PAGE 25-30

625 49 0
                                    


Kwanciya tayi a kan gadon da yake tsakiyar d'akin, wanda yasha gyra,

Tunani take yau kusan watan ta shida da fara aiki a gidan nan, makaranta ma amsa ta na talakawa dai-dai ita, tana kuma jin dad'in kara tun nata sosai, dan tana matukar fahim ta,

Matsalar ta daya wulak'anci da dukan da take sha a gurin Maheen, sam ta tsaneta bata k'aunar ganin ta a gidan, ta kuma kasa gane dalilin da yasa ta d'auketa aiki agidan, ita da zata samu ta sallame ta ma takoma k'auye, da yafi mata, dan ba k'aramin kewar baban ta tayi ba..

Koya yake yanzu oho,  tasan yanzu haka duk hankalin sa da tunanin sa yana kanta, bai san wani irin hali take ciki ba, haka itama bata san wani hali yake ciki ba...

Kuka mai karfi ne ya kwace mata, sanda tayi mai isar ta sannan tai shiru, mahai fiyarta ce ta fad'o mata arai, cikin kuka tace "nayi kewar ki umma na" duk da Zartaj bata da wani wayo sosai mahaifiyar ta ta rasu, tana da shekara shida ne aduniya, amma akullum takan yi kukan rashin ta akusa, tana gani da umman ta na raye bazata shiga duk wani matsala da take ciki yan zuba..

Wani sabon kukan ta soma tanayi tana kiran sunan umma da babanta, har bacci 6arawo ya saceta...

** ** ** ** ** ** ** ** **
Maheen kuwa, Zartaj na fita, ta ja tsuka mtssw, ta wurgar da magazine din a kan gadon, ranta ne ke mata suya,

Tarasa dalilin dayasa, a duk sanda ta kalli Zartaj sai taji gabanta ya fad'i, bacin rai da tsanar yarin yar ya d'arsu a ran ta,

Gashi dai Zartaj yarin ya ce yar k'arama, ga hankali da nutsuwa, sanin kimar kai da girmama nagaba da ita, gatada uwa uba tsabta, kullun kaganta fes take abinta, bata da yawan surutu, bata da gulma, yadda ta kulama ko boysquoter ma bata zuwa kullum tana dakin ta ko ta tafi school ko tana aikin ta, sam yarinyar bata da matsala, amma tarasa dalilin dayasa ta tsaneta haka..

Tsaki ta kara ja, ta janyo wayarta k'irar iPhone 7 ta shiga dialing number _Honey_ din ta, ringing uku yayi ya d'aga...

Tace" _Hello Honey nah_"

Tacikin wayan naji yace "'''na'am''' *Matata ta d'aya*''' kin yini lafia?'''

Had'e fuska tayi ta bata rai ta turo baki, kamar yana ganin ta tace "Honey na fad'ama bani son sunan nan ko, ni Maheen ni kad'ai ce matar Aaryan, babu tabiyu balle ta uku, sabida haka ka dai na cemin *Matarka ta d'aya* inba dai so kake mu bata ba, ta kara turo baki gaba cike da shago6a...

Murmushi yayi yace "'''tow is okay uwar rigima,naji bazan k'ara fad'a ba shikenan koh'''

Murmushi ta saki wanda sai da yaji sautin sa, cikin muryan shago6a tace "shikenan amma kar ka k'ara kaji"

Yace "'''naji'''"

Tace " _you promise ?_"

Yace '''"yes i promise"'''

Tace " _that's my husband, I love you so much_"

Yace '''"love you more baby nah"'''

Tace "wai nikam Honey yaushe zaka dawo ne, _you have no idea how much I missed you_ kafad'a min when zaka dawo..."

Yace '''"I miss you too baby nah, nan da one month zan dawo inshaAllah"'''

Tace "haba _Honey one month is way too far_ ina makace _one week_ amma har _one month_ gaskia yayi nisa, yanzu fa kusan seven months fah ake nema da tafiyar ka, gaskia na fara gajia,.."

Yace '''"kar ki sake na gara jin kin ce kin fara gajiya, ni na hanaki ki bini, ba nace miki zamuna tafiya tare kika k'iba, wai ke bazaki iya zirga zirgan tafiya k'asashe da ban da ban ba, yazu kuma zaki zo kina min complain,  akan natafi na jima..."'''

MATATA TA BIYUWhere stories live. Discover now