PAGE 1-5

1.9K 92 1
                                    

*BISMILLAHIR' RAHMANIR' RAHIM*

'''Zaune take akan wani hadde sofa kirar Italian, hannun ta reke da remote control, idon ta da hankalin ta suna kan wani hadedden plasma TV, wanda gabaki daya ta maida hankalin ta da nutsuwar ta gareshi, da dukkan alamu tana matikar jin dadin film din da take kallo wato''' *Gossip girls*...
Ahankali naga ta maida kallon ta ga tam fatsetsen gogon da ke daure a tsin-tsiyar hanun ta, wanda ko da ban tambaya ba nasan diamond ne a jiki,..  Kollon time tayi ta ja tsuka mtsww!!! "Lallai yau zan koya ma yar iskar yarinyar nan hankali, tun yaushe na aiketa, common hada milkshake ya gagareta,  about thirty minutes kenan da ai kenta amma haryanzu bata kawo ba, zanko ci ubanta yau" ta girgiza kai hade da cije lebenta wanda ya sha ado da red lipstick..
Rai a bace ta daga murya ta fara kiran sunan yar aikin nata "Zartaj! Zartaj!! Zartaj!!! Where the hell are u' u idiot ... ?"
Daga can cikin wani kofa najiyo wani siririyar murya mai da din sauraro tana fadin "Na'am Ma'am gani nan zuwa".. Niko ido na ware ina kurawa kofar da muryan yake fitowa domin inga wacce irin halitta ce mai dauke da wannan sanyaryar murya haka zata fito...
Ahankali ta budo kofar ta karaso ciki hanun da rike da trey da wani hadedden glass cup akai ta karaso inda madam din tata take ta duka ta aje trey din a kan wani dan table dake gefen ma'am din nata jikinta sai bari yake, cikin barin murya tace "dan Allah ma'am kiyi hakuri wlh na dan tsaya yin...." Kafin ta karasa maganan taji saukar mari a fuskarta tass kake ji, tai saurin dafe gurin tana fadin "dan Allah na tuba ba zan sake ba".. Kamin ta ankara ta farajin saukar duka ta ko ta ina ajikin ta,  inan take ta fara ihu tana bata hakuri, amma ita uwar gayyar ko ajikin ta sai jibgar ta take,  sanda taji ta gaji tunna ta kyaleta hade da daka mata sawa "GET LOST FROM MY SIGHT!!! wawuyar yarinya kawai gobe ki kara bata lokaci inna saki aiki,.." Tanemi guri ta zauna tana mai da nun fashi cike da bacin rai....
Itako zartaj mikewa tai da gudu ta nufi dakin ta tana shiga ta fada bathroom ta kulle kanta tasha kukanta sannan ta wasa ruwa tai alwala tafito...
mai tashafa ta canja kaya ta shimfid'a abin salla ta sa hijab ta tada sallah,.. Sai datai raka a shida intai biyu tai sallama,  intai biyu tai sallama, sannan ta zauna tana laxumi bayan ta idar tai yan addu'o'in da tasaba ta mike ta nufi main pallor din gidan ta soma aikin ta....

*WACECE ZARTAJ*
Yarinya ce yar kimanin shekara sha hudu a duniya,.. Tsayawa misalta kyan zartaj bata lokaci ne domin kuwa, yarinyar ta hadu ajin farko, inka ganta zaka iya dauka ba mutum bace tsabar kyau, baka ce amma ba har can ba zan iya kiranta da wankan tarwada, doguwa ce yar siririya amma ba harcen ba tana da suma mai tsawo wanda ya sauka har gadon bayan ta, uwa uba gata dailimin arabi da na boko,.. Zartay yar asalin garin Gombe ce anan kumo local government, sunan mahai finta Ahmad bello malami ne babba wanda aka san da zaman sa a cikin garin na kumo, malam ahmad na da matan aure uku matar sa ta fari itace hajiya kaltum, tana da yara biyu maza habu da manu, sai hajiya lantana, ita tanada yara uku mata biyu sai namiji daya ililu da safiya dakuma kuluwa, sai kuma hajiya aesha, tana da ya daya tilo zartaj,..  Kaf cikin matan malam yafi son aesha don kuwa tafikowa son shi da kuma soron Allah uwa uba kuma duk tafisu yarinta, hakan yasa malam yafi sonta da tausayin ta, bayan aesha ta auri malam ta sha matukar wahala agurin abokan zaman ta, sannan sanda tayi kusan shekara biyu ba hai huwa kullum cikin habai ci take, wai malam ya auro juye wacce bata hai huwa sai cika shadda da kashi,.. A shekara na ukun ne aesha ta samu haihuwa ta haifi yarta kyaukyawa mai matukar kama da ita, sabida tsananin kyaun yarinyar yasa matan gidan fadin ai ba mutun ta haifa ba aljana ce, inkuma ta musa suje su gwada ajiyeta abakin ruwa aga ko bazata bace ba, itadai aesha duk surutan da suke bata tan ka musuba,  wannan halin nata ne yakesa suke kara tsanarta a ransu, malam ko yai matukar farin ciki da haihuwar zartaj jiyake kamar akanta ya soma haihuwa, sonta da kautarta yashiga zuciyar sa sosai ako ina baya iya boyewa... Bayan shekara shida da haihuwar zartaj hajiya aesha tace ga garin mu, saka makon ciwom ciki data kwana tana yi, malam yayi matukar bakin ciki da rasuwar aesha sosai, bayan anyi arbain ne yatara matan nasa yace acikin su wace zata iya reke zartaj ta hada da nata yaran ta rike amana,..
Nan hajiya kaltum ta ce ita zata rike ta tunda dama yara biyu allah yabata kuma duka maza ne, takuma yi alkawarin riketa da amana, hakan yai matukar yima malam dadi nan yai ta sa mata albarka, itako harda kwallan muna furci,...

MATATA TA BIYUWhere stories live. Discover now