PAGE 45-50

620 43 0
                                    


Site din ta nufa, tura kofar falon tai ta sa kanta tashiga da sallama, k'anshi ne ya doki hancin ta, wanda yai matuk'ar bata mamaki..

6angaren da aka jima ba'a shiga bane yake tada wannan kanshi haka lallai, cigaba da tafiya tai taje ta kunna wuta, haske ya cika falon..

Tsayawa tayi cak sabida tsabar had'uwar falon, falo ne babba wanda ya tara abubuwan jin dad'in rayuwa, ba abinda zaka nema aciki ka rasa indai har abin ana ajiye shi a cikin falo, kaf gidan zan iya cewa ba site din da ya kai nasa haduwa da tsaruwa....

Ta shagala da kallon irin kayan alaton da aka watsa a cikin falon,  idonta ne ya kai kan wani had'ad'd'an designer prime wanda kyansa yayi matuk'ar daukar hankalin ta, a hankali ta karasa bakin prime din dan taga hoton waye a ciki, gabanta ne yayi wani mummunar faduwa, saka makon hoton Aaryan da tagani tam fatsetse aciki, fuskar sa dauke da murmushi...

Kirjin ta ne yaci gaba da bugawa wanda har sanda ta sa hanu ta dafe, kallon hoton ta cigaba dayi, atake taji zuciyar ta na son hoton, afili tace "Allah yayi kyau anan, mutum sai kace shi yayi kansa, lalai madam tayi sa'an kyakkawan miji, ashe dole ta rika kishin sa haka, anyi kyau kam anan, duk yadda nake gani madam ta hadu ashe ko k'afar mai gidan bata kamo ba, umm lalai fah.. 

Juyawa tayi ta soma aikin ta, bata jima ba ta kammala ta ko ina da ina ya rage saura bedroom din sa ne kawai....

Hanu tasa ta murd'a kofar dakin tashiga da sallama, dulum dakin yake da duhu, nan fa ta hau shafa bango tana neman inda makunnin wutan yake ta rasa, tafiya taci gaba dayi tana shafawa har sanda taji ta bugi wani k'aton abu a gaban ta...

Da sauri ta fad'i k'asa had'e da cewa "WASH ALLAH KAFANA!!!".. hanu tasa ta dafa gadon tana kok'arin tashi, sa hanunta ke da wuya sai gabaki d'aya jikin gadon ya fara haske...

Cike da mamaki ta k'arasa tsayawa tana kallon ikon Allah hanun ta biyu ta fara tafawa cike da dunbin mamaki...


Tafin farko da tayi kwai taga utan d'akin ya kama, idanu ta zaro waje cike da alajabi, sannan ta kuma tafawa domin ta tabbatar da zarginta tana tafawa kuwa wutan ya mutu, sannan ta sake tafawa ya kawo....

Tintsirewa tayi da dariya tace "lallai bature shegen mutum ne, wato har gadon na wuta, tafi shine makunnin wutan d'akin lallai, da ban yi tafi ba inaga sai dai na dauwama ina neman makunnin wutan...

Haka dai tai ta dariya sanda tayi mai isar ta sannan ta fara gyara d'akin, dakin shima ya matuk'ar haduwa sosai tsayawa fasalta tsaruwan dakin 6ata lokaci ne, bata jimaba ta kammala komai da komai ta koma site din Maheen...


WASHE GARI
Da sassafe Zartaj ta koma ta k'ara gyara side din Aaryan, sannan ta gyara na Maheen, bayan ta kammala komai ta nufi kitchen gurin su rose dan ta tayasu girki kamar yadda ta saba...

Bayan sun kammala ne ta kwashi kayan abincin ta kai side din Aaryan ta jerasu kan dinning table..

MATATA TA BIYUWhere stories live. Discover now