PAGE 5-10

869 52 0
                                    

Tunda rikon zartaj ya koma hanun haj. Kaltum rayuwa ta sauya mata wahalan yau daban na gode da ban, wanki, shara, wanke-wanke debo ruwa kai da duk wani aikin wahala na haj kaltum ya koma kan zartaj, baki daya gidan ma ba mai tausayin marai cin ta, kowa yatashi musguna mata yake, ba inda take samun sauki da farin ciki sai gurin malam, shima malam halin da zartaj take ciki yana matukar da munsa, yai fada akan a daina sata aiyuka da takura ta a gidan amma sam kamar wanda yake kara wutar tsanar ta a zukatan yan gidan,  ganin haka yasa ya daina tanka musu, iyaka dai in yaganta tana kuka ya tambayeta sannan yai ta bata hakuri,....
Haka rayuwar zartaj yaci gaba da kasan cewa cikin kunci da rashin kwanciyar hankali har ta cika shekara goma da hai huwa, nan haj. Kaltum ta fara daura mata tallan shinkafa, tana kaiwa kasuwa, duk randa bata saida ba ko kudi ya 6ata to rannan bata da abincin dare, kuma sai ta nad'a mata duka,...
Duk da irin wahalar da zultaj take sha agidan bai hana ta maida hakali ga karatu ba, malam kuma yayi kokari gurin bata ilimin boko da na arabi, ganin yarinyar tana da basira yasa ya toshe kunnuwan sa, ya rufe ido ya ke biya mata kudin makaran ta, haka dai rayuwa taci gaba...
Wata rana haj. Kaltum na zaune sai ga k'awarta haj. Luba ta shigo nan suka zauna bakin rumfa suna gulmace-gulmacen da suka sabayi, zaltaj ne tai sallam ta karaso ta sauke robar tallan tata a mikawa kaltum kud'in,  tamike ta nufi d'akin innan ta wanda ayanzu ya zama nata tashirya ta tafi makaran tan allo, tana fita haj. Luba ta kalli haj. Kaltum tace waini kaltume menene amfanin wannan tallan da yarinyar nan take zuwa, kaltum cike da mamaki ta kalli luba tace kamar ya menene amfanin wannan tallan,  luba tai murmushi tace eh gani nayi ba wani riba sosai aciki, dama aikatau kika kai yarinyar nan da kinfi yadda kike dinnan wlh, gashi dama akwai wata hajiya da take neman yar yarinya wacce zata ke mata gyaran daki da kuma nafalo da dai yan sauran kananun aiyuka,  matar tana aure wani attajiri ne wlh tanada tarun masu aiki wayayyu wadan da suka san kan aikin su, to wai ita duk bata yadda dasu surinka siga dakin mijinta da nata suna gyarawa bane, wai matan yanzu basu da tabbas, gwara a dauko mata yar k'auye wacce bata san komai ba, ita konawa ne ake so zata rika biyanta a wata, tunda haj kaltum taji wannan batu hankalin ta ya tashi tace da malam ita nan duniya sai ta tura zartaj aikatau, da fari malam yaki amma daya tuna irin ukubar da yar autar tasa take ciki sai ya amin ce, nan ya sanar da zartaj dalilin sa na aminciwa yakuma yi mata fad'a akan ta kula ta tsare mutun cinta da nasa, tace to dukda har cikin ranta bata k'aunar rabuwa da mahaifin nata to amma ya ta iya da maraicin ta,..
Malam ya samu haj kaltum ya sanar da ita ya amince amma bisa sharadi guda in ta yarda, nan cike da farin ciki kaltum tace ta amince komenene ya fada za'ayi, malam yace ko ina aka kai auta a tabbatar an sanar da iyayen gidan nata su sata makaran ta......

MATATA TA BIYUWhere stories live. Discover now