Sharara gudu sukeyi sosai akan titi, basu tsaya ba sai Gyallesu inda Last Don yake zaune.
Har cikin garage suka parker, dama akwai kofa daga cikin garage ɗin zuwa cikin falo. Ta wannan hanya sukabi.
Koda yake Maigadin Last Don ɗan gari ne kamar su yasan komai kasancewar Last Don shine shugaban operations.
Hunaisa tayi dogon suma kuma bata farka ba, sufa a dadin su saboda zasu shiga da ita cikin gida babu sukur sukur.
Hamza da kansa ya dauketa tsam kamar jaririya, bai direta ba sai ɗakin bak’i na Last Don. Yanka tape ɗin hannunta yayi saiya daure mata hannu ɗaya da handcuffs akan karfen gadon.
Daga nan saiya fita falo wajen Last Don, isarsa keda wuya ya tarar ya fito daga bayi kenan kuma da alama yayi alwala.
Daga ma juna gira sukayi sai Last Don yace, “Weldone Man” saiya wuce, shi kuma Hamza ya murmusa.
Bayi shima ya wuce yayi alwala amma kafin ya dawo har Last ya tada sallah yana sujjud. Gefe ya wuce shima ya tada nasa sallah.
Magrib suka jero tareda isha, suna idarwa sai suka mike suka nufa ɗakin Hunaisa. Ko a lokacin bata tashi ba, Last Don ne ya zungureta da kafa sai ta tashi a firgice.
Nan ta soma dube dube domin ta tantance meke faruwa da ita, karab idanta ya hadu dana Hamza.
Nan take komai ya dawo mata, barkewa da kuka tayi kuma ga tsanar shi daya diran mata kamar sukan kibiya.
Karkarwa ta somayi jikin ya hau rawa, da karfi taja hannunta saita jishi a garke. Anan ta kalle hannun sannan kuma ta kalle su Hamza.
Sudai basu ce komai ba suna karanta yanayinta, sam Hamza baiji daɗin yanda haduwarsa da Hunaisa ta kasance ba.
Shi yafiso su hadu ta hanya daban yanda zasu fahimci junar su amma kuma bazai yiwu ba idan bata haka ba.
Haka ta cigaba da kuka tana masu magiya amma sukayi kunnen uwar shegu da ita. Daga baya ne Hamza yayi magana kasa kasa “Hunaisa kina jin yunwa?”
A razane ta kara tsorata saboda sunarta dataji ya fito daga bakinsa, watau ma sun santa kenan kafin yau?
“Dan Allah kuyi hakuri, ni bansan me na muku ba kuke so ku rabani da darajata. Idan kudi kukeso bari na kira Babana ya kawo maku. Dan Allah ku barni na tafi.... Balle kuma ga YaMudassir da kuka illanta, kada ku rabani dashi saboda shine farin cikina”
“Ke rufe mana baki” Last Don ya daka mata tsawa. Babu shiri ta saka ɗayan hannunta da ba’a kulle ba akan bakinta.
Hawaye ke malalo mata, gashi kuma wani sabon tsoronsu da take yi. Kawai tana zare ido tareda girgiza kanta alamun suyi hakuri kafin ta buɗe baki su ɗauke ta da bindiga itama.
Hamza ne ya kama hannun Last sukayi waje saboda bayason yadda firgici ke cikin idanunta. Ita kuma ajiyar zuciya tayi ta cigaba da addu’a cikin ranta.
Shikuma YaMudassir yana kwance jine jine da jini kamar yana shirin Swimming. Bai mutu ba amma yana cikin matsananci wahala.
Hannunsa yana wajen da aka bindige ya dafa, yana kwance yana nishi sama sama sai ga wasu mutane sun fito daga gidansu zasu sallah.
Da saurayine ɗan shekara sha biyar da kuma mahaifinsa. Da azama suka karasa wajen suna salati. Daga Baban har yaron tunda suke basu taɓa gamo da jini mai yawa irinna yau ba.
Tallabo YaMudassir Dattijon yayi saiya soma masa magana, “Samari waya maka wannan aika aikan?”
“Sun tafi da ita, shikenan sun raba mu” amsar da YaMudassir ya basu kenan, ga wasu hawaye daya keyi sannan maganar sa baya fita.
“Sun tafi da wa?” Saurayin ya amsa.
“sun tafi da ita” YaMudassir yace, duk ya birkice ya fita hayacinsa. Ga kuma zafin bullets dake masa radadi.
“Yaro ka natsu ka faɗa mana meya faru?”
“Hunaisa” yace daga nan sai idansa ya kame. Nan Dattijon ya gane Hunaisa yarinyar makwabcinsa ne kuma kawar Yarsa ce.
Ba saida aka faɗa ma saurayinba da kansa ya tashi ya tafi gidansu Hunaisa, a cikin gida ya tarar da Maigadi, “Kace ma Daddy an sace Hunaisa” daga nan saiya koma gidansu domin ya dauko mota.
Koda ya fito mutane sunyi charko charko a gaban YaMudassir ana jimami. Daddyn Hunaisa ne da Kannenta, Mommy daga baya ta fito taje saboda tana sallah taji hayaniya.
Isarta keda wuya taga halin da Mudassir ke ciki. Anan ta yanke jiki ta faɗi kasa. Lokacin yayi daidai da isar mota sai aka takartasu aka kai Teaching Hospital ɗin ABU.
Emergency ward aka wuce dashi direct, anan Daddyn Hunaisa ya nuna masu ID dinsa a matsayinshi na Major kuma YaMudassir ɗan wajensa ne.
Nan take aka soma mashi aiki tunda dama sai an nuna security clearance kafin ayi treating abinda ya jibance bindiga.
Mommy wani daki aka kaita aka soma kara mata ruwa da wasu magunguna, dama tanada hawan jini tun haihuwar Hunaisa.
Major Musa abin duniya sun masa cunkoso, ga ɓacewan Hunaisa, sannan kuma ga ciwon matarsa sai kuma yaron wansa Mudassir da rai ke hannun Allah.
Zama yayi a bakin reception shida makwabcinsa Alhaji Ibrahim suna jimami. Daga nan sai Daddy ya kira Unit ɗinsa akan maganar ɓacewan Hunaisa.
Yau babu barci sai an gano inda take, walau cikin zariya ko waninsa...
YOU ARE READING
'Yan Gidan Gwaiba (Completed)
RandomYanka mata wani wawan mari tayi though ba yau suka saba gwabzawa ba, cikin masifa ta nuna mata ɗan yatsa "karki kuskura ki kara faɗin haka, any resemblance to you is what I hate most about myself" saita fashe da kuka.