Asma'ul Husna taje gida tanata tauna maganar da Lubna ta gaya mata, abubuwa kala kala ke fado mata.
Wani zuciyar yace mata tabi shawarar wani kuma ya hanata, haka tayita yi saita yanke shawara akan gwara tabi yanzu kafin tayi dana sani nan gaba. Dama wanda baya bin shawara yafi cutuwa a duniya.
Lubna wants what's best for her yasa ta bata shawara akan haka, ita karin kanta tasan cewa Cancer of the pocket Watau talauci mugun ciwo ne. Kamar yadda wani mawaki yace, "Da yayi sati daya a talauci gwara amai duka da icce Kokuma yaje sudan a kasa"
Yanzu ta riga ta saba da zama cikin daula wanda bata fatan barinta, gwara ta lallaba tasan yanda zata dauwama akai. Anan tayima Lubie text, 'Na yarda ki haɗa mu ɗin'
Lokacin da Lubie taga sakon tana hanyar komawa Lagos saboda Minister yace taje su sasanta. Waya ta dauka ta kira 'Goje Scofield'
Kamar yadda akasan cewa Goje Sunar kaura ne haka shima wannan yake. Kullum saiya shanye kwallin sigari Uku sannan ya kuma haɗa da Wiwi. Baya shan barasa amma kama suna haɗuwa dasu Codeine irin kwalba ɗaya a rana kasancewar yanada tsada, saidai kuma idan Lubie tayi masa hadarin kudi.
Dan ta'adda ne na bugun jarida saboda duk inda wani dan daba yakai to yafi haka, baya rabuwa da karamin wuka a aljihu ko mashi saboda ɓacin rana, yanzu idan dambe ya haɗaku zai luma maka. Akwai wani lokaci da aka tsinta gawa a layinsu, babu wanda zai iya magana amma ana kyautata zaton shi ne ya kashe. Lubna ta sanshi saboda shine take Sawa ya zane mutum idan ya mata raini, za'a iya cewa Lubna Uwar gidansa ne.
Saidai kuma yana da kyan fuska sosai, ɗan Manbila Plateau ne bafilatani. Gashin kansa kamar yadda Lubie tace It's curly gashi da santsi ga baki, idansa ma abin kallo ne gashi dirarren namiji.
An haɗa AP zai sameta a Tafawa Balewa Guest Inn, itace taje ta kama ɗaki tana jiransa a room 7, Zuciyarta duka uku uku yakeyi kar akama ta, daɗin Abin TK yana chan NNPC dake kakuri yana kokarin yaji dalilin da mansa bai iso ba.
Yasa bai wani lura yadda taketa ɗari ɗari ba kafin ya bar gida, itama Hajja Zee an bata kwangila aiki ya kachame mata. Ita kam Husna babu irin addu'an da batayi ba harda na shiga bayi da saka sabon kaya don ruɗewa.
Murda kofa akayi ta mayar da hankalinta taga irin halittan da zai shigo, a cire shigar da yayi za'a iya cewa ya haɗu.
Amma shigar yan uwansa ya tasha tayi, riga ce gwanjon asali sai koɗarɗiyan jens wando wanda akwai bak'in mai na kanikawa akai. Sai kuma ya daga kafa daya zuwa kusan gwiwa, hannunsa kuma rike yakeda wiwi yana busa.
Duk xafin da mutanen annabi ke fama dashi bai hanashi saka head warmer ba. Baiyi sallama ba ya shiga, yana kallon Husna ya soma lashe baki tareda shafa gemunsa duk salon yan iska.
YOU ARE READING
'Yan Gidan Gwaiba (Completed)
RandomYanka mata wani wawan mari tayi though ba yau suka saba gwabzawa ba, cikin masifa ta nuna mata ɗan yatsa "karki kuskura ki kara faɗin haka, any resemblance to you is what I hate most about myself" saita fashe da kuka.