PAGE 20-25

687 48 0
                                    


*ASALIN AARYAN*
Aaryan asalin haifaffen garin kano ne, sunan mahai finsa Mr. Majid Sambo, babban maikacin government ne, sannan kuma dan kasuwa ne, Mr. Majid sambo ya nada tarun dukiya,

matar sa d'aya ta aure, sunan ta luwaisat, luwaisat macece mai hakuri, kawaici, taimako da tausayi, duk da yawan dukiyar da daulan da suke ciki, hakan bai sa ta mai da talaka mak'iyin ta ko abin kyama agare ta ba.

Wad'annan halayen na ta ne yasa mr. Majid yake matukar so da kyaunar ta, duk da ba auren so yayya suka yi ba.

Yayan su uku a duniya, mata biyu namiji daya, Aaryan shine babba sai kainat sannan kazeen.

Yaran sun taso cikin tarbiya mai kyau, so, kwauna da gata ba irin wan da basa gani, duk da irin gata da daulan da suke ciki, bai hana su samun tarbiya ta gari ba.

Kainat da kazin yara ne masu nitsuwa da hankali ba ruwan su da abin da bai sha fesu ba,   sannan kuma kyawawa ne angani a fad'a, dan kuwa kyau ga donta sukayi a wajen mahaifan nasu.

Aaryan saurayi ne dan shekara a shirin da tara, ya kammala karatun sa ne a k'asar Philippine, inda ya karan ci pilot, yafara aiki da su, cikin yan shekarun da basu fi biyu ba Allah ya bud'a masa ya sa Albarka acikin aikin nasa, kafin kuce me tuni ya zama shahararren matukin jirgi wanda ake ji dashi a k'asashe daban daban...

Wata rana Aaryan ya dawo daga U. S. A sun sauka a airport din malam aminu kano ya fito daga jirgi, ya ceri hulan uniform din pilot din dake kansa, ya sak'ale a tsakanin hanunsa, yana amsa waya da d'aya hanun, bai luraba sai ji yayi an bugi kafadar sa, a hankali ya tsaya, yajiyo domin yaga wanda ya buge shi haka, juyawan da zai kawai yayai arba da wata fara, had'add'iyar yarin ya, tajuyo rai a bace tace "FU*K UP..", sai kuma tai shiru saka makon haduwar da idanun su sykayi, nan take yaji son yarinyar ya shiga zuciyar sa ya zauna daram.

Nan dai ya gabatar mata da kansa itama ta fad'a masa sunan ta maheen, tun daga wannan rana soyayya mai k'arfi ya shiga takanin su har ya kai su ga aure, wanan shine kad'an daga tarihin captain aaryan...

*CIGABAN LABARI*

Bayan ta kammala gyaran falon ne ta shiga d'akin ma'am din, dan ta gyara mata,

Kwance ta sameta kan had'adden Italian bed nata wanda yaji bedshits da blanket masu kyau da laushi, ga filulluka nan baikatai a jere a kan gadon, d'akin sai k'anshi da sanyin a/c ne yake tashi, kwance take, tana duba wani magazine.

sallama zartaj tai tak'a rasa ta duk'a gaban gadon tace "sannu da hutawa ma'am"

A dakile ciki ciki, maheen ta amsa mata da "'''what are you doing in my room'''"

Zartaj tace "ma'am nazo gyra d'akin ne, naga yau sau d'aya na gyara, kuma kince sau biyu zan nayi a rana"

Wani kallon banza maheen ta watsawa zartaj, nan take zartaj ta sunkuyar da kai k'asa,

Cike da jin hausi da tsana maheen tace "'''okay''' so kike in tashi in fita in baki guri kiyi gyara ko, ke bazaki iya hakuri ba har sai na ta shi, dan rashin kunya koh, kwata kwata watan ki nawa ne a gidan nan, amma har kin falle koh, to ko zan koya miki hankali in bazaki nutsuba, tashi ki bani waje, '''idiot'''"

Jiki na rawa zartaj ta mike tana cewa "'''I'm sorry ma'am, my mistake''' ba zan kara ba"..

Tsawa maheen ta katsa mata tace "'''Get out of my room''', wawuyar yarinya kawai, mai kama da mutanen boye"

Dasauri zartaj ta fice, gudun kar a kara nada mata na jaki, ta nufi dakin ta....

MATATA TA BIYUWhere stories live. Discover now