PAGE 65-70

715 44 0
                                    

                 



*Bayan Shekara Hudu*
Haka dai rayuwar Zartaj taci gaba da gudana a cikin gidan captain Aaryan a matsayin ta na yar aiki...

Tacigaba da kula da duk wani al'amura na Maheen da Aaryan komai nasu ita ke yi, hatta girkin abincin Aaryan ya komo hanun ta

Ayanzu duk wani surar budurci sun gama baiyana a jikin Zartaj, ta zama cikekkiyar budur wa,  kyanta ya kara baiyana, gawani nutsuwa da ta kuma yi, sam yanzu bata da yawan magana, bata shiga harkan mutane sosai, sai dai duk da haka tana bawa duk wani na gaba da ita girman sa, kowa kuma a ma'aikatan gidan yana sonta yana kuma jin dadin zama da ita....

Tsakanin ta da Maheen kuwa tana matukar ko kari ganin ta kiyaye duk wani abu da zai ja mata zagi ko duka a wajen Maheen,...

Sannan a yanzu tasan yadda take tafiyar da zaman ta da ma'am din nata, bata taba yadda ta aikata wani kuskure da zai sa Maheen tayi yunkurin daura hanun ta a kanta...

Fannin karatun ta kuwa a yanzu tana ajin karshe ne na gama secondary wato SSS3, tana kuma matukar fahim tar karatun nata sosai, dan Zartaj a kwai hazak'a da basira, hakan yasa ta zama overall a cikin set din nasu, ilimin ta yasa tai suna sosai a cikin makarantar, hakan yasa dukkan malaman makarantar ke matukar so da ji da ita, sabi da tsabar ilimin ta yasa ko Quiz za ayi da school din su to ita suke dauka...

K'awar ta daya a school din Ameena Arabi wacce take kira da meena, kowa a school din yasan su tare, tun suna jss1 suke tare...

Ameena Arabi yarinya ce mai nutsuwa da hankali, gata da ilimi da son karatu, hakan yasa jinin su yazo daya da Zartaj suka soma k'awance, gidan su amina yana k'asa kadan da gidan Aaryan, hakan yasa suke yawan ziyartar junan su....

A 6an garen gidan su Zartaj kuwa, a cikin she karu hudun nan da tayi a gidan captain Aaryan ta je gida kusan sau shida...


**   **   **   **   **   **
A 6angaren Aaryan kuwa tun ranan da ya daura idon sa akan Zartaj ya kamu da matsa nacin sonta wanda shi bai ma san da hakan ba, duk da a duk san da yaji muryan ta ko ya ganta ko yaji an ambaci sunan ta sai ya tsinci kansa cikin faduwar gaba, wanda ya kasa gane dalilin hakan, sannan a duk san da yayi tafiya yakan yi kewar ganin ta yayi ta tunanin ta kenan wanda a nashi wautan wai sabo da yawan zirga zirgan da take akan sa ne yasa ya saba da present din ta, sannan da kuma tausayin ta da yake jine yake yawan sashi tunanin ta, dan shi kanshi yasan kalar tsanar da Maheen take yiwa Zartaj, wanda shi kansa abin na matukar basa haushi da kuma mamaki....

Yau kusan shekara daya da rabi rabon sa da kasar Nigeria, ya tafi wani course na shekara biyu a k'asar America, wanda in ya kammala ne ya dawo zai samu karin girma a wajen aikin nasa..

Asanda zaiyi tafiyar yayi yayi su tafi tare da Maheen amma firrr tak'i, wai ita batason wahala, haka ya kama hanya ya tafi ya barta, in tana da buk'atar sane takan wanke kafa tabishi can din nan ma intaje iyakar jima wanta one week ne ta juyo, ga uwa uba abin da yake kara d'aga mai hankali yau kusan shekara nawa da auren su amma Maheen taki yar da ta haihu, wai ita bata son ta tsufa tun bata gama more yarin tar ta ba, hakan yasa ta ke family planning, gudun kar ta samu ciki, Aaryan matsalar nan tana matu kar cimai tuwo a kwarya, gashi kuma a duk san da yaje wa da ameenin nasa Qaseem da zance amsa daya yake basa, wato "ka k'ara aure" shikuma har ga Allah bai da niyar aure nan kusa, a ganin sa dayan ma ya kasa controlling din ta ina kuma ga ya auro wata sun zama biyu, ina bazai iya ba, haka dai zai cigaba da haka da Maheen din, haka dai rayuwa ta ci gaba musu gashi yanzu saura 1month ya dawo gida....

**   **   **   **   **   **
Maheen kuwa tun da Aaryan yasa k'afa ya bar kasar take cin gashin kanta yadda ya kamata, kullum gidan cike yake da k'awayen ta, wad'an da suka shahara a bariki....

Tsanar da tayi wa Zartaj kuwa sai abinda ya k'aru, musamman yanzu data ga ta zama cikakkiyar budurwa ta kara kyau, hakan ba karamin tayar mata da hankali yake ba, dan sam bata kwaunar Aaryan yadawo ya daura idon sa akan wannan mai kama da Aljanun dan kyau, a duk sanda tayi yun kurin korarta sai ta tuna cewa ba lallai ta sake samun yarinya mai nutsuwa da hakuri irin na Zartaj ba, sai ta fasa...

haka dai rayuwa ya ci gaba da gudana a cikin gidan captain Aaryan.....

MATATA TA BIYUWhere stories live. Discover now