manor....
      Shakuwa mara misaltuwa ne ya kullu tsakanin Deenie da Nawwarah, ta sake mashi sosai suna shan soyayya.
     Koda bai taɓa ganin zobe a hannunta ba sai jefi jefi yasan cewa ita batasan ana takura mata ne.
     in between kuma suna haɗuwa da Nuwairah, irin idan yazo gidansu kafin ya kira Nawwarah kuma tana kusa to da ita ake yi ranar. Abinda yasa baya kawo wani abu ransa baifi yasan cewa wanda ba ita bace budurwasa bazata zo kusa da shi ba balle tayi masa murmushi ko magana.
    A wajen treatment ɗinta kuma sauki yazo fiye da yadda ake tsammani, dama stress ke kawo mata abin kuma ta rage 75%. Ta kanyi dauke dauke amma baya wuce sau ɗaya a sati ba.
   Shima baya wuce daukan abinda bai taka kara ya karya ba. Ita karin kanta ta yaba da yanda take samun cigaba akan komai.
    Shikuma tunda Nawwarah tace ya rinka sakin jiki da Nuwairah yasa ko wajen therapy session dinsu yana dan hadawa da wasa da dariya.
   Dayake suna gamawa ake kiran sallah juma’a yasa bata damuwa akan rashin hirar da basayi da an gama. Ko ita bata san wasa da sallah kuma bata san wanda yake wasa dashi.
     A chan office kuma suna zuwa aiki, sun gama Internship ɗin kuma an turasu department ɗinsu.
   Ita Nuwairah tana karkashin production, ita kuma Nawwarah tana kasan Sales. Husna tun aurenta ta daina zuwa kuma Mermer ma haka tun lokacin.
    Yanzu Yan biyu basu cika haɗuwa ba kasancewar sunyi nesa da juna.
     Mobilization na bautar kasa ya fito kuma an turasu Black Gold na Kaduna, saidai basu tsaya a camp ba.
     Suna daga gida Momee tayi ɓarnar naira. Saidai aka kawo masu kayan registration sukayi daga gida.
     Mermer kam babu labari saboda ko su thumb print da uploading data ɗinta da akeyi da farko batayi ba balle a kyautata zaton za’ayi postn ɗinta.
      Komai ya tsaya mata cak, kawai dai addu’a za’a tayata dashi saboda tana cikin ukuba.
     Wajen 10am Baffa ya tara conference na gaggawa, Nawaz yana daga bakin kofa ya tsaya
   Taron Board members ne sai kuma Su Nawwarah saboda za’a fara nuna masu yadda ake abin kafin su kara shekaru.
    Koda yake suna ciki kasancewar sunada shares masu tsoka a kamfanin. Nawaz yana tsaye saiga Nawwarah tazo wucewa.
     Sanye take da multi colored abaya wanda pink yafi yawa. Saita yana kanta da pink gyale tareda saka dogon Hills ɗin Jimmy Choo. Sannan Bouquin ɗinta na kamfanin Maison Kitsune.
     Tana tafe gira a haɗe har tazo wucewa zata shiga ciki, ko kallon Nawaz batayi ba balle ta nuna tasan dashi. Shine yayi murmushi kana yayi mata magana.
   “Wucewa zakiyi ko gaisuwa babu, ba faɗa Meya kawo gaba”
     Harta wuce taku ɗaya ko biyu saita tsaya, cire tabaran idonta tayi saita juya ta kalleshi, “Akan me zanyi maka magana, baka san cewa ko gaisuwa tsakanin mutanen social class ɗaya akeyi ba, masu kudi yan uwansu suke gaidawa ba kaiba”
      “Ba abinda nake nufi ba kenan, Allah ya huce zuciyarki”
        “kuma ka kiyaye ni, kar kaga kuna shiri da Baffa zai baka damar ka kawo min raini. Niba tsaranka bane. Ko Mermer bata isheni kallo ba balle kai karamin alhaki. Kuma duk sanda ka sake min irin maganar nan saika bar aikin nan”
   Saita wuce tareda mayar da tabaranta, sororo ya tsaya miyau na bakinsa ya bushe kap. Yana tsaye Nuwairah tazo wucewa.
     Riga ta saka da skirt na latin America. Saita saka babban mayafi ta yana kanta, duk tana jin kanta babu daɗi yau.
   Sai samun faɗuwar gaba takeyi na rashin dalili, koda yake ance tana cikin wanda zasuyi presentation amma bai kamata yasata jin abinda take jiba.
     “Ina kwana?” tace ma Nawaz tazo wucewa.
     “Lafiya lau” ya amsa da fara’arsa
     12pm....

     Tana zaune a ofis ɗin Deenie tana jiransa sabida ance wai yau baima zo aiki ba, tana zaune ranta yayi mata baki na rashin dalili har yanzu.
    Tunani kala kala yake faɗo mata. Na farko ma wai ace batada number ɗin Deenie.
     Wai tanace number yana cikin abinda mutum yake samu, amma ita kullum saidai ya cika da surutu amma bai taɓa kiranta ba.
    Kuma yakance ya aiko mata da text msg amma bata taɓa ganin ko ɗaya ba. Gashi ita kawai ranar nan ta karɓa Tulips amma a duniya ta tsane flower ɗin.
     Kowa a gidansu yasan Nawwarah kesan abin, ita ka barta da Hydrangeas. Amma tunda Deenie ya bata tasan bai sani bane tunda basu taɓa maganar flowers dashi ba. Gaskiya yau zata sake tambayarsa meyasa yake son ta saboda amsar daya bata rannar kamar ba ita yakeso ba.
    Shikuma Deenie abinda yasa ya siya Yellow Tulips baifi yanda Nawwarah tace masa bayan pink color ba tana san Yellow musamman Tulips yasa ya siya domin ya burgeta.
   Nuwairah tana zaune wajen 12:30 pm saiga Deenie yazo. Kana ganinsa kamar yanzu ya tashi daga barci.
    Koda yake yanzun ma ya tashi saboda a Naf club ya kwana, Ya gurza rawa babu style dinda bai iya ba sannan kuma yayi ɓarnar naira domin kusan kowa na wajen ya siyan mashi kwalba ɗaya na Gulder.
    Shima ya tula ma cikinsa bila adadin, yau yayi wawan sha ne wanda rabonsa da yayi haka tun yana US, to sai wajen kiran sallah na farko yaje gida da kyar.
   A falo ya baje bai farka ba sai sha biyun rana, toh a gurguje yayi brush ya canza kaya saiya saka tabarau ya tafi ofis.
    Yana isa shine ya wuce cabinet ɗin magani wanda zai bama Nuwairah saiya koma ya cigaba da barci. Da tabarau baki na Calvin Klein a idonsa suka gaisa.
     Gashin kansa kacha kacha amma kuma ya karɓa fuskansa a matsayin sa na kyakyakya.
     “Meyasa kake sona?” yaji muryan Nuwairah. Abin yayi bala’in daure masa kai. Banda rashin hankali wayace mata daga yana mata fara’a na Doctor and patient shine Zata mayar da abin soyayya.
    Juyawa yayi bai cire tabaran sa ba, a dakilce ya soma magana, “wayace maki ina sanki”
     Mamaki ya kamata saboda ita bama amsar datake jira ya fito daga bakinsa bane, kada ma ya soma wasan nan da ita saboda yanzu zuciyar ta zai iya harbawa idan ta rasa shi.
     “Baby kabar wasan nan please, banso”
   Cire glass yayi mamaki karara a fuskarsa, “Gaskiya you are delusional, nine kike cema baby?”
    “Toh da wa zance ma baby idan bakai saurayina ba”
    “Okay please don’t be confused, Unless sunanki Nawwarah, kuma kinasan Pink and Yellow. Flowers ɗin Tulips ne favorites ɗinki. Kuma you’re mean but in a charming way, Kawai i suggest you wake up”
    Hawaye ne ya soma gangaro mata, tabbas sai yanzu 2+2 ya bata 4,tuntuni tana kokarin haɗa maths ɗin abinda yasa Deenie ke mata strange strange ta kasa ganewa.
   Tabbas ba ita yake soba face Nawwarah kamar yadda duniya suka fi santa akan ita, tabbas idan basu Baffa da Momee ba babu wanda zai iya kaunar ta, kuma tabbas ta yaudara kanta datayi tsammanin Deenie zaiso ta ya kyale Nawwarah
    Haba duk zuwan datake ganinsa gidansu wajen Nawwarah ne, duk msgs din dayake turawa da bata gani wajen Nawwarah yake aikawa.
    Nan ta durkusa kasa ta kama mashi kafa, “Dan Allah Deenie karka min haka, wallahi bazan iya rayuwa ba tareda kaiba”
    Mamaki Deenie yakeyi, lallai yarinyar nan batada hankali. Ciwon Satanta yana damun tunaninta. Kuma ai duk laifin Nawwarah ne datace ya rinka sake mata fuska gashi yanzu har raini ya shiga tsakanin su.
     Irinta dubu basu iseshi kallo ba. Dayake giyar bai gama sakinsa ba gashi tun fil azal ya tsani Nuwairah kuma dama bashida mutunci.
    Anan ya hambareta a ciki da kafarsa ya wuce, ita kuma kuka takeyi sosai saboda tashin hankali data shiga. “Banda rashin hankali kina tunanin zan aure arm robber ne kamarki yar kauye kawai kuchaka”
    Ya nufa hanyar kofa saiya tsaya ya saka tabaransa saboda kada a gane a buge yake. Zuwa yayi ofis ɗin Dr Amrah saboda daga yau bazai kara duba Nuwairah ba kafin ta gama raina shi.
    Dr Amrah zata rinka daukarta, daga nan ya fice ya shiga motarsa. Sauran sminoff din dake cikin motarsa ya fara kyankyanma.
    Itako Nuwairah tana kuka har zafin dake mata zugi a cikinta ya warware, da tasan yau abinda zai faru kenan da bata soma kawo zancen ba.
     Saidai kuma duka babu bambanci tunda yana ma magana da ita a rashin sani ne..... Wannan kenan!






#YGG





DIMPLΣS ce ✨

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Où les histoires vivent. Découvrez maintenant