PAGE 50-55

606 46 0
                                    

10:30am dai-dai jirgin su Aaryan yayi landing a airport din malam Aminu kano...


Sanya yake yau ma da uniform dinsu na pilot, hannayen sa sanye cikin Aljihun wandon sa, tafiya yake a nutse har ya k'arasa bakin wata doguwar mota kirar limozeen fara tas...

Wani matashin saurayi ne sanye cikin uniform din driver's irin na gidan Aaryan tsaye bakin k'ofar motan, hanun sa rike da murfin motan yana jiran uban gidan nasa ya shiga ya rufe k'ofar...

Ahan kali Aaryan ya sanya k'afa daya cikin motan sannan ya sunkuya a nitse ya shiga ya zauna, wannan matashin yai saurin kulle kofar yanufi gaban motar ya shiga ya tada suka nufi gida...

Suna isa bakin gate din gidan driver din yayi horn take get din ya bude kansa driver din yashiga sannan gate din ya rufe kansa...

Kaf ma'aikatan gidan maza da mata sun taru a bakin main kofar shiga cikin gidan, ciki harda Zartaj, dukkan su sanye suke cikin uniform din su sun yi layi, matan sun jeru a gefen dama mazan kuma a gefen hagu, matan da mazan duk suna fuskantar juna suna jiran k'ara sowar uban gidan nasu..

Driver nayin parking yai saurin fitowa ya bud'e wa Aaryan k'ofa,

Sanda yakusan ten seconds sannan ya fito yanufi hanyar shiga ciki, saura baifi taku biyar ba ya k'arasa inda ma'aikan suka yi layi suna jiran k'arasowar sa domin sumai barka da dawowa kamar yadda yake a cikin al'adar gidan...

Ji yayi kirjinsa ta bada sautin damm!!! Nan take ta fara harbawa da sairi da sauri, hanu yasa ya dafe ya soma karan to *innalillahi wa'inna'ilaihi raju'un* a cikin zuciyar sa, dak'er ya ke daga kafar sa har ya k'arasa inda suke...

Suna ganin sa a take suka rusuna kamar masu ruku'u suka ce _Welcome home sir_, sannan suka kuma mikewa tsaye suna kallon sa....


Hanu kawai ya daga musu yana murmushi wanda kana gani kasan iya lebe ya tsaya bai kai har zuciya ba, matsowa yake kirjin sa na k'ara tsanan ta bugawa har ya shiga ciki, duk iron tunanin yake amma yaka sa gane dalilin da yasa zuciyar sa ke harbawa amma ya kasa figuring, ahaka dai har ya k'arasa bakin side dinsa ya shiga falon da sallama ya nemi daya daga cikin kujerun falon ya zauna, har lokacin addu'a yake yi, ya kuma kasa gane dalilin faduwar gaban, duk da yana shigowa ciki ya dai naji amma Al'amarin yai matukar daure mai kai, yakai kusan 15second kafinnan ya nufi bedroom din sa....

*****************
A6angaren Zartaj kuwa itama tun sanda motar da yi parking ta fara jin bugun zuciya har ya shige ciki, bata cikin nutsuwa dan duk abin da tayi yi kawai tayi amma bata san me take yi ba, bayan ya shiga ciki suma suka watse, dakin ta ta nufa tana tafiya hankalin ta baya tare da ita, sai ji tayi ana jijjiga ta, tai firgigit ta dawo hankalin ta, hade da daga ido ta kalli mai girgi zatan...

sister rose ce tsaye idanuwan ta cike da mamaki tace "Zartaj _what are you thinking about, you seems so lost_, me yafaru ne"

Murmushi Zartaj tayi tace "bakomai sister rose wlh tunani kawai nake, amma ba komai fah, akwai abin da zan miki ne"

Rose tace "no bakomai dama dai zance yau aikin ki ya karu ne tunda sir ya dawo kuma bumusan ran komawar sa ba"

Zartaj tai murmushi tace "kar ki damu bakomai zan iya aikina ai"

Rose murmushi tayi tace " _OK go get some rest before_ ma'am ta kiraki"

Zartaj tace "to nagode" sannan ta nufi d'akin ta da yake cikin main parlor din gidan, tana shiga gado ta fad'a ta kwanta ta kara fad'awa duniyar tunani...














MATATA TA BIYUWhere stories live. Discover now